"Za a ga Wata Yau?": Fadar Sarkin Musulmi Ta Fitar da Sanarwa ana Shirin Fara Duban Watan Sallah

"Za a ga Wata Yau?": Fadar Sarkin Musulmi Ta Fitar da Sanarwa ana Shirin Fara Duban Watan Sallah

  • Kwamitin ganin wata na fadar sarkin musulmi ya tunatar da batun fara duban jinjirin watan Shawwal yau Asabar, 29 ga watan Ramadan, 1446H
  • Kwamitin ya bukaci duk wanda Allah ya sa ya ga watan ya tura sakon sunansa, wuri da lokaci zuwa lambobin nan: 08020878075, 09096369117
  • Amma dai masana ilimin taurari sun bayyana cewa zai wahala a iya ganin jinjirin watan Shawwal a yau Asabar, 29 ga watan Maris, 2025

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Fadar Mai martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar II ta sake tunatar da jama'a batun fita duban jinjirin watan Shawwal, 1446 watau watan ƙaramar sallah.

Fadar Sultan ta hannun kwamitin ganin wata ta buƙaci musulmi su tura rahoton ganin wata, wuri da sunayensu ga wasu lambobin waya da aka fitar.

Sarkin musulmi.
Fadar sarkin musulmi ta fitar da tsarin kai rahoton ganin watan Shawwal Hoto: Daular Usmaniyya
Asali: Getty Images

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da kwamitin duban watan ya wallafa a shafinsa na Facebook da safiyar yau Asabar, 29 ga watan Ranadan, 1446H.

Kara karanta wannan

Bayan soke hawa, Sanusi II ya gana da malaman Musulunci da kusoshin gwamnati

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fadar Sarkin musulmi ta yi tunatarwa

Kwamitin ganin wata ya bayyana cewa yau Asabar, 29 ga watan Ramadan 1446H, wanda ya yi daidai da 29 ga watan Maris 2025, ita ce ranar da za a fara duban jinjirin watan Shawwal.

Sanarwar ta bukaci al’ummar Musulmi su fito domin neman watan Shawwal, wanda zai tabbatar da karshen azumin watan Ramadan na bana.

Haka nan kuma, an shawarci mutane su yi kokarin fita cikin rukuni don neman watan, domin tabbatar da sahihancin ganin jinjirin watan fiye da mutum guda.

A jiya Juma'a, 28 ga watan Ramadan, Sarkin Musulmi ya umarci jama'a su fara duban watan Sallah bayan faɗuwar ranar yau Asabar.

Za a ga wata ranar Asabar a Najeriya?

Wannan na zuwa ne bayan ɗaya daga cikin ƴan kwamitin ganin wata kuma masanin ilimin taurari, Simwal Usman Jibril ya yi hasashen cewa azumi 30 za a yi.

Kara karanta wannan

Sallah: Sarkin Musulmi ya bukaci a fara duba watan Shawwal a Najeriya

Malam Simwal ya bayyana cewa a ilimin falaki, ido ba zai iya ganin jinjirin watan Shawwal ba a ranar Asabar, 29 ga watan Ramadan amma ya ce komai na iya faruwa saboda abin na Allah ne.

A sanarwar tunatarwa da ya fitar yau Asabar, kwamitin ya kuma bukaci duk wanda ya ga jinjirin wata ko bai gani ba, da ya tabbatar da aika rahoton ga lambobin da aka bayar.

Watan musulunci.
Fadar sarkin musulmi ta ba da lambobin da za a tura rahoton ganin wata Hoto: Inside The Haramain
Asali: Facebook

Taya za a tura saƙon ganin wata ga Sultan?

"A cikin rahoton da za a turo, dole ne a bayyana cikakken suna, wurin da kuma lokacin da aka ga watan," in ji sanarwar.

A karshe, kwamitin ya yi addu’a da fatan Allah Ya amshi ibadun da aka yi a cikin watan Ramadan tare da ba wa kowa ikon ci gaba da aikata ayyukan alheri.

Ga lambobin da za a iya aika rahoto idan an ga watan:

📞 08020878075

📞 09096369117

Kara karanta wannan

Fadar Sarkin Musulmi ta faɗi dalilin da ya sa take amfani da ganin watan Saudiyya a Najeriya

Kura-kuran da ake yi ranar ƙaramar sallah

A wani labarin, mun kawo maku jerin wasu kura-kurai da musulmi ke yi a ranar ƙaramar sallah da hanyoyin da za a bi wajen kauce masu.

Ana sa ran za a yi idin ƙaramar sallah ne ranar Lahadi, 30 ga watan Maris, ko kuma ranar Litunin, 31 ga watan Maris, 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng