Kungiyar Izalah Ta Yi Maganar Kisan Ƴan Arewa a Edo, Ta Fadi Hanyar Dakile Lamarin

Kungiyar Izalah Ta Yi Maganar Kisan Ƴan Arewa a Edo, Ta Fadi Hanyar Dakile Lamarin

  • Kungiyar Izalah a Najeriya ta nuna bakin cikinta kan kisan matafiya a Edo, ta na mai kira ga hukumomi da a binciki lamarin tare da hukunta masu laifi
  • Lamarin ya faru ne a garin Uromi, inda wasu bata gari suka kashe matafiya ‘yan Arewacin Najeriya da ke kan hanyarsu ta komawa gida don sallah
  • Sannan kungiyar ta yi Allah wadai da wannan aika-aika,ta ce dole hukumomi su dauki matakin gaggawa don hana faruwar irin wannan a nan gaba
  • JIBWIS ta reshen Kaduna ta jajanta wa iyalan mamatan, ta ke cewa barin irin wannan abu ba tare da hukunci ba zai kara tabarbarewar tsaro a kasar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Uromi, Edo - Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta yi magana kan kisan ƴan Arewa a Edo.

Kara karanta wannan

Barau ya yi martani kan kisan 'yan Arewa a Edo, ya fadi hanyar da zai samo musu adalci

Kungiyar ta yi Allah wadai da kisan da aka yi wa wasu matafiya ‘yan Arewa a jihar da ke yankin Kudu maso Kudancin Najeriya.

Kungiyar Izalah ta yi Allah wadai da abin da ya faru a Edo
Kungiyar Izalah ta bukaci hukumomi su dauki mataki kan kisan Hausawa a Edo. Hoto: Abdullahi Bala Lau.
Asali: Facebook

Yadda aka hallaka Hausawa a Edo

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya wallafa a shafin Facebook a yau Asabar 29 ga watan Maris, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya faru ne a garin Uromi da ke karamar hukumar Esan ta Arewa Maso Gabashin jihar Edo a ranar Alhamis 27 ga watan Maris, 2025.

Matafiyan sun taso daga birnin Port Harcourt ta jihar Rivers suna kan hanyarsu ta komawa gida don bikin sallah, amma wasu bata gari suka tare su suka hallaka su.

Abin ya jawo maganganu a yankin musamman a Arewa inda ƴan siyasa, kungiyoyi da malaman addini da kuma manyan lauyoyi suka yi Allah wadai da harin.

Rahotanni sun ce daga cikin mafarautan akwai wadanda suka tsira da rayukansu inda suka bayyanawa ƴan jaridu halin da suka tsinci kansu yayin harin.

Kara karanta wannan

An fara kama mutanen da suka kashe 'yan Arewa a Edo

Gwamnatin Edo ta yi Allah wadai da kisan Hausawa a jihar
Gwamna Monday Okpebholo ya bukaci zakulo wadanda suka hallaka Hausawa a jihar. Hoto: HE Sen. Monday Okpebholo.
Asali: Twitter

Kungiyar Izalah ta yi Allah wadai da kisan Hausawa

Kungiyar Izalah ta bukaci hukumomi su gudanar da bincike mai zurfi tare da hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aika.

A cikin sanarwar da ta fitar, JIBWIS ta bayyana cewa:

"Wannan mummunan al’amari na nuna jahilci da rashin sanin ciwon kai ne.
"Muna kira ga hukumomi su dauki matakin gaggawa don hukunta masu laifi."

Kungiyar ta kuma jajanta wa iyalan mamatan tare da yi musu addu'ar samun rahama a gobe kiyama.

Sanarwar ta kara da cewa:

"Barin irin wannan al’amari ba tare da daukar tsattsauran mataki ba na iya haifar da matsalar tsaro, inda ‘yan kasa ba za su ji kwanciyar hankali ba."

Gwamnonin Arewa sun fusata kan kisan Hausawa

A wani labarin, Gwamnonin yankin Arewacin Najeriya sun yi Allah-wadai da kisan matafiya a Edo, suna cewa wannan abin takaici ne da ya sabawa hakkin dan Adam.

Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya ce dole ne a binciki lamarin tare da hukunta masu laifi, domin hana irin haka faruwa a gaba.

Gwamnan ya jaddada cewa kowane dan Najeriya na da ‘yancin tafiya ba tare da fargabar farmaki, barazana ko muzgunawa ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng