Tinubu Zai Cika Shekaru 73 da Haihuwa, Za a Tattaro Malamai Su Yi Addu'o'i a Abuja
- Shugaba Bola Tinubu zai cika shekaru 73 a ranar Asabar, 29 ga Maris, kuma zai yi bikin zagayowar ranar haihuwarsa ta hanyar taron addu’o'i
- A cewar mai magana da yawunsa, Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya su yi addu’a domin samun shiriya, hadin kai da waraka ga kasar nan
- Tinubu ya gode wa Allah SWT bisa tsawaita rayuwarsa da kuma damar da ya ba shi na shugabancin Najeriya, yana mai fatan samun ci gaba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Fadar shugaban kasa ta ce Bola Tinubu zai yi bikin cika shekaru 73 ta hanyar yin gangamin addu'o'i na musamman a masallacin kasa da ke Abuja.
Rahotanni sun bayya cewa, Shugaba Tinubu zai cika shekaru 73 da haihuwa a ranar Asabar, 29 ga watan Maris 2025.

Kara karanta wannan
Sanata Kalu ya watsa wa matasan Arewa ƙasa a ido, ya yi maganar karawa da Tinubu a 2027

Asali: Twitter
Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaban kasar, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu zai shirya taron addu'o'i a Abuja
Sanarwar ta bayyana cewa, Shugaba Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya su yi addu’a domin samun shiriya daga Allah, hadin kai da waraka ga kasar nan.
A cewar Onanuga, shugaban kasar zai sadaukar da zagayowar ranar haihuwarsa ta hanyar komawa ga Allah da yin addu’o’i domin wanzuwa zaman lafiya, cigaba da wadata a Najeriya.
Sanarwar ta ce:
“Kafin zagayowar ranar cikarsa shekaru 73 da haihuwa a ranar Asabar, Shugaba Bola Tinubu, zai halarci taron addu’o'i na musamman a masallacin Kasa da ke Abuja a ranar Juma’a domin rokon albarka ga Najeriya.
"Haka kuma, zai yi amfani da wannan dama wajen gode wa Allah bisa tsawaita rayuwarsa da ya yi, da kuma ba shi dama don jagorantar al’amuran kasa."
Tinubu ya nemi 'yan Najeriya su dage da addu'a
Sanarwar Bayo Onanuga ta ci gaba da cewa:
"Ranar haihuwar shugaban kasa ta zo daidai da watan Ramadan mai alfarma, kuma wata biyu kafin cika shekara biyu da hawa kan mulki.
"A wannan rana mai muhimmanci, Shugaba Tinubu zai sadaukar da kansa ga tunani da addu’o'i domin dorewar zaman lafiya, ci gaban kasa da wadata ga Najeriya.
"Yanke shawar gudanar da taron addu’o'in na nuna jajircewar Shugaba Tinubu ga wajen neman shiriya, hikima da karfi daga Allah wajen shugabancin Najeriya.
"Shugaban kasar ya yi imani da cewa yin addu’a ta bai daya ya na da matukar muhimmanci wajen jagorantar kasar zuwa ga cigaba da kuma samun daidaito.
"Ya bayyana matukar godiyarsa ga ‘yan Najeriya bisa goyon baya da fatan alheri da suke masa, a yayin da gwamnatinsa ke aiki tukuru don inganta tattalin arziki, karfafa tsaro, da fadada damammaki ga ‘yan kasa."
"Mu yi addu'ar samun shiriya" - Tinubu
Sanarwar ta ruwaito Shugaba Tinubu ya na cewa:
“Ina matukar godiya ga Allah bisa tsawaita rai na da kuma damar da ya ba ni na yi wa wannan babbar kasa hidima. Yayin da nake murnar zagayowar ranar haihuwa ta, da cika shekaru biyu a kan mulki, zuciyata cike take da sabon fata ga Najeriya.
"Ina kira ga ‘yan kasa da su yi addu’a don samun shiriya daga Allah, hadin kai, da waraka ga kasar mu. Idan muka hada kai, za mu iya shawo kan kowane kalubale kuma mu gina kasar da kowa zai samu cigaba.”
Ya tabbatar da kudirinsa na karfafa dimokuradiyya, farfado da tattalin arziki, da bunkasa hadin kan kasa.
Shugaba Tinubu ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da dogara da makomar kasar a matsayin abin alfahari a nahiyar Afirka.
Karanta sanarwar a nan:
Yadda aka taya Tinubu murnar cika shekaru 72

Kara karanta wannan
'Wani gwamnan Najeriya zai mutu kafin 2027': Malami ya hango makomar Atiku, Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, fitattun mutane da shugabanni na gida da wajen Najeriya, sun taya Shugaba Bola Tinubu murna, lokacin da ya cika shekaru 72.
Daga cikin wadanda suka aika wa Tinubu sakon 'murnar karin shekara', akwai Shugaba Muhammadu Buhari, Sanata Godswill Akpabio, jam'iyyar APC da sauransu.
Asali: Legit.ng