'Dama Ta Fada': Malamin Musulunci Ya Fadi Abin da Mahaifiyar Gwamna Ta ce Zai Faru

'Dama Ta Fada': Malamin Musulunci Ya Fadi Abin da Mahaifiyar Gwamna Ta ce Zai Faru

  • Malamin addini, Alfa Mohammed Ali Eyonbo Anabi, ya ce mahaifiyar Gwamna AbdulRazaq ta tabbatar musu tun 2019 cewa ɗanta zai yi aiki nagari
  • Malamin ya ce maganar mahaifiyar gwamnan ta tabbata, domin AbdulRazaq ya nuna bajinta a mulkinsa, ya cika alkawuransa ga mutanen Kwara
  • Wani malami, Amosa Asisoloriro, ya yaba wa gwamnan saboda manyan ayyukan ci gaba da ya aiwatar, tare da tabbatar da zaman lafiya a jihar
  • Alhaji Usman Bibire Ajape ya ce AbdulRazaq shugaba ne mai adalci, ya na kira ga mutanen Kwara su mara masa baya don ci gaban jiharsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ilorin, Kwara - Wani shahararren malamin addini, Alfa Mohammed Ali Eyonbo Anabi, ya yabawa Gwamna AbdulRahman AbdulRazak na jihar Kwara.

Malamin ya tuna yadda mahaifiyar Gwamna AbdulRazaq ta tabbatar musu bayan ya hau mulki a 2019 cewa ɗanta zai yi aiki sosai.

Kara karanta wannan

Musulmin Najeriya sun yi babban rashi, Sheikh Muhammad ya rasu ana shirin sallah

Malamin Musulunci ya yabawa Gwamna kan inganta jiharsa
Malamin Musulunci ya ce tun a baya mahaifiyar gwamnan Kwara ta yi hasashen abin da zai faru. Hoto: AbdulRazak AbdulRahman.
Asali: Facebook

Yadda mahaifiyar Gwamna ta yi hasashen mulkinsa

Eyonbo Anabi ya nuna farin cikinsa cewa furucin mahaifiyar gwamnan na cewa AbdulRazaq zai yi nasara ya tabbata, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya ce:

"Mahaifiyar gwamnan ta tabbatar mana lokacin wata hira da manema labarai a 2019 cewa ɗanta zai yi aiki.
"Ta ce ta san shi sosai, koda ya ke shiru-shiru ne, amma zai gudanar da aiki nagari, gaskiya ta tabbata, domin gwamnan ya tabbatar da hakan."

Malamin ya yabawa gwamnan, yana mai cewa ya zama ɗa nagari da mahaifiyarsa ke alfahari da shi.

Malamin Musulunci ya yabawa gwamnan Kwara

A cikin wa’azinsa, wani malami, Alfa Amosa Asisoloriro daga unguwar Okelele a Ilorin, ya jinjina wa AbdulRazaq kan manyan ayyukan ci gaba da ya aiwatar.

Ya ce:

"Mafi mahimmanci, muna zaune lafiya a duk faɗin Jihar Kwara a yau Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq yana bakin ƙoƙarinsa.
"Ya kamata mu yaba masa, amma tabbas tarihi zai yi masa adalci saboda irin ayyukan alheri da yake yi."

Kara karanta wannan

Mutane sun ga abin al'ajabi da wani bawan Allah ya rasu a masallaci bayan sallar asuba

Malaman Musulunci sun yabawa Gwamna kan ayyukan alheri a jiharsa
Malamin Musulunci ya fadi yadda mahaifiyar gwamnan Kwara ta yi hasashe kan mulkinsa. Hoto: AbdulRazak AbdulRahman.
Asali: UGC

Malami ya shawarci yan kasuwa kan ajiya

Sannan malamin ya yi kira ga ‘yan kasuwa su guji ajiye kaya ko ƙara farashi, yana mai gargaɗi da su ji tsoron Allah da ranar hisabi.

A cikin wata gajerar magana, wani jigo a jam’iyyar APC, Alhaji Usman Bibire Ajape, ya yaba wa Gwamna AbdulRazaq bisa kasancewarsa shugaba mai adalci.

Ya jaddada bukatar mutanen Kwara, musamman na Ilorin, su ba gwamnan cikakken goyon baya domin ci gaban jiharsu.

Yadda aka farmaki malami yana tafsiri a Ramadan

Mun ba ku labarin cewa malamin Musulunci a Oyo, Khalifah Mojeed Alawaye, ya ce an kai masa hari yayin tafsirin Ramadan saboda ya na sukar giya da amfani da sassan jikin mutum.

Malamin ya ce wasu malamai da masu mulki a Oyo sun fusata saboda ya na kira da a hana abubuwan da ba su dace da addini ba, ya ke zarginsu da kitsa masa harin.

An ce wasu ‘yan bindiga sun kutsa wurin tafsirin da adduna da bindigogi, inda suka far wa tsofaffi da mata, har suka kwashe wayoyi da dukiyoyin jama’a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng