Matatar Ɗangote Ta Kara Farashin Litar Man Fetur ana Shirin Karamar Sallah? An Samu Bayani

Matatar Ɗangote Ta Kara Farashin Litar Man Fetur ana Shirin Karamar Sallah? An Samu Bayani

  • Kungiyar ƴan kasuwar mai watau PETROAN ta ce har yanzu matatar Ɗangote ba ta fara sayar da kayanta da Dalar Amurka ba
  • Shugaban ƙungiyar, Billy Gillis-Harry ya kuma tabbatar da cewa kamfanin Ɗangote bai ƙara farashin fetur ga ƴan kasuwa ba
  • Ya ce kuɗin da ake saye da sayarwa da kudin sufuri na cikin abubuwan da suke taka rawa wajen tashi ko saukar farashin man fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Kungiyar masu gidajen sayar da fetur a Najeriya (PETROAN) ta bayyana cewa har yanzu ba a fara cinikin mai da Dalar Amurka a matatar Dangote ba.

Haka nan kuma ƙungiyar ƴan kasuwar ta kuma tabbatar da cewa Ɗangote bai kara farashin litar man fetur ba.

Aliko Ɗangote.
Dangote bai fara sayar da man fetur da Dala ba Hoto: Aliko Dangote
Asali: Getty Images

Shugaban PETROAN, Billy Gillis-Harry, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da gidan talabijin na Arise a ranar Laraba, 26 ga watan Maris. 2025.

Kara karanta wannan

Ana shirin sallah: An kara kudin litar man fetur a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗangote ya koma sayar da mai da Dala?

Ya bayyana cewa duk da sanarwar da matatar Dangote ta fitar cewa za ta daina sayar da mai a Naira, har yanzu ‘yan kasuwar mai na ci gaba da karbar kaya a kudin Najeriya.

Gillis-Harry ya ce PETROAN ba ta samu wata sanarwa daga Dangote ba cewa an canza tsarin sayar da mai zuwa Daloli.

“Har zuwa jiya, ‘yan kungiyarmu da suka sayi man fetur, sun biya da Naira. Ban ga alamun cewa Dangote na son jefa kasuwa cikin rudani ba, amma ya na kokarin tabbatar da daidaiton kasuwanci,” in ji shi.

Ɗangote na shirin canza kuɗin cinikin fetur

A ranar 19 ga watan Maris, matatar Dangote ta sanar da dakatar da sayar da man fetur a Naira saboda tana sayen danyen mai a da Daloli.

Wannan mataki ne ya sa aka fara tsammanin cewa farashin feturin Ɗangote zai kara tashi a Najeriya, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

"Ba yau aka fara ba," Gwamnatin Kano ta yi zazzafan martani kan kisan ƴan Arewa a Edo

Sai dai har yanzu ana ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarori daban-daban don cimma matsaya kan kasuwancin ɗanyen mai da Naira.

Gillis-Harry ya ce PETROAN na goyon bayan sayar da danyen mai na Najeriya a Naira, yana mai cewa idan za a sauya wannan tsari, ya kamata a tattauna da duk masu ruwa da tsaki.

“Ya kamata a kira taron tattaunawa da bangarori masu alaka da fannin fetur kafin a yanke hukunci,” in ji shi.

Dalilin da ke sa a ƙara farashin fetur

Dangane da hauhawar farashin man fetur, Gillis-Harry ya bayyana cewa farashin mai yana canzawa, ya tashi ko ya sauka, bisa la’akari da abubuwa daban-daban.

Ya ambaci kudin cinikayya, kudin sufuri da sauran kudade masu nasaba da shigo da man fetur a matsayin manyan abubuwan da ke kawo tashi ko saukar farashi.

A karshe, ƙungiyar PETROAN ta bukaci ‘yan Najeriya da su guji yin turereniya wajen siyan mai, domin babu wata alamar karancin man fetur a halin yanzu.

Kara karanta wannan

An fara bugawa kan kudirin hana Tinubu, Atiku da Obi takara a 2027

Matatar Ɗangote ta ɗauki asarar N16bn

A wani rahoton, kun ji cewa matatar Ɗangote ta amince zs ta ɗauki asarar Naira biliyan 16 domin saukakawa ƴan Najeriya.

Matatar ta ce za ta mayarwa da ƴan kasuwa waɗannan kuɗi bayan ta rage farashin kowace litar man fetur a ƙasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel