Abin da Shehu Sani Ya ce bayan Aminu Ado Ya Janye Hawan sallah, Ya Shawarci Sanusi II

Abin da Shehu Sani Ya ce bayan Aminu Ado Ya Janye Hawan sallah, Ya Shawarci Sanusi II

  • Shehu Sani ya jinjinawa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, bisa janye hawan Sallah, ya ce wannan mataki zai kawo zaman lafiya
  • A yau Alhamis, 27 ga watan Maris, 2025, Sanata Shehu Sani ya bayyana ra'ayinsa a shafinsa na X, bayan fitar da sanarwar janye hawan
  • Sani wanda ya yi Sanata tsakanin 2019 da 2023 ya bukaci sarakan biyu su yi amfani da wata mai albarka don sulhu da hadin kai
  • Ya kara da addu’ar Allah ya ba masarautar ikon fahimtar juna da kwanciyar hankali, ya ce hakan zai taimaka wajen ci gaban Kano

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Sanata Shehu Sani ya yi martani bayan Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya janye hawan sallah.

Shehu Sani ya yabawa basaraken kan matakin da ya dauka inda ya ce hakan zai kawo zaman lafiya a Kano.

Kara karanta wannan

'Aminu Ado ka hakura da mulkin Kano,' Kiran jama'a bayan janye hawan sallah

Shehu Sani ya yi magana kan rigingimu game da yawan sallah a Kano
Shehu Sani ya shawarci Sanusi II da Aminu Ado Bayero su sasanta tsakaninsu. Hoto: Sanusi II Dynasty, Shehu Sani.
Asali: Facebook

Hawan sallah: Aminu Ado ya sauya shawara

Shehu Sani ya bayyana haka a yau Alhamis 27 ga watan Maris, 2025 a shafinsa na X awanni bayan fitar da sanarwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin Shehu Sani na zuwa ne bayan basaraken ya nuna dattaku inda ya sanar da janye shirinsa na hawan sallah a Kano.

Hakan ya zo ne yayin da mazauna Kano ke cikin fargabar abin da zai faru a bukukuwan hawan sallah kafin Aminu Ado Bayero ya fitar da matsaya.

Basaraken ya bayyana cewa hukuncin ya biyo bayan shawarwari daga malamai, iyaye, shugabanni, da masu ruwa da tsaki a masarauta.

Ya bukaci jama’a da su yi hakuri da wannan mataki tare da amfani da bukukuwan sallah wajen sada zumunci da ƴan uwa a Kano.

Matakin da Aminu Ado ya ɗauka kan hawan sallah a Kano
Shehu Sani ya shawarci Sanusi II da Aminu Ado Bayero kan sulhu game da rigimarsu. Hoto: Sanusi Bature Dawakin-Tofa, Masarautar Kano.
Asali: Twitter

Shehu Sani ya roki Sanusi II, Aminu Ado

Sanata Shehu Sani ya ce wannan wata dama ce da Allah ya kawo domin a zauna a kuma sasanta saboda samun zaman lafiya a jihar.

Kara karanta wannan

"Sun haƙura?" An saki bidiyon Sanusi II bayan Aminu Ado ya janye hawan sallah a Kano

Ya roki dukan bangarorin guda biyu da su yi amfani da wannan wata mai albarka domin hada kai da kawo zaman lafiya.

Shehu Sani ya ce:

"Matakin Mai Martaba Aminu Ado Bayero ya soke shahararren hawan sallah a Kano abin a yaba ne.
"Wannan mataki na nuna alamun fata ga zaman lafiya a Kano.
"Ina addu’a cewa 'yan takarar sarauta guda biyu za su yi amfani da albarkar wannan wata mai alfarma domin sulhunta da hada kan iyalinsu na sarauta."

Sanatan ya ce wannan wata dama ce da Allah ya kawo don masarauta ta samu kwanciyar hankali.

Ya yi addu'ar Allah ya ba su ikon fahimtar juna da hadin kai domin ci gaban jihar Kano.

Martanin Sanusi II bayan matakin Aminu Ado

A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi martani bayan Alhaji Aminu Ado Bayero ya sanar da janye shirin hawan sallah saboda masalahar zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Sheikh Lawan Triumph ya sa baki kan rikicin hawan sallah a Kano, ya aika sako ga Aminu Ado

An gano Sanusi II a wani bidiyo yana tambayar shin 'sun haƙura?' cikin zolaya da barkwanci saboda tabbatar da gaskiyar lamarin.

Hakan na zuwa ne bayan Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya sanar da jami'an tsaro shirinsa domin fita hawan sallah a wannan shekara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng