Dama Ta Samu: Gwamnatin Uba Sani Za Ta Dauki Ma'aikata, Ta Fadi Wadanda Za Su Amfana

Dama Ta Samu: Gwamnatin Uba Sani Za Ta Dauki Ma'aikata, Ta Fadi Wadanda Za Su Amfana

  • Gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani za ta ɗauki sababbin ma'aikata a ɓangaren lafiya
  • Uba Sani ya amince a ɗauki ma'aikatan kiwon lafiya 1,800 a faɗin jihar domin inganta samar da lafiya a matakin farko
  • Kwamishinar lafiya ta jihar wadda ta tabbatar da hakan ta kuma bayyana cewa za a ƙara ɗaga darajar dakunan shan magani

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da daukar ma’aikatan lafiya guda 1,800.

Gwamna Uba Sani ya amince da ɗaukar ma'aikatan ne don cike giɓin ma’aikata a dukkanin cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko (PHC) a faɗin jihar.

Gwamna Uba Sani zai dauki ma'aikata
Uba Sani zai dauki ma'aikatan lafiya Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishiniyar lafiya ta jihar Kaduna, Hajiya Umma Ahmad, ta fitar a ranar Alhamis, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Shugabannin SDP sun ziyarci mai martaba sarki, ya tsage masu gaskiya kan yaudarar jama'a

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Uba Sani zai ɗauki ma'aikata?

Hajiya Umma Ahmad ta bayyana cewa ɗaukar ma’aikatan zai ƙara ƙarfafa matsayin ja gaba da jihar ke da shi a ɓangaren kiwon lafiya matakin farko a ƙasar nan, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

"Ɗaukar ma’aikatan zai magance matsalar ƙarancin ma’aikata a cibiyoyin kiwon lafiya, wanda hakan zai rage yawan mace-macen mata masu juna biyu da yara, tare da inganta lafiyar al’ummar jihar Kaduna."

- Hajiya Umma Ahmad

Sanarwar ta kuma bayyana cewa ana ci gaba da gyara cibiyoyin PHC guda 255, samar da kayan aikin zamani, da kuma rarraba magunguna masu muhimmanci a faɗin jihar.

"Dukkan cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko guda 255 da ke jihar Kaduna za a sake fasalinsu tare da ɗaukaka darajarsu zuwa mataki na biyu, a matsayin wani ɓangare na gyaran da gwamnatin Gwamna Uba Sani ke yi a ɓangaren kiwon lafiya.”
"Sababbin cibiyoyin PHC da aka inganta za su riƙa kula da cututtuka kamar ciwon suga mara tsanani, hawan jini da bai yi tsanani ba, farfaɗo da marasa lafiya masu fama da asma, da taimakawa wajen haihuwa, tare da sauran muhimman ayyuka."

Kara karanta wannan

Shirin kawar da gwamnatin APC: Sababbin jam'iyyu na tururuwar yin rajista da INEC

- Hajiya Umma Ahmad

Kwamishinar ta ƙara da cewa tun daga hawansa mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, gwamnatin Gwamna Uba Sani ta na bai wa ɓangaren kiwon lafiya muhimmiyar kulawa.

Gwamnan Kaduna, Uba Sani
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani Hoto: @ubasanius
Asali: UGC

Haka kuma, kwamishiniar ta jaddada cewa a ƙarƙashin gwamnatin Uba Sani kowane mutum yana da haƙƙin samun kiwon lafiya mai inganci.

Gwamnatin Kaduna ta samu kyaututtuka

Ta yi nuni da matsayin da jihar Kaduna ta samu matsayin jihar da ta fi yin ƙoƙari a fannin kiwon lafiya matakin farko a yankin Arewa maso Yamma, inda har aka ba ta kyaututtuka.

"An yaba da ƙoƙarin mai girma gwamna ta hanyar samun karramawa guda 10, a ciki da wajen Najeriya, ciki har da lambar yabo daga ƙungiyar International Supply Chain Education Alliance (ISCEA)."

- Hajiya Umma Ahmad

Abin a yaba ne

Wata ƴar jihar Kaduna, Zainab Nasir ta nuna jin daɗinta kan wannan matakin da Gwamna Uba Sani ya ɗauka ƙara yawan ma'aikata lafiya.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Natasha ta karbi N500m a hannun Akpabio? An ji gaskiyar zance

"Wannan abin yabawa ne domin asibitocin suna buƙatar ƙarin ma'aikata domin kula da lafiyar marasa lafiya yadda ya kamata."

"Muna fatan idan an ɗauke su a riƙa biyansu albashi a kan kari domin na yanzu suna kokawa kan cewa ba su samun kuɗaɗensu a kan lokaci."

- Zainab Nasir

Tinubu ya umarci a ɗauki matasa aiki

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa ya ba da umarnin a ɗauki matasan da ake horarwa kan sa ido a cibiyoyin kiwon lafiya aiki.

Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya umarci a maida matasan a matsayin ma'aikata bayan sun kammala aikinsu na shekara ɗaya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng