Da Gaske Atiku Ya Karbi Miliyoyin Naira daga Gwamnan Legas a Lokacin Zaben 2023?
- Atiku Abubakar ya musanta karbar kudi daga Gwamna Sanwo-Olu, yana mai cewa zarge-zargen karya ne da aka kirkira don bata sunansa
- Atiku ya bukaci jama’a su yi watsi da rahotannin, yana mai cewa ya gudanar da yakin neman zabensa da kudadensa ba tare da almundahana ba
- Tawagar Atiku ta kalubalanci EFCC da ta fito da sakamakon bincikenta, yayin da ta yi zargin cewa ana son mayar da zargin makamin siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya karyata zargin da ke danganta shi da karbar wasu kudi da aka ciro su daga asusun jihar Legas.
A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan yada labarai, Paul Ibe, ya fitar, Atiku ya musanta karbar kudi daga hannun Gwamna Babajide Sanwo-Olu a lokacin zaben 2023.

Asali: Twitter
Atiku ya karyata karbar kudin jihar Legas
Ofishin yada labaran Atiku ya bayyana rahotannin a matsayin marasa tushe, yana mai cewa an kirkiro su ne domin bata sunansa gabanin zaben 2027, inji Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta bukaci jama’a su yi watsi da zarge-zargen, tana mai jaddada cewa Atiku ya gudanar da yakin neman zabensa cikin gaskiya, ba tare da wata alaka da kudin jihar Legas ba.
Paul Ibe ya fitar da sanarwar dauke da taken: "A dakatar da wannan makircin na Tinubu na bata sunan Atiku Abubakar."
A cikin sanarwar, ya bayyana zarge-zargen a matsayin “karya tsagwaronta” da kuma “kirkirarrun abubuwa don bata suna” da nufin rage darajar Atiku.
"Babu wata alaka tsakanin Atiku da Sanwo-Olu"
Mai magana da yawun tsohon mataimakin shugaban kasar, ya jaddada cewa: "Wazirin Adamawa bai san Gwamna Sanwo-Olu ba, kuma bai taba haduwa da shi ba."
Sanarwar ta kara da cewa:
"Babu wata alaka tsakanin Atiku da Sanwo-Olu, don haka, zargin cewa ya karbi kudi daga gwamnan yayin zaben 2023 ba shi da tushe ko makama."
Tawagar Atiku ta yi ikirarin cewa rahotannin wani yunkuri ne na siyasa da ke neman bata sunan Gwamna Sanwo-Olu da kuma ‘yan adawa, ciki har da Atiku.
Tawagar Atiku ta kalubalanci hukumar EFCC
Paul Ibe ya kuma kalubalanci hukumar EFCC da ake cewa tana binciken lamarin, da ta fito da sakamakon bincikenta, yana mai cewa ana amfani da zargin a matsayin makamin siyasa.
"Tun da an ce hukumar EFCC ta shiga cikin wannan batu, muna kalubalantarta da ta bayyana sakamakon bincikenta kowa ya gani.
"’Yan Najeriya, ciki har da Atiku da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, sun cancanci a su san gaskiya."
- Inji sanarwar Paul Ibe.
Tawagar Atiku ta bukaci bangaren Shugaba Bola Tinubu da ya daina amfani da siyasar bata suna, tana mai gargadi cewa irin wadannan hanyoyi ba za su hana ‘yan adawa ci gaba da shirinsu na siyasa ba.

Kara karanta wannan
2027: Ta fara tsami tsakanin ƴan adawa, burin Atiku da maganar yanki na son ta da kura
Karanta sanarwar da Paul Ibe ya wallafa a shafinsa na X a nan kasa:
Asali: Legit.ng