Bayan Dakatar da Fubara, Dalibai Sun 'Kunyata' Matar Tinubu a Yankin Neja Delta
- Wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna yadda daliban makarantar a Delta suka ƙi amincewa da Remi Tinubu a matsayin “uwarsu.”
- Matar shugaban Najeriyar ta kai ziyara zuwa jihar Delta domin gabatar da shirin tallafi na Renewed Hope Initiative (RHI) da take jagoranta
- Wani ɓangare na taron ya haɗa da rabon kayan aiki ga matan gwamnoni na yankin Kudu maso Kudu, waɗanda ke kula da shirin RHI a jihohinsu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja Wani faifan bidiyo ya bayyana yadda daliban makarantar koyon aikin jinya ta jihar Delta suka yi watsi da kirarin da aka yi wa Oluremi Tinubu a matsayin “uwarsu.”
Matar Shugaban Ƙasa ta kai ziyara jihar Delta ne domin gudanar da shirin Renewed Hope Initiative, wanda ke da nufin inganta rayuwar ‘yan Najeriya.

Asali: UGC
Bayan faruwar lamarin, Legit ta gano bidiyon ne a cikin wani sakon da @ChuksEricE ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Punch ta wallafa cewa gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta ya yaba da ƙoƙarin Oluremi Tinubu, yana mai cewa shirin nata na kawo sauyi a fannin kiwon lafiya.
Abin da ya faru da matar Tinubu a Delta
A yayin taron, an gudanar da rabon kayan aiki ga matan gwamnoni na yankin Kudu maso Kudu, waɗanda ke kula da shirin RHI a jihohinsu.
Oluremi Tinubu ta kuma kai ziyara zauren sarakunan gargajiya, inda ta gana da manyan sarakuna, ciki har da Orodje na Okpe, Manjo Janar Felix Mujak Peruo (mai ritaya).
Duk da haka, abin da ya fi jawo ce-ce-ku-ce shi ne yadda daliban koyon aikin jinya suka mayar da martani lokacin da mai gabatar da taro ya gabatar da Oluremi Tinubu a matsayin “uwarsu.”
A cikin bidiyon, an ji mai gabatar da taron yana cewa, “Uwarmu ce” amma daliban suka amsa da cewa, “Mamarka ce!” hakan ya nuna ƙin amincewarsu da wannan kiran.
Menene dalilin martanin dalibai ga Remi Tinubu?
Ba a bayyana takamammen dalilin da yasa daliban suka ƙi amincewa da Oluremi Tinubu a matsayin “uwarsu” ba, amma ana ganin yana da nasaba da halin da ƙasar ke ciki.
Tun bayan hawa mulkin Bola Tinubu a watan Mayu 2023, ‘yan Najeriya da dama sun koka kan matsalar tsadar rayuwa, ƙarancin abinci, da kuma rashin tsaro.
Wasu suna ganin martanin daliban na iya zama wata alama ta rashin gamsuwa da yadda gwamnatin Tinubu ke tafiyar da harkokin ƙasa.

Asali: Facebook
Hakazalika, ana danganta wannan martani da gagarumin fushi da ake nunawa a kan manufofin gwamnati da suka jefa talakawa cikin wahala.
Fadar shugaban kasa ba ta ce komai ba
Bayan bayyanar bidiyon, mutane da dama sun yi martani a kafafen sada zumunta, wasu na goyon bayan daliban, yayin da wasu ke sukar su.
Wasu na ganin cewa abin da daliban suka yi ba daidai bane, domin matsayin Oluremi Tinubu a matsayin matar Shugaban Ƙasa yana buƙatar girmamawa.
Sai dai wasu sun nuna cewa martanin daliban yana nuni da yadda yawancin ‘yan Najeriya ke jin takaici da halin da ƙasa ke ciki.
A halin yanzu, ba a samu wata sanarwa daga fadar Shugaban Ƙasa ko kuma daga Oluremi Tinubu kan wannan batu ba.
Remi Tinubu ta gaisa da dalibai a Kwara
A wani rahoton, kun ji cewa matar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu ta sauka a mota ta gaisa da dalibai.
Legit ta rahoto cewa lamarin ya faru ne yayin da Remi Tinubu ta kai ziyarar bude ayyuka a jihar Kwara, kuma an yaba mata kan abin da ta yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng