Bayan Aminu Ado Ya Haƙura, Gwamnatin Kano Ta Canza Tsarin Ranar Jajibirin Sallah

Bayan Aminu Ado Ya Haƙura, Gwamnatin Kano Ta Canza Tsarin Ranar Jajibirin Sallah

  • Bayan komai ya lafa game da batun hawan sallah, gwamnatin Kano ta sauya wasu tsare-tsarenta na ranar Asabar mai zuwa
  • Kwamishinan mahalli da sauyin yanayi ya ce an janye dokar taƙaita zirga-zirga ranar Asabar ta karshen wata saboda jajibirin sallah
  • Ɗahir H. Hashim ya ce gwamnati ta yi haka ne domin bai wa jama'a damar ci gaba da shirye-shiryen sallah cikin kwanciyar hankali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Gwamnatin Jihar Kano ta sassauta dokar hana zirga-zirga a ranar Asabar, 29 ga watan Maris, 2025.

A tsarin gwamnatin Kano, ana taƙaita zirga-zirgar ababen hawa a kowace Asabar ta karshen wata domin kwashe shara da sauran ayyukan tsaftace mahalli.

Gwamna Abba da Sanusi.
Gwamnatin Kano ta sauƙaƙa dokar hana zirga-zirga ranar Asabar mai zuwa Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Amma a wata sanarwa da kwamishinan mahalli da sauyin yanayi na Kano, Dr. Ɗahir H. Hashim ya wallafa a shafinsa na X, ya ce an ɗage dokar ranar Asabar mai zuwa.

Kara karanta wannan

Rigima ta kaure a sakatariyar APC, matasa su kusa lakaɗawa ciyaman duka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Kano ta ɗage dokar shara ranar Asabar

Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin Kano ta ɗauki wannan matakin ne saboda ranar za ta zama jajibirin sallah, don haka ta bar mutane su ci gaba da shirye-shiryen ƙaramar sallah.

Duk da sassauta dokar, gwamnatin jihar ta bukaci al’ummar Kano da su ci gaba da tsaftace muhalli domin gudanar da bukukuwan Sallah cikin tsafta da kwanciyar hankali.

An bukaci mutanen Kano su tsaftace mahallinsu

Kwamishinan ya ce:

"Mu na kira ga jama’a da su tsaftace gidajensu da unguwanni, domin mu yi bukukuwan Sallah a cikin yanayi mai kyau.
"Amma za a yi aikin tsaftace duka kasuwanni da ma’aikatu kamar yadda aka saba a gobe Jumu’a."

Ya ƙara da cewa shara da datti su ne manyan matsalolin muhalli da ke haifar da cututtuka, don haka yana da muhimmanci kowa ya bayar da gudunmawa wajen tsaftace muhalli.

Gwmanati ba ta canza aikin Juma'a ba

Kara karanta wannan

Rundunar ƴan sanda ta yi magana kan shirin hawan sarakuna 2 a Kano

A cewar Dr. Dahir M. Hashim, aikin tsaftace muhalli da ake yi a ranakun Jumu’a a kasuwanni da ma’aikatu ba zai canza ba.

Ya bukaci shugabannin kasuwanni da masu ma’aikatu da su tabbatar da bin wannan tsari kamar yadda aka saba.

Gwamna Abba.
Gwamnatin Kano ta bar mutane su ci yi harkokinsu ranar Asabar Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook
"Kwashe shara na ranakun Jumu’a ya na da matukar muhimmanci, domin ya na taimakawa wajen rage yawan cututtuka da ke da nasaba da rashin tsafta.
"Don haka, muna kira ga kowa da kowa da ya bada hadin kai wajen tabbatar da tsaftar muhalli."

Gwamnatin Kano ta kuma yi addu’a da fatan alheri ga al’umma, ta na mai roƙon Allah ya karɓi ibadun da aka gudanar a watan Ramadan kuma ya sa a gudanar da bukukuwan Sallah cikin lumana da kwanciyar hankali.

"Allah Ubangiji ya karɓi ibadarmu, ya kuma zaunar da Jihar Kano lafiya," in ji Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi.

Sanusi II ya gana da Gwamna Abba

Kara karanta wannan

KADIRS: "Yadda El Rufa'i ya yi rugu rugu da hukumar haraji a zamaninsa"

A wani rahoton, kun ji cewa Muhammadu Sanusi II ya ziyarci gidan gwamnatin Kano sa'o'i ƙalilan bayan Aminu Ado Bayero ya janye hawan sallah.

Ana kallon wannan ziyara a matsayin wata alama ta ci gaba da karfafa dangantaka tsakanin masarautar Kano da gwamnatin jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel