Yadda Musulmi zai Yi Bikin Sallah da Idi cikin Nishadi a Tsarin Musulunci

Yadda Musulmi zai Yi Bikin Sallah da Idi cikin Nishadi a Tsarin Musulunci

Addinin Musulunci ya tanadi hukunce hukunce da suka shafi yadda ake gudanar da sallar idi da bikin sallah da ake bukatar kowane Musulmi ya yi koyi da su.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Al'ummar Musulmi a fadin duniya sun fara shirye shirye domin gunadar da sallar idi da bikin sallah.

Hakan na zuwa ne yayin da aka fara sanar da duba watan Shawwal wanda a karshen shi za a yi bikin sallar azumi.

Sallar Idi
Abubuwan da ya kamata a kiyaye a lokacin bbikin sallah. Hoto: Abdul Gany Bashir|Anadolu
Asali: Getty Images

A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu hukunce hukunce da suka shafi bukukuwan sallah da yadda za a gudanar da sallar idi bisa yadda Musulunci ya tsara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Yin wanka kafin fita sallar Idi

Daya daga cikin sunnonin Idi shi ne yin wanka kafin fita zuwa sallah. An samu ruwaya daga Abdullahi bin Umar cewa yana yin wanka a ranar Idi kafin fita zuwa masallacin Idi.

Kara karanta wannan

Da gaske Atiku ya karbi miliyoyin Naira daga Gwamnan Legas a lokacin zaben 2023?

Wannan ya na nuna cewa yin wanka kafin Idi yana daga cikin sunnoni masu karfi kamar yadda yake a Jumu’a da sauran tarukan jama’a.

Sheikh Salih Al-Munajjid ya wallafa a shafinsa na amsa tambayoyi cewa dalilin yin wankan shi ne tsaftace jiki da kuma nuna darajar wannan rana.

Sallah
Musulmai na jira a fara salar Idi a Najeriya. Hoto: Anadolu
Asali: Getty Images

2. Cin abinci kafin fita sallah

A ranar Idin azumi, ana so Musulmai su ci abinci kafin su fita zuwa sallah. Manzon Allah (SAW) ya kasance yana cin dabino kafin fita Idi, yana cin guda uku ko biyar ko fiye.

Hakan yana nuni da cewa an gama azumin watan Ramadan da kuma toshe kofar yin karin azumi a ranar sallah.

Amma a Idin sallar layyya, ana so mutum ya jira har sai ya koma gida daga masallaci sannan ya ci abinci.

Sallah
Gwamnan Kano da Rabi'u Kwankwaso a filin Idi. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Twitter

3. Yin kabbarori ranar Idi

Malamai sun bayyana cewa yin kabbarori a ranakun Idi yana daga cikin manyan sunnoni da ake bukata Musulmi ya aikata.

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta: Dalung ya yi gargadi kan 'shirin' saka dokar ta baci a Kano

A tarihi, Sahabbai suna yin kabbarori daga lokacin da suka fito daga gidajensu har zuwa lokacin da Liman ya fito domin gudanar da sallah.

Wannan yana daga cikin al’adun Musulunci masu daraja a ranakun Idi, saboda haka malamai suke jan hankali domin kar a manta da su.

Makka
Musulmai na sallar Idi a Makka. Hoto: Abdul Gany Bashir
Asali: Getty Images

4. Gaisawa da juna lokacin Idi

Daga cikin kyawawan dabi’u a ranar Idi akwai gaisawa da juna da yin addu’ar fatan Allah ya karbi ibadar da aka yi a Ramadan.

Addini ya koyar da cewa yin haka yana kara dankon zumunci da hadin kai a tsakanin al’ummar Musulmi.

5. Yin ado da sanya tufafi masu kyau

Yana daga cikin sunnoni a Idi a sanya tufafi masu kyau. An rawaito cewa Manzon Allah (SAW) yana da wata rigar ado da yake sanya wa a ranakun Idi da kuma ranakun Jumu’a.

Maza suna da damar sanya tufafi masu kyau, amma mata ba su da damar yin ado mai nuna kyawun surarsu a waje. Ya kamata su fita cikin ladabi ba tare da jan hankalin maza ba.

Kara karanta wannan

Rundunar ƴan sanda ta yi magana kan shirin hawan sarakuna 2 a Kano

Sallah
Tsohon shugaban kasa, Buhari a filin Idi. Hoto: Bashir Ahmed
Asali: Facebook

6. Sauya hanya a yayin dawowa daga idi

Daga cikin abubuwan da Manzon Allah (SAW) yake yi a ranar Idi akwai sauya hanya yayin dawowa daga sallar Idi. An ce yana yin haka ne:

  • Domin kasa ta yi shaida kan ibadarsa.
  • Domin ya yada alheri a hanyoyi daban-daban.
  • Domin yawaita kabbarori a wurare da dama.

Yin wadannan sunnoni yana kara albarkar wannan rana da kuma kara kusancin bawa ga Allah Madaukakin Sarki.

Tattaunawar Legit da limami

Wani limami a jihar Gombe, Musa Yahaya ya ja hankalin al'ummar Musulmi a kan bikin Sallah yayin da ya tattauna da Legit.

Malam Musa Yahaya ya bayyana cewa ya kamata iyaye su kula da yadda yaransu za su fita da wuraren da za su je yawon sallah.

"Ya na da matukar muhimmanci kowane uba ko uwa su tabbatar da cewa 'ya'yansu sun yi shiga ta kamala. Kuma su tabbatar da ba su je wuraren banza ba.

Kara karanta wannan

'Dan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu ya gamu da fushin matasa, an dakawa motar tallafinsa wawa

"Bai kamata a yi sakaci tarbiyar yara ta lalace a sanadiyyar bikin sallah ba. Masu yara kanana ma ya kamata su saka ido domin kaucewa batar yara."
Musulmai
Musulmai a sahun sallar Idi a Najeriya. Hoto: Audu Marte
Asali: Getty Images

Za a fara duba wata a Saudiyya

A wani rahoton, kun ji cewa kasar Saudiyya ta fitar da sanarwa kan fara duba watan Shawwal domin kawo karshen azumin Ramadan.

Legit ta rahoto cewa Saudiyya ta bayyana cewa za a fara duba watan ne a ranar Asabar, 29 ga watan Ramadan a dukkan sassa na kasar

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng