Hafsan Tsaro Ya Tsoma Baki kan Kisan Ƴan Arewa a Edo, Ya Fadi Shirinsu kan Lamarin
- Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya yi Allah wadai da kisan gilla da aka yi wa wasu farauta yayin tafiya a jihar Edo
- Lamarin ya faru ne a ranar 28 ga Maris 2025, kuma ana ganin cewa da hukumomi sun samu labari da wuri, za a iya kaucewa wannan mummunan abu
- Janar Musa ya yi ta’aziyya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da iyalan wadanda suka rasa ransu, yana mai jaddada bukatar bin doka a harkokin tsaro
- Ya bukaci mafarauta da kungiyoyin sa-kai su yi rijista da hukumomi, domin hana yawaitar amfani da makamai ba bisa ka’ida ba, tare da neman goyon bayan al’umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Babban hafsan tsaron Najeriya (CDS), Janar Christopher Musa, ya yi martani kan kisan ƴan Arewa a jihar Edo.
Christopher Musa ya yi Allah wadai da kisan gilla da aka yi wa wasu farauta yayin da suke tafiya a jihar.

Asali: Facebook
Edo: Hafsan tsaro ya soki kisan ƴan Arewa
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar tsaron Najeriya ta wallafa a shafin X a yau Lahadi 30 ga watan Maris, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin da ya faru a ranar 28 ga Maris 2025, ana ganin cewa da an sanar da hukumomi da wuri, da sun tantance su kuma an kauce wa hakan.
Harin ya jawo maganganu musamman a Arewacin Najeriya inda aka bukaci daukar matakin gaggawa kan lamarin.
Janar Musa ya yi ta’aziyya ga Shugaban kasa kuma kwamandan rundunar sojin Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, da iyalan mutanen da suka rasa rayukansu.
CDS ya roki ‘yan Najeriya da kada su dauki doka a hannunsu, yana mai cewa:
"Yan sanda da sojoji na da horon da ya dace don magance irin haka.”

Kara karanta wannan
Bidiyon yadda aka yi jana'iza, aka birne ’yan Arewa 16 a Edo cikin hawaye da tausayi

Asali: Original
Christopher Musa ya shawarci mafarauta a Najeriya
Shugaban hafsan tsaro ya tabbatar da cewa rundunar sojin Najeriya za ta hada kai da ‘yan sanda da hukumomin tsaro don gurfanar da masu laifi.
Ya ja hankalin mafarauta da kungiyoyin sa-kai su yi rijista da ‘yan sanda, DSS, sojoji, da sauran hukumomin da ke da alhakin kula da mallakar makamai.
Ya kuma bukaci kungiyoyin tsaro na sa-kai su rika sanar da ‘yan sanda kafin daukar mataki, domin hana aikata kura-kurai da rashin fahimta.
A karshe, ya bukaci ‘yan kasa su ci gaba da bai wa sojoji da hukumomin tsaro hadin kai, domin su yi aikinsu na kare kasa cikin kwanciyar hankali.
Sanusi II ya magantu kan kisan ƴan Arewa
Kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi Allah wadai da kisan 'yan Arewa da aka yi a jihar Edo, yana mai kira ga hukuma ta bi musu kadunsu.

Kara karanta wannan
Jajen Peter Obi kan kisan ƴan Arewa ya bar baya da kura, an bukaci ya bar ɓoye-ɓoye
Basaraken ya nuna damuwa kan yadda aka yi wa mutanen Bunkure, Garko da Kibiya kisan gilla, yana mai cewa hakan rashin imani ne.
Sanusi II ya bukaci al'umma su guji jita-jita da daukar doka a hannunsu, su saurari hukuncin hukuma domin gudun ta da husuma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng