Rikicin Sarauta: 'Yan Sanda Sun Hana Hawan Sallah a Jihar Kano
- Rahotanni na nuni da cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano ta hana hawan sallah da ake shirin gudanarwa
- Hakan na zuwa ne bayan mai martaba Aminu Ado Bayero ya sanar da janye hawan sallah da ya ce zai gudanar
- Matakin zai shafi bangaren mai martaba Muhammadu Sanusi II da ya riga ya fitar da sanarwa kan yadda zai gudanar da hawan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta sanar da cewa ta hana gudanar da hawan sallah a jihar.
Hakan na zuwa ne bayan kura ta fara lafawa a kan rikicin da ya kunno kai kan hawan sallah da bangaren Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II suka ce za su yi.

Asali: Twitter
Kakakin 'yan sandan jihar, Haruna Abdullahi Kiyawa ne ya fitar da sanarwar hana hawan sallar a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kiyawa ya bayyana cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori ne ya sanar da matakin a wani taron manema labarai da aka gudanar a hedkwatar ‘yan sanda da ke Bompai.
Ya bayyana cewa rundunar ta dauki matakin ne bayan tattaunawa da gwamnatin jihar da sauran masu ruwa da tsaki, domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
Dalilan haramta hawan sallah a Kano
Kwamishinan ‘yan sanda ya bayyana cewa rahotannin sirri sun nuna cewa akwai wasu bata-gari da ke shirin amfani da hawan Sallah domin tayar da rikici a jihar.
Ya ce rundunar ta yi dubi sosai tare da tuntubar bangarori daban-daban, kuma an yanke shawarar haramta hawan ne domin gujewa duk wani tashin hankali da ka iya biyo baya.
A cewarsa, manufar hukuncin ita ce tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Kano, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar matsin lamba kan harkokin siyasa da sarauta.

Asali: Facebook
'Yan sandan Kano sun gargadi jama’a
Kwamishinan ya bukaci jama’a da su gudanar da sallarsu a filayen idi kamar yadda aka saba a baya, domin gujewa duk wata matsala ta rashin tsaro.
Haka kuma, ya lissafo wasu dokoki da ya kamata jama’a su kiyaye yayin bukukuwan Sallah:
- Kada a zo da duk wani abu da ka iya janyo tsoro ko fargaba ga jama’a.
- An haramta yin tseren dawakai (Kilisa), tseren motoci ko tuƙin ganganci.
- Iyaye su kula da ‘ya’yansu, kada a yaudare su a yi amfani da su wajen tayar da rikici.
- Duk wani abu da ka iya haddasa rashin zaman lafiya ya kamata a guje masa.
Kira ga jama’a kan hadin kai
Kwamishinan ya bukaci jama’a da su ci gaba da zama lafiya da junansu tare da gujewa duk wata fitina da ka iya kawo rudani a jihar.
Ya jaddada cewa zaman lafiya shine ginshikin ci gaban kasa, don haka kowa ya dauki nauyin tabbatar da tsaro a cikin al’umma.
Har ila yau, ya bukaci jama’a da su rika kai rahoton duk wani abu da suka ga yana da alamar barazana ga tsaro, ta hanyar tuntubar ‘yan sanda ko amfani da lambobin gaggawa kamar haka:
- 08032419754
- 08123821575
- 09029292926
Haka kuma, an bukaci jama’a su yi amfani da manhajar NPF Rescue Me ko shafukan sada zumunta na rundunar ‘yan sanda domin tuntuɓa.
Yanzu haka dai an zuba ido aga matakin da gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf za ta dauka kan bayanin da 'yan sanda suka yi.
An kashe 'yan Arewa 16 a Edo
A wani rahoton, kun ji cewa wasu matasa a jihar Edo sun kashe mutane 16 sun kona su kurmus bayan sun fito daga Fatakwal zuwa Kano.
Rahotanni sun tabbatar da cewa mutanen 'yan farauta ne kuma sun kama hanyar dowowa gida ne daga Kudu zuwa Arewa domin bikin sallar azumi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng