Sallah: Sarkin Musulmi Ya Bukaci a Fara Duba Watan Shawwal a Najeriya

Sallah: Sarkin Musulmi Ya Bukaci a Fara Duba Watan Shawwal a Najeriya

  • Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bukaci daukacin al'ummar Musulmi a Najeriya su kalla jinjirin watan Shawwal 1446AH
  • Farfesa Sambo Wali Junaidu, Wazirin Sakkwato, ya fitar da sanarwa cewa al'ummar Musulmi su yi tsayin daka wajen neman jinjirin watan a ranar Asabar
  • An fitar da lambobin waya na musamman da al'umma za su iya amfani da su wajen tuntuɓar Sarkin Musulmi domin bayar da rahoton ganin jinjirin watan
  • Duban watan Shawwal yana da matukar muhimmanci wajen tabbatar da karewar watan azumi da kuma shigowar watan Shawwal da za a yi bikin sallah karama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto - Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci daukacin al’ummar Musulmi a Najeriya da su kalla jinjirin watan Shawwal 1446AH a ranar Asabar, 29 ga Maris, 2025.

Kara karanta wannan

Shugaban hadakar PDP ya yi Allah wadai da jita-jitar da ake yada wa kan Atiku

Wannan kira ya fito ne daga cikin sanarwa da Farfesa Sambo Wali Junaidu, Wazirin Sakkwato kuma Shugaban kwamitin tuntuba kan harkokin addini na fadar Sarkin musulmi ya fitar.

Sarki
Za a fara duba watan Shawwal Hoto: Sultanate Council Sokoto Public Relations Unit/Gleb Fjodoroff
Asali: Facebook

A sanarwar da fadar ta wallafa a shafinta na Facebook, Sultan, wanda shi ne Shugaban majalisar kolin harkokin addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), su fara duban wata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa su yi tsayin daka wajen neman jinjirin wata tare da sanar da hukuma idan sun hango shi a cikin gaggawa.

Za a fara neman jinjirin watan Shawwal

Jaridar Aminiya ta ruwaito jaddada cewa duk wanda ya ga jinjirin watan Shawwal ya gaggauta sanar da hakimin yankinsa ko dagacin garinsu, domin a isar da sakon zuwa ga Masarautar Sakkwato.

Haka kuma, an fitar da lambobin waya na musamman da za a iya tuntubar Mai Alfarma kai tsaye don bayar da rahoton hangen wata.

Lambobin sun hada da 08037157100, 08066303077, 08035965322, 08035945903 da kuma 07067146900 domin isar da sakon cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi martani ga Amurka kan zargin kashe kiristoci karkashin Tinubu

Muhimmancin duban watan Shawwal

Duban watan Shawwal yana da matukar muhimmanci a tsarin addinin Musulunci, domin yana tabbatar da karewar watan azumi tare da kawo babban bikin Idin Karama (Eid al-Fitr).

Sarki
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III Hoto: Sultanate Council Sokoto Public Relations Unit
Asali: Facebook

Idan aka ga watan a daren Asabar, to ranar Lahadi, 30 ga Maris, 2025, za ta kasance ranar Idi, amma idan ba a ga watan ba, Ramadan zai cika kwana 30, kuma za a gudanar da sallar Idi a ranar Litinin, 31 ga Maris, 2025.

An fadi yadda ake neman watan Shawwal

A wani labarin, kun ji cewa daya daga cikin ƴan kwamitin ganin wata na fadar Sarkin Musulmi, Simwal Usman Jibrin, ya bayyana yadda ake duban wata da tantancewa kafin a sanar a Najeriya.

Malam Simwal ya bayyana cewa, idan kwamitin ganin wata ya tattara dukkan rahotannin da aka samu daga yankunan daban-daban, rahoton yana miƙa wa Sarkin Musulmi domin yanke hukuncin ƙarshe.

Malam Simwal, wanda masanin ilimin taurari ne, ya ƙara da cewa, a kowane shekara, kwamitin yana samun rahotanni daga al'ummar Musulmi a cikin ƙasar da ke tallafawa ganin wata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng