"Ba Yau Aka Fara ba," Gwamnatin Kano Ta Yi Zazzafan Martani kan Kisan Ƴan Arewa a Edo

"Ba Yau Aka Fara ba," Gwamnatin Kano Ta Yi Zazzafan Martani kan Kisan Ƴan Arewa a Edo

  • Gwamnatin Kano karƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta nuna damuwa kan kisan gillar da aka yi wa wasu mafarauta a Edo
  • Mai girma gwamna ya buƙaci hukumomin tsaro su gudanar da cikakken bincike tare da bayyana wa ƴan ƙasa gaskiyar abin da ya faru
  • Abba ya ce wannan ba shi ne karo na farko da aka yi wa bayin Allah kisan gilla ba, ya na mai cewa dole a hukunta masu hannu a lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana matuƙar jimaminta kan kisan gillar da aka yi wa wasu matafiya a garin Uromi, Jihar Edo.

Ta ce wannan danyen aiki da ya lakume rayukan akalla mutum 16, ya zama abin takaici da dole ne hukumomin tsaro da na shari’a su dauki matakin gaggawa don ganin an yi adalci.

Kara karanta wannan

Bayan kona 'yan Arewa kurmus a Edo, an kashe mutane 10 da ke zaman makoki a Filato

Gwamna Abba.
Gwamnatin Kano ta yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa ƴan Arewa a Edo, ta bukaci a yi gaggawar yin bincike Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun kwamishinan yaɗa labarai na Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya wanda kuma Gwamna Abba Kabir ya wallafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kashe ƴan Arewa a Edo

Rahotanni sun nuna cewa mutanen da aka kashe galibi masunta ne kuma suna kan hanyarsu daga Fatakwal zuwa Kano don gudanar da bukukuwan Sallah tare da iyalansu.

Sai dai, wasu ‘yan sintiri da matasa dauke da makamai sun tare su, suka farmake su, suka jibge su, sannan suka daure su da tayoyi, suka cinna masu wuta.

Gwamnatin Kano ta ce wannan danyen aiki tashin hankali ne ga iyalan mamatan, kuma yana kara nuna yadda daukar doka a hannu ke yawaita a kasar nan.

"Idan har ba a hukunta wadanda suka aikata wannan ta’asa ba, hakan zai ci gaba da rage wa jama’a kwarin gwiwa kan ikon gwamnati na kare rayuka da doka da oda." in ji sanarwar.

Kara karanta wannan

A ƙarshe, Shugaba Tinubu ya yi maganar kisan da aka yi wa ƴan Arewa a jihar Edo

Gwamnatin Kano ta buƙaci a yi bincike

Gwamnatin Kano ta yi kira da a gudanar da bincike cikin gaggawa da kuma bayyana gaskiya kan wannan lamari.

Ta ce dole ne a hukunta duk wanda ke da hannu a wannan aika-aika, ciki har da jami’an tsaro da suka yi sakaci da aikinsu.

Gwamnatin ta ƙara da cewa ya zama dole a tabbatar da cewa an dauki matakin doka kan duk wani nau’in zalunci ko azabtarwa da ake yi wa ‘yan kasa.

"Muna kira ga Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Monday Okpebholo da su bayyana matsayarsu a fili kan wannan lamarin tare da tabbatar da cewa an yi adalci.
Wannan lamarin na Uromi ba shi ne na farko ba a jerin irin wadannan kisan gilla da ke faruwa a kasar nan. Ana bukatar daukar matakan da suka dace don hana yawaitar irin wannan ta’asa.

- In ji Ibrahim Abdullahi Waiya.

Kara karanta wannan

Sheikh Pantami ya jero hanyoyi 3 da za a kama waɗanda suka kashe yan Arewa a Edo

Gwamnatin Kano ta jaddada cewa tana tare da ƴan Najeriya wajen yin Allah-wadai da wannan danyen aiki tare da bukatar daukar matakin gaggawa domin hana sake faruwarsa.

Bola Tinubu ya ɗauki matakai kan kisan Edo

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin a gaggauta kama waɗanda suka kashe mafarauta da ke hanyar zuwa Kano daga Edo.

Shugaban kasa ya jajanta wa iyalan mamatan, ya na mai tabbatar musu da cewa ba za a bar bata-gari su ci gaba da zubar da jinin bayin Allah haka kurum ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng