Tsohon Hadimin Osinbajo Ya Zuga Fubara, Ya Fadi Abin Ya Dace Ya Yi Wa Tinubu
- Laolu Akande ya shawarci gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara da ya ƙalubalanci dakatarwar da aka yi masa a gaban kotu
- Tsohon mai magana da yawun bakin Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa bai kamata Fubara ya jira har sai gwamnonin PDP sun shigar da ƙara ba
- A cewarsa akwai alamun tambaya kan dakatarwar da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi wa gwamnan na jihar Rivers
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon mai magana da yawun Yemi Osinbajo, Laolu Akande, ya ba Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers shawara kan dakatarwar da aka yi masa.
Tsohon hadimin na Osinbajo ce ya kamata Siminalayi Fubara ya kasance mutum na farko da zai ƙalubalanci dakatarwar da shugaba Bola Tinubu ya yi masa a matsayin gwamnan jihar Rivers.

Asali: Twitter
Laolu Akande ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Sunrise Daily'.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Akande da a ce an dakatar da Tinubu a lokacin da yake gwamnan Legas daga watan Mayu 1999 zuwa Mayu 2007, da ya yi gaggawar zuwa Kotun Koli don ƙalubalantar matakin.
Tinubu, wanda ke cikin adawa a lokacin da yake gwamnan Legas, ya ƙalubalanci ƙin sakin ƙuɗin ƙananan hukumomin jihar da gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ta yi.
Wace shawara Akande ya ba gwamna Fubara?
Tsohon hadimin shugaban ƙasar ya ce bai kamata Fubara ya jira har sai gwamnonin jam’iyyarsa ta PDP guda bakwai sun kai ƙara Kotun Koli ba domin ƙalubalantar dakatarwar da aka yi masa na tsawon watanni shida.
Akande ya koka cewa Fubara bai da zuciya, ya na mai jaddada cewa ya saɓa doka shugaban ƙasa da aka zaɓa ya dakatar da gwamnan da aka zaɓa ta irin wannan hanya.
"Abin da gwamnonin PDP suka yi abu ne mai kyau. Wataƙila hakan zai iya ceto al’amura. Amma abin mamaki ne yadda Gwamna Fubara ya tsaya sakaka kawai."
"Idan wani ya yi wa Bola Ahmed Tinubu haka a lokacin da yake gwamnan Legas, ka san abin da zai aikata?"
"Ya kamata Fubara ya kasance na farko da zai garzaya kotu, har yanzu shi ne gwamna kuma ba a cire shi ba. Ba za a iya cire shi ta haka ba. Akwai alamun tambaya kan wannan dakatarwar da aka yi masa."
"Abu na farko da ya kamata Gwamna Fubara ya yi, idan da ya san abin da yake yi, shi ne garzayawa kotu. Ya kuma bayyana wa jama’arsa cewa abin da ya faru a jihar Rivers ya saɓa doka, amma ya kasa samun zuciyar yin hakan."
"Ta ya ya zan zama gwamna, sai kuma shugaban ƙasa wanda shi ma zaɓarsa aka yi, ya umarce ni na bar kujera ta."
"Tabbas, zan bar kujerar don ka da a samu hargitsi, amma zan garzaya kotu. Kuma zan shaida wa jama’ata cewa ku ne kuka zaɓe ni, amma shugaban kasa ya na son in bar kujerata."
- Laolu Akande
Gwamnonin da suka goyi bayan Tinubu kan Fubara
A baya rahoto ya zo cewa akwai gwamnonin da suka goyi bayan shugaban ƙasa Bola Tinubu, kan dakatarwar da ya yi wa Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers.
Gwamnonin waɗanda suka goyi bayan matakin, sun nuna cewa abin da shugaban ƙasan ya yi, ya zama tilas domin dawo da zaman lafiya a jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng