Ana Maganar Hawan Sallah, Abba Ya Gana da Sanusi II, Manyan 'Yan Fadar Kano

Ana Maganar Hawan Sallah, Abba Ya Gana da Sanusi II, Manyan 'Yan Fadar Kano

  • Bayan janyewar Aminu Ado Bayero daga hawan Sallah, an hango Muhammadu Sanusi II ya kai ziyara gidan gwamnatin Kano
  • A bisa hotunan da aka wallafa, gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi Sarkin Kano na 16 tare da wasu manyan masu masarauta a jihar
  • Biyo bayan lamarin, jama’a sun bayyana ra’ayoyinsu kan wannan ziyara, wasu na taya murna sai kuma fadin wasu abubuwa dabam

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Bayan da Aminu Ado Bayero ya janye hawan Sallah domin zaman lafiya a Kano, Muhammadu Sanusi II ya kai ziyara zuwa gidan Gwamnatin Jihar Kano.

Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya kai ziyara gidan gwamnatin Kano ne tare da wasu manyan masu fada a ji a fadar Kano.

Kara karanta wannan

'Aminu Ado ka hakura da mulkin Kano,' Kiran jama'a bayan janye hawan sallah

Sanusi II ya gana da Abba Kabir
Sanusi II ya gana da Abba Kabir a fadar gwamnati. Hoto: Sanusi II Dynasty
Asali: Facebook

Sarkin Kano na 16 ya wallafa hoton wannan ziyara a shafinsa na X, inda aka nuna shi tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana kallon wannan ziyara a matsayin wata alama ta ci gaba da karfafa dangantaka tsakanin masarautar Kano da gwamnatin jihar.

Sanusi II ya samu tarba a gidan gwamnati

A cewar sanarwar da shafin mai martaba Muhammadu Sanusi II ya fitar, gwamna Abba Kabir Yusuf ya tarbe shi tare da wasu manyan mutane daga masarautar Kano.

Wadanda aka yi wannan ganawa da su, su ne:

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf
  • Muhammadu Sanusi II (Sarkin Kano na 16)
  • Munir Sanusi (Wamban Kano)
  • Mujtaba Abubakar Abba (Sarkin Yakin Kano)

Ziyarar ta zo ne a dai-dai lokacin da ake ci gaba da samun rashin jituwa a Kano bayan rikicin sarauta da ya biyo bayan mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin sarki.

Kara karanta wannan

"Ba abin a mutu ko a yi rai ba ne," Aminu Ado ya canza shawarar hawan sallah a Kano

Martanin jama'a kan haduwar Abba da Sanusi II

Bayan wallafa labarin ziyarar da aka yi, jama’a da dama sun tofa albarkacin bakinsu kan wannan lamari.

Atisaba Suleiman ya yi addu’a, yana mai cewa:

"Amin, amin, amin! Allah ya kara albarka da rahama ga Mai Martaba, Allah ya albarkaci gwamna."

A daya bangaren, Abdullahi Ibrahim Wase ya bayyana cewa:

"Aminu Ado ya daga musu hankali."

Naseerou Adamu Mlmw ya yi addu’a da cewa:

"Allah ya musu albarka damu baki daya."

Jibril Muhammad Dahiru ya yi fatan alheri yana cewa:

"Allah ya kara lafiya da nisan kwana, Maulana Khalifa Muhammad Sanusi II."
Sarkin Kano
Muhammadu Sanusi II a fadar Sarkin Kano. Hoto: Masarautar Kano
Asali: Facebook

Tasirin ziyarar kan sarautar Kano

Ana ganin wannan ziyara ta kara jaddada cewa gwamnatin Kano da masarautar jihar karkashin Muhammadu Sanusi Ii suna aiki tare.

Duk da cewa ba a bayyana abubuwan da suka tattauna ba, ana ganin ziyarar ba za ta rasa nasaba da yadda za a gudanar da hawan sallah a Kano ba.

Kara karanta wannan

An shiga jimami a Kano: Babban mai taimaka wa Gwamna Abba ya rasu ana azumi

Yanzu haka dai kallo ya koma jihar Kano domin ganin yadda za a gudanar da hawan sallah, musamman bayan janyewar Aminu Ado Bayero.

Mutanen Bichi sun ziyarci Sanusi II

A wani rahoton, kun ji cewa tawaga mai karfi daga masarautar Bichi a jihar Kano ta ziyarci Mai martaba Muhammadu Sanusi II.

Legit ta rahoto cewa a cikin tawagar akwai shugaban karamar hukumar Bichi, hakimin yankin, dagatai, limamai da sauran 'yan fada.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel