Sanusi II Ya Fadi Matsayarsa kan Umarnin Hana Hawan Sallah a Kano
- Mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ys yi magana kan umarnin hana hawan Sallah da ƴan sanda suka bayar
- Sarkin ya nuna goyon bayansa kan umarnin soke hawan, inda ya nuna cewa rayuwar mutanen Kano ta fi komai muhimmanci
- Ya buƙaci jama'a da su kasance masu bin doka da oda tare da ba hukumomin tsaro cikakken haɗin kai domin samar da zaman lafiya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya goyi bayan haramta gudanar da bikin Hawan Sallah na wannan shekarar.
Muhammadu Sanusi II ya jaddada cewa wannan mataki yana da muhimmanci don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.

Asali: Twitter
Jaridar The Punch ta rahoto cewa Sarkin ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a wajen wata liyafar buɗa baki da aka shirya a fadarsa a ranar Asabar, 29 ga watan Maris 2024.

Kara karanta wannan
Hafsan tsaro ya tsoma baki kan kisan ƴan Arewa a Edo, ya fadi shirinsu kan lamarin
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanusi II ya goyi bayan hana Hawan Sallah
Muhammadu Sanusi ya bayyana cewa Hawan Sallah wanda tsohuwar al’ada ce da aka daɗe ana yi, ba ta kai muhimmancin tsaron al’ummar Kano ba.
Sarkin ya bayyana zaman lafiya a matsayin ginshiƙi na ci gaba da habɓakar kowace al’umma, kuma ya yarda da janye duk wasu shirye-shiryen da masarautar ta yi na gudanar da wannan shahararren bikin.
Kwamishinan ƴan sanda na Kano, Adamu Bakori, ƙarƙashin haɗin gwiwar hukumomin tsaro, ya sanar da haramta gudanar da Hawan Sallah da aka shirya, inda ya ce an samu rahoton sirri da ke nuna yiwuwar samun barazanar tsaro.
Sai dai mai martaba Sarkin ya tunatar da cewa bai ɗauki bikin Hawan Sallah a matsayin abun a mutu ko a yi rai ba, yana mai jaddada cewa rayuka da tsaron mutanen Kano sun fi masa muhimmanci.
Don haka, ya yi kira ga jama’a gaba ɗaya da su kasance masu bin doka da oda tare da ba da haɗin kai ga hukumomin tsaro don tabbatar da zaman lafiya kafin da bayan bukukuwan Sallah.
Gwamna Abba ya jinjinawa Sanusi II
A nasa ɓangaren, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda sakataren gwamnatin jihar, Ibrahim Faruq, ya wakilta, ya jinjinawa Sarkin bisa jajircewarsa wajen nuna soyayya da tausayi.
Ya bayyana cewa ya shaida halin kirki na Sarkin tun lokacin da yake malami a jami’ar Ahmadu Bello (ABU) a farkon shekarun 1980, inda ya jagorance su tare da ba su kulawa a matsayin ɗalibansa.
Sakataren gwamnatin jihar ya nuna godiyarsa ga Sarkin bisa kulawar da ya nuna kan rayukan al’ummar Kano, ta hanyar yarda da dakatar da Hawan Sallah na bana.
Sanusi II ya yi Allah wadai da kisan ƴan Arewa
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya nuna takaicinsa kan kisan gillar da aka yi wa ƴan Arewa a jihar Kano.
Sarkin ya yi Allah wadai kan yadda aka nuna tsantsar rashin imani wajen yi wa mutanen kisan kiyashi ta hanyar cinna musu wuta.
Asali: Legit.ng