Kiranye: Natasha Ta Nuna Yatsa ga INEC bayan Sanar da Ita Shirin Koro Ta daga Majalisa

Kiranye: Natasha Ta Nuna Yatsa ga INEC bayan Sanar da Ita Shirin Koro Ta daga Majalisa

  • Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta nuna rashin jin daɗinta kan abin da hukumar INEC ta yi dangane da shirin yi mata kiranye
  • Ta zargi hukumar zaɓen ta nuna son kai ta hanyar goyon bayan masu shigar da ƙorafin yi mata kiranye daga majalisar dattawa
  • Sanata Natasha ta bayyana cewa kamata ya yi INEC ta yi watsi da ƙorafin saboda rashin ingancinsa da saɓa dokar da ya yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kogi - Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta caccaki hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) kan shirin yi mata kiranye.

Sanata Natasha Akpoti ta soki hukumar INEC bisa gazawarta wajen yin watsi da ƙorafin neman a yi mata kiranye daga majalisar dattawa.

Natasha ta caccaki hukumar INEC
Sanata Natasha ta nuna yatsa ga hukumar INEC Hoto: Natasha H Akpoti
Asali: Original

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, 26 ga watan Maris 2025, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Shirin kawar da gwamnatin APC: Sababbin jam'iyyu na tururuwar yin rajista da INEC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

INEC, a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, ta tabbatar da karɓar ƙorafin da ke ɗauke da sa hannun sama da rabin masu zaɓe 474,554 da suka yi rajista a mazaɓar sanatar, a matsayin wani ɓangare na shirin yi mata kiranye.

Sai dai, INEC ta bayyana cewa ƙorafin bai cika sharuɗɗan da ake buƙata ba, saboda babu cikakkun bayanai kamar adireshi, lambobin waya, da adireshin imel na masu shigar da ƙorafin, kamar yadda dokokin INEC na 2024 suka tanada.

Natasha ta zargi hukumar INEC da son-kai

Amma a martaninta, Sanata Natasha, ta hannun lauyanta, Victor Giwa, ta zargi INEC da ɗaukar ɓangare, inda ta ce ya kamata hukumar ta yi watsi da ƙorafin gaba ɗaya maimakon ba wa masu shigar da shi damar gyara kura-kurensu.

“Matsayar da kuka bayyana a cikin sanarwar da kuka fitar a ranar 25 ga Maris, 2025, wacce Sam Olumekun ya sanyawa hannu, ta nuna cewa hukumar ta nuna fifiko ga masu shigar da ƙorafi a wannan lamari."

Kara karanta wannan

INEC ta aika sako ga Sanata Natasha kan shirin koro ta daga majalisar dattawa

"Hukumar ta lura cewa ƙorafin bai cika ƙa’idojin da ake buƙata don kiranye ga ɗan majalisa ba, kasancewar bai ƙunshi cikakkun bayanan adireshi, lambobin waya, da adireshin imel a cikin wasiƙar shigar da ƙorafin ba."
"Matakin da ya dace INEC ta ɗauka shi ne ta bayyana ƙorafin a matsayin maras inganci sannan ta yi watsi da shi gaba ɗaya."

- Victor Giwa

Sanata Natasha ta gano kuskuren INEC

Sanata Natasha ta ce hanya mafi dacewa da INEC za ta nuna rashin nuna bangaranci ita ce ta bayyana ƙorafin a matsayin maras inganci, wanda hakan zai kawo ƙarshen shirin kiranyen gaba ɗaya.

Natasha ta caccaki hukumar INEC
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmud Yakubu Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter
“A bisa doka, ya kamata INEC ta bayyana ƙorafin a matsayin mara inganci saboda matsalolin da ke tattare da shi, amma abin mamaki, maimakon ta yi watsi da ƙorafin saboda gazawarsa wajen cika sharuɗɗa, sai ta koma mai ba da shawara ga masu shigar da ƙorafin."
"Ta gaya musu cewa idan suka cike bayanan da ba su bayar ba, za ta fara tantance sahihancin sa hannun da aka tattara daga kowace rumfar zaɓe."

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Natasha ta karbi N500m a hannun Akpabio? An ji gaskiyar zance

“Muna da ra’ayin cewa INEC ta bayyana kanta a matsayin mai goyon bayan masu shigar ƙorafi, kuma ta lalata sahihancin tsarin."
"Idan har hukumar za ta kare mutuncinta da nuna rashin son rai, kamata ya yi ta bayyana ƙorafin a matsayin mara inganci kuma ta sanar da masu shigar da shi, don kawo ƙarshen shirin gaba ɗaya."

- Victor Giwa

INEC ta aika saƙo ga Natasha

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), ta aika saƙo ga Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha H Akpoti.

Hukumar INEC ta sanar da Sanata Natasha shirin wasu mutanen mazaɓarta na.yi mata kiranye daga majalisar dattawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel