Bayan Soke Hawa, Sanusi II Ya Gana da Malaman Musulunci da Kusoshin Gwamnati

Bayan Soke Hawa, Sanusi II Ya Gana da Malaman Musulunci da Kusoshin Gwamnati

  • Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi buda baki tare da sarakuna, manyan malamai, da jami’an gwamnati
  • Wata sanarwa daga shafin Sanusi II Dynasty a Facebook ta tabbatar da cewa an gudanar da walimar buda bakin a yammacin Juma’a
  • Bayanai sun nuna walimar ta gudana ne a ranar 28 ga watan Ramadan 1446, inda aka hallara domin yin addu’o’i da sada zumunci
  • Manyan malamai, sarakuna da kusoshin gwamnati sun tattauna batutuwa masu muhimmanci da suka shafi ci gaban al’umma a Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi buda baki da manyan malaman Musulunci a jihar a daren ranar Juma'a.

Mai Martaba Sanusi II, CON, ya jagoranci walimar bude baki tare da sarakuna, malamai, da kusoshin gwamnati a Kano.

Kara karanta wannan

Kungiyar Izalah ta yi maganar kisan ƴan Arewa a Edo, ta fadi hanyar dakile lamarin

Sanusi II ya yi zama da manyan malamai da jiga-jigan gwamnatin Kano
Sarki Sanusi II ya yi buda baki da kusoshin gwamnatin Kano da manyan malaman Musulunci. Hoto: Sanusi II Dynasty.
Asali: Facebook

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin Sanusi II Dynasty ya wallafa a manhajar Facebook a yau Asabar 29 ga watan Maris, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun hana hawan sallah a Kano

Wannan na zuwa ne awanni kadan bayan rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta sanar da haramta duk wani hawan Sallah a bukukuwan sallah karama, domin tabbatar da doka da oda.

Kwamishinan 'yan sanda na Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa an dauki wannan mataki ne saboda karuwar rashin jituwa a jihar.

Ibrahim Bakori ya gargadi Musulmi da su bi dokokin tsaro, ciki har da guje wa tukin ganganci da hawan doki, tare da kiyaye dokar da aka gindaya.

Yan sanda sun hana hawan sallah a Kano
Bayan yan sanda sun janye hawan sallah a Kano, Sanusi II ya yi buda baki da manyan malaman Musulunci. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa.
Asali: Twitter

Sanusi II ya gana da malaman Musulunci

Walimar ta gudana ne a yammacin Juma’a, 28 ga watan Maris, 2025 wanda ya yi daidai da 28 ga Ramadan 1446 bayan hijira, aka hallara domin yin addu’o’i da sada zumunci

Kara karanta wannan

"Mun hango babbar barazana," Yan sanda sun hana hawan Sallah a Kano

Manyan malamai daga bangarori daban-daban sun halarci taron da aka gudanar tare da sarakunan gargajiya da ke da daraja ta biyu a masarautar Kano.

Haka kuma, jami’an gwamnatin Kano sun samu halarta, sun tattauna batutuwa masu muhimmanci da suka shafi ci gaban al’umma da kuma zaman lafiya.

Sanarwar ta kara da cewa:

“Sarkin Kano, Khalifa Dr. Muhammad Sanusi II, CON, ya jagoranci walimar bude baki tare da sarakuna masu daraja ta biyu, malamai daga kowanne bangare, da kusoshin gwamnatin Kano a yammacin Juma’a.
“An gudanar da walimar ne a ranar Juma’a, 28 ga watan Ramadan, 1446 bayan hijira."

Hawan sallah: Sheikh Khalil ya yabawa Aminu Ado

Kun ji cewa bayan Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya janye hawan sallah, Sheikh Ibrahim Khalil ya yaba wa basaraken kan matakin da ya dauka saboda maslahar tsaro.

Malamin ya ce janye shirin hawan Sallah da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya yi yana nuna cewa zaman lafiya ya fi komai muhimmanci.

Sheikh Ibrahim Khalil ya ce matakin Sarkin ya dace da maslahar tsaro kuma ya nuna cancantarsa a shugabanci saboda muhimmancin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng