Malamin Musulunci Ya Fanɗarewa Sarkin Musulmi, Ya Fadi Ranar Sallar Idi a Najeriya
- Sheikh Muhammed Habibullah Adam Abdullah El-Ilory ya bayyana Litinin, 31 ga Maris, 2025, a matsayin ranar Eid-el-Fitr a Najeriya, bisa ga ka’idojin ilimi da addini
- Malamin ya ce ba za a iya ganin sabon jinjirin wata ba a ranar 29 ga Maris, 2025, don haka 31 ga Maris ita ce ranar farko ta Shawwal
- Sheikh El-Ilory ya jaddada cewa ilimin taurari na zamani na iya hango lokaci da matsayin wata, kamar yadda ake hasashen faduwar rana da duniyar rana
- Ya bukaci Musulmai su hada ilimi da koyarwar addini wajen tantance ranar Sallah, tare da mika fatan alheri ga jagororin Musulunci a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Agege, Lagos - Sheikh Muhammed Habibullah Adam Abdullah El-Ilory ya fadi ranar da za a sallar Idi a Najeriya.

Kara karanta wannan
Hafsan tsaro ya tsoma baki kan kisan ƴan Arewa a Edo, ya fadi shirinsu kan lamarin
Shehin malamin ya bayyana Litinin, 31 ga Maris, 2025, a matsayin ranar Eid-el-Fitr ga Musulmin Najeriya, bisa ka'idojin kimiyya da addini.

Asali: Twitter
Sallah: Malami ya saba da Sarkin Musulmi
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Nurudeen Ibrahim, ya wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh El-Ilory ya bayyana cewa kimiyyar taurari na zamani na iya tantance bayyanar sabon wata.
Malamin ya bayyana cewa:
"Da taimakon fasahar zamani, ana iya sanin lokaci da wuri na bayyanar wata, kamar yadda ake hasashen fitowar rana da duniyar rana."
Ya ce a ranar 29 ga Maris, 2025, shekarun sabon wata a Najeriya zai kasance awanni 6 da mintuna 59, wanda ba zai ba da damar ganin jinjirin da ido ba.
Haka nan, a Saudiyya, shekarun jinjirin zai kasance awanni 4 da mintuna 40, wanda hakan na nufin ba za a iya ganinsa da ido ba.
Ya kara da cewa:
"Samuwar hoton da manhajojin CCD ke samarwa ba ya cikin Sunnah na Manzon Allah (SAW), kamar yadda koyarwar addini ta bayyana."
"Litinin, 31 ga Maris, ita ce 1 ga Shawwal, kuma ranar Eid-el-Fitr bisa ga koyarwar Annabi da kimiyyar zamani."
"Allah ya kawo mana zaman lafiya da albarka a wannan bikin Eid-el-Fitr."

Asali: Twitter
Malami ya shawarci Musulmi kan haɗin kai
Sheikh El-Ilory ya bukaci Musulmai su hada ilimi da addini don gujewa rudani kan ranar Sallah a Najeriya.
Ya mika fatan alheri ga jagororin Musulunci a Najeriya, ciki har da Mai Martaba Sultan, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar.
Har ila yau, malamin ya yi addu'ar gudanar da bukukuwan sallah cikin aminci da walwala a Najeriya ba tare da tsaiko ba.
Sarkin Musulmi ya sanar da ganin wata
A baya, mun ba ku labarin cewa Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya fitar da sanarwa kan ganin watan Shawwal a Najeriya.

Kara karanta wannan
Rai baƙon duniya: Musulunci ya yi rashi bayan sanar da rasuwar malami a watan azumi
Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya bayyana an samu rahotannin ganin watan Shawwal 1446AH a sassa daban-daban na Najeriya.
Sultan ya bayyana cewa yau Lahadi, 30 ga watan Maris 2025, ita ce daidai da 1 ga watan Shawwal 1446AH.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng