Gwamna Ya Yi Magana da Aka Yi Wa Ƴan Arewa Kisan 'Wulakanci' a Jihar Edo

Gwamna Ya Yi Magana da Aka Yi Wa Ƴan Arewa Kisan 'Wulakanci' a Jihar Edo

  • Gwamna Monday Okpebholo ya yi Allah wadai da kisan matafiya ƴan Arewa a garin Uromi da ke ƙaramar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas
  • Okpebholo ya ba da umarnin gudanar da bincike domin hukunta duk mai hannu a aikata wannan ɗanyen aiki
  • Tun farko dai wasu matasa sun ƙone Hausawa da ke hanyar dawowa gida domin shagalin ƙaramar sallah bisa zargin cewa masu garkuwa ne

Edo - Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya yi Allah wadai da kisan gilla da wasu matasa suka yi wa Hausawa ‘yan Arewa a garin Uromi da ke karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas.

An ce matasan sun ƙona ƴan Arewan da ke hanyar dawowa gida domin shagalin sallah bisa zargin ƴan garkuwa da mutane ne.

Gwamna Okpebholo.
Gwamnan Edo ya yi Allah wadai da kisan ƴan Arewa a Uromi Hoto: Monday Okpebholo
Asali: Twitter

Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na manhajar X.

Gwamma Okpebholo ya yi Allah wadai

Kara karanta wannan

Kisan 'rashin imani' da aka yi wa 'yan Arewa ya tada ƙura, Kwankwaso ya maida martani

Gwamnan ya yi tir da wannan ɗanyen aiki a wata sanarwa da babban jami'in tsaro (CSO) na fadar gwamnatin Edo, SP Solomon Osaghale ya fitar yau Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Monday Okpebholo ya bayyana cewa abin da ya faru rashin imani ne kuma ba za a lamunta ba, inda ya jaddada cewa za a gurfanar da duk wanda ke da hannu a wannan aika-aika a gaban kotu.

Yadda lamarin ya faru a jihar Edo

Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna, Fred Itua, ya bayyana cewa bincike ya nuna matafiyan sun kasance fasinjoji a cikin wata mota kirar tirela da aka tsaida.

A yayin binciken da ƴan sa-kai suka yi, an gano makamai a cikin motar, wanda hakan ya haddasa zargi daga mutanen gari, nan take suka hau kansu.

Gwamnan Okpebholo ya gargaɗi jama’a cewa babu wanda ke da ikon yanke hukunci da karfi ko daukar doka a hannunsa.

Kara karanta wannan

Rigimar Gide da Aliero ta rikice bayan kisan rikakken ɗan bindiga, an kira taron gaggawa

Wane mataki gwamnan Edo ya ɗauka?

“Lokacin da Gwamna Okpebholo ya samu labarin wannan lamari, ya umarce ni da in ziyarci wurin domin gano hakikanin abin da ya faru.
“Haka kuma ya umurci Kwamishinan ‘Yan Sanda da ya gudanar da cikakken bincike a kan lamarin. A halin yanzu, an kama mutum hudu da ake zargi da hannu a harin.”

- in ji Osaghale.

Gwamna ya buƙaci a kwantar da hankali

Gwamnan ya bukaci jama’a su zauna lafiya, yana mai tabbatar wa Hausawa da ke Uromi cewa jami’an tsaro sun dauki mataki domin kare rayukansu da dukiyoyinsu.

Shugaban al’ummar Hausawa a Uromi, Aliyu Haruna, ya yaba wa gwamnatin jihar Edo bisa gaggawar daukar mataki kan lamarin.

“Tun fiye da shekaru 70 muna zaune lafiya a wannan gari, kuma mutane Uromi mutane ne masu kyakkyawan hali,” in ji Haruna.

Ya ce an samu zaman lafiya a baya kuma irin wannan mummunan al'amari bai taba faruwa a tarihin Uromi ba.

Kara karanta wannan

Kano: Abin da Reno Omokri ya ce bayan ƙone Hausawa a Edo, ya shawarci ƴan Arewa

Omokri ya yi tir da kisan ƴan Arewa

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ya yi Allah wadai da kisan ƴan Arewa da ke hanyar komawa gida a jihar Edo.

Omokri ya bukaci gwamnatin Edo da ta dauki matakin gaggawa domin hukunta masu hannu a lamarin, ya na mai jaddada cewa wannan abin bakin ciki ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel