Abin ba Dadi: 'Yan Shi'a Sun Gwabza da Jami'an Tsaro, an Samu Asarar Rayuka
- Al'amura sun rincaɓe a babban birnin tarayya Abuja bayan 'yan ƙungiyar Shi'a sun fafata da jami'an tsaro a ranar Juma'a
- Ƙungiyar ta bayyana cewa jami'an sojoji sun hallaka mambobinta guda biyar bayan sun fito don tunawa da ranar Quds ta duniya
- Rundunar ƴan sandan birnin Abuja ta cafke mutum 19 da ake zargin suna da hannu a arangamar da ta auku tsakanin bangarorin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - An samu asarar rayuka bayan jami'an tsaro sun gwabza da mambobin ƙungiyar Shi'a a birnin tarayya Abuja.
Ƙungiyar Shi'a ta yi iƙirarin cewa an kashe mambobinta guda biyar yayin wata arangama da jami’an sojojin Najeriya a ranar Juma’a.

Asali: Twitter
Ƴan Shi'a sun zargi jami'an tsaro da farmakarsu
Jaridar The Punch ta rahoto cewa ƴan Shi’a da sojoji sun yi arangama ne yayin wani jerin gwanon tunawa da ranar Quds ta Duniya a Abuja.

Kara karanta wannan
An hallaka Kachalla Dan Isuhu da ya sa haraji a kauyuka 21 ya kashe Farfesa Yusuf
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar ƴan Shi’a, lamarin ya jawo an raunata mutane da dama, tare da mutuwar aƙalla mutum biyar.
Wani daga cikin shugabannin ƙungiyar, Sheikh Sidi Sokoto, ya yi iƙirarin cewa jami’an sojoji sun kai wa mambobinsu hari ba tare da sun tsokane su ba.
Ƴan sanda sun karyata mabiya Shi'a
Da yake mayar da martani kan lamarin, kwamishinan ƴan sanda na babban birnin tarayya Abuja, Ajao Saka Adewale, ya nuna mamaki kan abin da ya haddasa arangamar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Adewale, wanda ya yi magana ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan Abuja, Josephine Adeh, ya bayyana cewa an tabbatar mutuwar mutum ɗaya a Asibitin Ƙasa da ke Abuja.
"A ranar 28 ga Maris, 2025, da misalin karfe 2:20 na rana, rundunar ƴan sandan Abuja ta samu kiran gaggawa cewa mambobin IMN sun kai wa jami’an tsaro hari da makamai irin su ɗankuna, sanduna, duwatsu da sauran muggan makamai a yankin Banex, Aminu Kano Crescent, Wuse 2."

Kara karanta wannan
Shugabannin SDP sun ziyarci mai martaba sarki, ya tsage masu gaskiya kan yaudarar jama'a
"Bayan an tura jami’an tsaro cikin gaggawa zuwa wurin, sun fuskanci ruwan wuta daga masu kawo harin, wanda hakan ya sanya aka jikkata jami’an tsaro guda uku."
"An gaggauta kai su Asibitin Kasa, inda aka tabbatar da mutuwar ɗaya daga cikinsu."
"An kama mutane 19 da ake zargi da hannu a wannan lamarin, yayin da wasu suka tsere."
"Zaman lafiya ya dawo bayan shawo kan lamarin kuma ana ci gaba da bincike don tabbatar da cewa duk masu hannu a wannan aika-aikar sun fuskanci hukunci."
- Josephine Adeh
Ƴan shi'a sun zargi jami'an tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa mambobin ƙungiyar Shi'a a Najeriya sun zargi jami'an tsaro da tarwatsa musu taro a babban birnin tarayya Abuja.
Ƙungiyar ta Shi'a ta nuna yatsa ne ga jami'an tsaron kan tarwatsa taron Nisfu Sha'aban da suke gudanarwa domin tunawa da haihuwar Imam Mahdi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng