Ana cikin Fargaba a Kano kan Bukukuwan Sallah, Ƴan Sanda Sun Gano Makarkashiya
- Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da tsauraran matakan tsaro kafin, lokacin, da bayan bukukuwan sallah duk da rigimar sarauta
- Tun farko, an samu damuwa da bangarori masu hamayya suka shirya gudanar da hawa daban-daban, wanda ya haifar da tsoron yiwuwar rikici
- Duk da tabbacin da aka bayar, wasu mazauna sun nuna damuwa kan yiwuwar tashin hankali, akwai masu nuna kwarin gwiwa ga jami'an tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano- Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta shirya tsaf domin ba da tsaro yayin bukukuwan sallah.
Rundunar ta tabbatar da daukar tsauraran matakan tsaro kafin, lokacin, da bayan bukukuwan sallah, domin hana duk wani tashin hankali.

Asali: UGC
'Yan sanda sun kwantarwa al'ummar Kano hankali
Leadership ta ce wannan tabbaci ya zo ne a lokacin da ake fuskantar tashin hankali a jihar, sakamakon rikicin sarauta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi hasashen rigima tsakanin magoya bayan tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, da kuma Sarki mai ci, Muhammadu Sanusi II.
Duk da kokarin hukumomi na kwantar da hankula, wasu mazauna sun nuna damuwa kan yiwuwar rikici yayin bukukuwan Sallah.
Wasu sun bayyana kwarin gwiwa ga jami'an tsaro, yayin da wasu ke nuna shakku kan yiwuwar samun zaman lafiya.
A wani shiri na rage wannan tashin hankali, rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kara kaimi wajen shirye-shiryen tsaro na bukukuwan sallah, cewar Tribune.
A lokacin taro tare da kungiyoyin farar hula, Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa hukumomin tsaro sun gano wasu kungiyoyi da ke shirya bukukuwa daban-daban.
Ya ce:
"Muna sake tsara dabaru da yin tuntuba mai yawa don tabbatar da cewa an kiyaye doka da oda."
Ya nanata cewa hukumomin tsaro suna cikin shirin ko-ta-kwana kuma ba za su yarda da duk wani abu da zai tayar da hankula ba.

Asali: Twitter
Bukukuwan sallah: Martanin wasu 'yan Kano
Yayin da bukukuwan Sallah ke karatowa, da dama daga cikin mazauna Kano suna fatan bukukuwan za su gudana cikin lumana.
Wani ma'aikacin gwamnati, Malam Abubakar Sani, ya nuna kwarin gwiwa ga 'yan sanda, yana mai cewa Kano koyaushe tana zaman lafiya yayin bukukuwan sallah.
Ya ce:
"Ina da imani cewa 'yan sanda za su yi aikinsu, amma mazauna su ma dole su bi umarnin hukumomi da kuma kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba."
Amma ga Malam Musa Adamu, wani dan kasuwa a birnin Kano, ya ce har yanzu yana cikin fargaba.
"Ina farin cikin cewa 'yan sanda suna daukar mataki, amma gaskiya har yanzu ina jin tsoro, saboda mun ga yadda rikicin siyasa zai iya rikidewa zuwa tashin hankali, musamman a lokutan bukukuwan hawan sallah."
- Cewar dan kasuwar
A daya bangaren, wata mazauniyar Kano, Hajiya Amina ta ce ta na da yakinin cewa hukumomin tsaro za su yi aikinsu, amma za ta guji tarukan jama'a.
A cewarta:
"Ina da tabbacin cewa 'yan sanda za su yi kokarinsu don hana duk wani tashin hankal, amma zan yi bukukuwa a gida tare da iyalina, domin hakan yafi aminci."
Aminu Ado ya janye hawan sallah
A baya, an ruwaito cewa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya soke shirinsa na gudanar da hawan sallah bisa la'akari da matsalar tsaro.
Wannan mataki ya biyo bayan makonni na tashin hankali da suka shafi shirye-shiryen hawan sallah tsakanin Aminu Ado Bayero da Sarki Muhammadu Sanusi II.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng