Rai Baƙon Duniya: Musulunci Ya Yi Rashi bayan Sanar da Rasuwar Malami a Watan Azumi
- Gwamna AbdulRazaq ya nuna alhinin rasuwar Muhammad Jamaalu Deen Yahyah Murtadoh Agodi, wanda ya rasu safiyar Asabar, 29 ga Maris, 2025
- Marigayi Sheikh Jamaalu Deen na cikin zuriyar Sheikh Yahyah Agodi, kuma ya shugabanci Markaz Taaleemil-arobiyyah wal Islamiyyah, Agodi
- Gwamnan Kwara ya aike da ta’aziyya ga iyalansa, dangin Markaz da daukacin al’ummar Musulmi na masarautar Ilorin kan wannan babban rashi
- An tunatar da mutane cewa rayuwa mai wucewa ce, kuma wajibi ne a dage wajen bautar Allah, yana mai addu’a ga marigayin domin samun rahama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ilorin, Kwara - Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya yi ta'aziyyar rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci.
Gwamnan ya nuna alhini kan rasuwar fitaccen malamin, Sheikh Muhammad Jamaalu Deen Yahyah Murtadoh Agodi.

Asali: Facebook
An cafke malami kan zargin kisan daliba
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin Gwamnatin jihar Kwara ya wallafa a manhajar Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan cafke wani malamin Musulunci a Kwara kan zargin hadin baki da kisan wata dalibar Kwalejin ilimi.
Bayan zargin da ake yi masa, kotun majistire ta umarci a tsare Abdulrahmam Mohammed, wanda ya kira kansa da malamin addinin Musulunci a gidan gyaran hali.
Ana zarginsa tare da wasu mutum huɗu da haɗa baki wajen kashe ɗalibar ajin karshe a kwalejin ilimi ta jihar Kwara mai suna, Hafsah Lawal.
Alkalin kotun ya umarci a garƙame waɗanda ake ƙara bayan sun amsa laifinsu kana ya ɗage ƙarar zuwa ranar 6 ga watan Maris, 2025.

Asali: Twitter
Fitaccen malamin Musulunci ya kwanta dama
Sanarwar da sakataren yada labaran gwamna, Rafiu Ajakaye ya sanyawa hannu ya ce malamin ya rasu a safiyar Asabar, 29 ga Maris, 2025.
Marigayi Sheikh Jamaalu Deen, wanda ya kware a wa’azi da tarihin addini, yana cikin zuriyar babban malami Sheikh Yahyah Agodi.
Malamin ya shugabanci makarantar Markaz Taaleemil-arobiyyah wal Islamiyyah da ke Agodi a birnin Ilorin.
Gwamna AbdulRazaq ya aike da ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, iyalan Markaz, da daukacin al’ummar Musulmi na masarautar Ilorin bisa wannan babban rashi.
Sanarwar ta ce:
"Rasuwar wannan fitaccen malami, kwanaki kadan bayan ya jagoranci sallar tahajjud da aka gudanar a cikin wannan wata mai albarka ta Ramadan abin takaici ne.
“Mun roki Allah ya gafarta wa Sheikh Muhammad Jamaalu Deen Agodi, ya haskaka kabarinsa, ya yalwata masa, kuma ya sanya shi cikin Aljannah Firdausi.”
Shugaban majalisar malamai ya rasu a Yobe
Mun ba ku labarin cewa rahotanni sun tabbatar da rasuwar shugaban Majalisar Malamai na ƙungiyar JIBWIS watau Izala reshen jihar Yobe, Imam Muhammad Khuludu Geidam.
Kungiyar Izala ta bayyana cewa malamin ya riga mu gidan gaskiya a ranar Laraba, 26 ga watan Ramadan, 1446AH daidai da 26 ga watan Maris din shekarar 2025 da muke ciki.
An ce malamin ya ba da gudummuwa sosai ga al'umma ta fuskar wa'azi da ilimantar da jama'a hanyar rayuwa mai inganci bisa koyarwar addinin Musulunci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng