'Dalilin da Ya Sa Aminu Ado ba Zai Taba Iya Gudanar da Hawan Sallah a Kano ba'

'Dalilin da Ya Sa Aminu Ado ba Zai Taba Iya Gudanar da Hawan Sallah a Kano ba'

  • Masanin tarihi, Malam Ibrahim Ado Kurawa ya ce ba zai yiwu Aminu Bayero ya yi hawan sallah ba tun da ba shi da ikon gudanarwa a al'ada
  • Kurawa ya ce hawa ya na da tsari da ka'idoji sama da shekaru 500, kuma dole ne a gudanar da shi daga fadar Gidan Rumfa, ba wani wuri ba
  • Ya ce kokarin Aminu Bayero ba hawan sallah ba ne, sai dai hawan doki, kuma ya na haddasa rikici ne saboda goyon bayan gwamnatin tarayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - An bayyana janyewar Aminu Ado Bayero daga shirya hawan sallah a Kano a matsayin abin dariya kawai, ba wani abin da aka tsara ba.

Wani masanin tarihi, Malam Ibrahim Ado Kurawa ya ce Aminu Ado ba zai iya shirya hawan sallah ba tun da ba shi da kayan al'ada da ke ba shi damar yin hakan.

Kara karanta wannan

Bayan Aminu Ado ya janye, Sanusi II ya fitar da jadawalin hawan sallah a Kano

Masanin tarihi ya fadi dalilin Aminu Ado na shirin hawan sallah tun farko
Wani masanin tarihi ya tona dalilin da ya sa Aminu Ado ba zai iya hawan sallah ba. Hoto: Masarautar Kano.
Asali: Facebook

Hawan sallah: Masanin tarihi ya fayyace komai

Kurawa, masani kan tarihin Kano, ya ce ba zai yiwu a canza tsarin hawa mai shekaru sama da 500 ba don biyan bukatun siyasa, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masanin ya kara da cewa Aminu Bayero ba shi da fadawa kamar Shamaki, Dan Rimi, Madakin Shamaki da Sallama da ke jagorantar hawa.

Ya kuma ce Makaman Kano ne ke jagorantar tafiyar hawa, amma babu daya daga cikinsu da ke tare da Aminu Ado Bayero a halin yanzu.

Kurawa ya ce:

"Hawa na da tsari da ka'idoji, ba za a iya yin sa ba sai daga Gidan Rumfa, inda aka fara gudanar da shi tun farko.
“Misali, idan Sarki zai fita zuwa Sallar Idi, sai ya fito daga Kofar Fatalwa sanye da fararen kaya, sannan ya tafi har masallacin Idi.
“Bayan Sallah, sai ya bi wata hanya daban don ya yi jawabi ga jama’a kafin ya koma fadar Gidan Rumfa ta wani kofa daban.”

Kara karanta wannan

'Aminu Ado ka hakura da mulkin Kano,' Kiran jama'a bayan janye hawan sallah

“Idan kuma Sarki zai kai wa mahaifiyarsa ziyara, yana bin wata hanya ta musamman wadda aka tsara tun shekaru 500 da suka gabata.”
Aminu Ado ya janye daga hawan sallah a Kano
Masanin tarihi ya fayyace ka'idoji da ke cikin hawan sallah a Kano. Hoto: Sanusi Bature Dawakin-Tofa, Masarautar Kano.
Asali: Twitter

An zargi gwamnatin tarayya da rikita lamura

Kurawa ya bayyana cewa Aminu Bayero ba shi da ikon gudanar da hawan sallah, domin ba shi da fada a Gidan Rumfa da ke da wannan iko.

Ya kara da cewa:

“Don haka, abin da ya yi ba shirin hawa ba ne, sai dai hawan doki kawai, hawa ya na da tarihi da ka’ida da ba za a iya canzawa ba.”
“Shi ne ma ya fara haddasa rikici a farko. Idan yanzu ya daina, mu na yaba masa. Amma ya na samun goyon bayan gwamnatin tarayya.”

Kurawa ya ce da gwamnatin tarayya ba ta tsoma baki ba, da tun farko gwamnatin jiha ta magance lamarin cikin sauki ba tare da matsala ba.

Dalilin janye hawan sallah

A cewar wasu rahotanni, Aminu Ado Bayero ya fada cikin wani yanayi mai sarkakiya bayan da ya janye daga shirya hawan sallah a Kano a ranar 26 ga Maris, 2025, saboda matsalolin tsaro da aka nuna a wani jawabi da ya yi a cikin dare.

Kara karanta wannan

Abin da Shehu Sani ya ce bayan Aminu Ado ya janye hawan sallah, ya shawarci Sanusi II

Wannan mataki ya biyo bayan tashin hankali da ya kunno kai tsakanin masu goyon bayansa da gwamnatin jihar Kano, inda aka zarge shi da kokarin kafa iko a kan al’adar da ba ta karkashinsa ba.

A lokacin da yake shirin yin hawan, jama’a sun ji dadin ganin yadda zai farfado da wannan al’ada mai daraja, amma sai aka ga an samu sabani da masu adawa da shi.

Gwamnatin jihar Kano, a karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta nuna rashin amincewa da wannan shiri, inda ta ce ba shi da wani matsayi a hukumance don gudanar da irin wannan taro.

Ra'ayoyin sauran masu sarauta a Kano

An kuma ce wasu daga cikin manyan sarakunan gargajiya, wadanda suke da alaka da Gidan Rumfa, sun ki bin Aminu saboda rashin samun goyon bayan da ya dace daga al’ummar Kano.

Wannan ya haifar da rudani a tsakanin al’umma, inda wasu ke ganin cewa gwamnatin tarayya na kokarin shiga tsakani don tallafa masa.

Kara karanta wannan

"Sun haƙura?" An saki bidiyon Sanusi II bayan Aminu Ado ya janye hawan sallah a Kano

A wani bangare, masana sun ce hawan sallah ba wai kawai taron biki ne ba, alama ce ta iko da tarihi mai zurfi a cikin al’adar Hausa.

Saboda haka, duk wani yunkuri na canza wannan tsari na iya haifar da tashin hankali. A halin yanzu, bayan janyewar Aminu, an samu kwanciyar hankali a garin, amma har yanzu ana ci gaba da tattaunawa kan yadda za a magance wannan matsala ta dindindin.

Wasu na ganin cewa wannan lamari zai iya zama wani babban gwaji ga gwamnatin jihar Kano da kuma gwamnatin tarayya wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Sarki Sanusi II ya shirya fita hawan sallah

Kun ji cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya fitar da sanarwa kan yadda zai gudanar da bikin hawan sallah a Kano.

Mai martaba Sanusi II ya fitar da jadawalin ne bayan Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya janye hawan sallah a jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng