Bayan Aminu Ado Ya Janye, Sanusi II Ya Fitar da Jadawalin Hawan Sallah a Kano
- Bayan Aminu Ado Bayero ya janye hawan sallah, Muhammadu Sanusi II ya fitar da sanarwa kan yadda bikin zai gudana a Kano
- Masarautar Kano ta wallafa jadawalin hawan sallah a shafinta na X, inda aka bayyana hanyoyin da Sarki Sanusi II zai bi a Kano
- Mai martaba Sanusi II ya fara sanarwar da taya sabon kwamishinan ‘yan sanda maraba, tare da yi masa fatan alheri a bakin aikinsa
- A ranar farko, hawan zai fara daga Kofar Fatalwa zuwa Rimin Kira, Shahuci, Asibiti da Kofar Mala har zuwa masallacin Idi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Awanni bayan janye hawan sallah da Aminu Ado Bayero ya yi, Muhammadu Sanusi II ya fitar da sanarwa.
Sarki Muhammadu Sanusi II ya fitar da jadawalin yadda bikin hawan sallah zai gudanar a birnin Kano.

Asali: Twitter
Aminu Ado Bayero ya hakura da hawan sallah
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin Masarautar Kano ya wallafa a shafin X a yammacin yau Alhamis 27 ga watan Maris, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na zuwa ne bayan Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya duba al'ummar jihar inda ya janye shirin hawan sallah.
Yayin da mazauna Kano ke cikin fargabar abin da zai faru a bukukuwan hawan Sallah, Aminu Ado Bayero ya fitar da matsaya kan lamarin.
Basaraken ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan shawarwari daga malamai, iyaye, shugabanni, da masu ruwa da tsaki a masarauta.
Ya bukaci jama’a da su yi hakuri da wannan mataki tare da amfani da bukukuwan sallah wajen sada zumunci da ƴan uwa a Kano.

Asali: Twitter
Sanusi II ya fitar da sanarwar hawan sallah
A cikin sanarwar, Sarki Sanusi II ya fara da yi wa sabon kwamishinan yan sanda barka da zuwa Kano tare da yi masa fatan alheri.
Sanarwar da sakataren kwamitin hawan, Alhaji Aliyu Harazimi Umar ya sanya hannu ta ce za a fita ranar farko daga ƙarfe 8:00 zuwa 9:00 na safe.
Ta ce a ranar farko, Sarkin zai fara bin hanyoyin Kofar Fatalwa zuwa Rimin Kira har Shahuci zuwa Asibiti da Kofar Mala har masallacin Idi.
Har ila yau, bayan idar da sallar idi, Sarki zai bi Kofar Wambai zuwa Zage zuwa Shahuci har Gidan Shattima zuwa Kofar Arewa.
Mai Martaba ya ce a rana ta biyu zai yi hawan daushe daga karfe 4:00 zuwa 6:30 na yamma.
Sarkin zai fara hawan ne inda zai fito daga Kofar Arewa misalin karfe 4:30, zai bi titin babban masallacin Juma'a da ke yamma da gidan Sarki ya je babban Daki.
Sanusi II ya magantu bayan janyewar Aminu Ado
Kun ji cewa Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya sanar da janye shirin hawan sallah saboda masalahar zaman lafiya.

Kara karanta wannan
Abin da Shehu Sani ya ce bayan Aminu Ado ya janye hawan sallah, ya shawarci Sanusi II
An ce jim kaɗan bayan haka ne aka saki wani bidiyo da Muhammadu Sanusi II ke tambayar shin 'sun haƙura?' cikin zolaya da barkwanci.
Rahotanni sun ce wasu malamai kamar Sheikh Lawan Abubakar Triumph sun sanya baki kan batun hawan sallah, suka roki Aminu Ado Bayero ya yi haƙuri.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng