Tinubu: Zargin Magudin Zaben 2027 ta Nadin Sabon Shugaban INEC
- Ana rade radin cewa ana shirin naɗa sabon shugaban INEC da zai yi biyayya ga gwamnati domin tunkarar zaɓen 2027
- Wa'adin Farfesa Mahmood Yakubu a shugaban INEC zai ƙare a watan Nuwamba 2025 bayan kammala wa'adinsa na biyu
- An ce wasu jiga-jigan 'yan siyasa daga cikin da wajen Aso Rock ne ke jagorantar shirin sauya shugabancin hukumar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ana ci gaba da hasashen wanda zai gaji Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin shugaban Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC), kasancewar wa'adinsa zai ƙare a watan Nuwamba 2025.
Wata majiya ta bayyana cewa wasu manyan jiga-jigan siyasa da ke da alaƙa da Aso Rock ne ke ƙoƙarin tabbatar da cewa wanda za a naɗa zai kasance mai biyayya ga gwamnati.

Asali: Facebook
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa har yanzu Shugaba Bola Tinubu bai yanke shawarar wanda zai maye gurbin Tanimu Yakubu ba, amma akwai shirin naɗa mutum da gwamnati za ta iya sarrafa shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shirin nada sabon shugaban hukumar INEC
Rahotanni sun nuna cewa wasu manyan ‘yan siyasa, ciki har da wani tsohon gwamna daga yankin Kudu maso Kudu, na jagorantar shirin naɗa sabon shugaban INEC.
An gano cewa ana duba wasu kwamishinonin INEC da shugabannin zaɓe da aka taɓa naɗawa a baya, duk da cewa ba su da cikakken tarihin gudanar da sahihin zaɓe.
Ana zargin cewa wasu daga cikin jami'ai masu nagarta a hukumar zaɓe na fuskantar matsin lamba daga masu faɗa a ji domin su zama masu biyayya ga gwamnati.
Idan har wannan shirin ya cimma nasara, akwai yuwuwar hakan zai shafi sahihancin zaɓukan 2027, kamar yadda ya faru a wasu zabukan baya.
Dokar kasa ta tanadi ‘yancin INEC
Kundin tsarin mulkin Najeriya ya kafa hukumar INEC domin zama mai zaman kanta, tare da kare ta daga tasirin siyasa.
Sashe na 153 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya kafa hukumar INEC a matsayin mai cin gashin kanta, inda ba a bukatar matsin lamba daga kowace gwamnati.
Dokar Najeriya ta bayyana cewa dole ne a tuntuɓi majalisar ƙasa kafin a naɗa sabon shugaban INEC, sannan dole ne Majalisar Dattawa ta tantance shi.
A cewar doka, wanda za a naɗa dole ne ya kasance mutum mai nagarta da ba ya cikin wata jam’iyyar siyasa.
Tinubu na son tabbatar da sahihin zaɓe
Wata majiya daga Aso Rock ta bayyana cewa Shugaba Tinubu yana son ganin sahihin tsarin zaɓe a Najeriya.
Majiyar ta bayyana cewa Tinubu yana son ganin an gudanar da adalci a zaɓukan 2027 ta hanyar naɗa mutum mai nagarta a matsayin shugaban INEC.

Asali: Facebook
Duk da wannan batu, har yanzu ana sa ido don ganin sauye-sauyen da za a yi a INEC za su kasance bisa adalci ko kuma akasin haka.
Shirin gyara tsarin zaben a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa majalisar wakilan tarayya ta yi karatu na biyu ga kudirin sauya tsarin zaben Najeriya.
Rahoton Legit ya nuna cewa idan kudirin ya samu karbuwa, za a dawo gudanar da zaben shugaban kasa da gwamnoni a rana daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng