Bidiyo: Yadda Sheikh Pantami Ya Fashe da Kuka a Wurin Rufe Tafsirin Ramadan

Bidiyo: Yadda Sheikh Pantami Ya Fashe da Kuka a Wurin Rufe Tafsirin Ramadan

  • Sheikh Isa Ali Pantami ya fashe da kuka da hawaye a lokacin da yake addu'oin neman zaman lafiya da saukin rayuwa a wurin rufe tafsirin Ramadan
  • Babban malamin kuma tsohon ministan sadarwa a Najeriya ya roki Allah Ya kai ɗauki ga dukkan mutanen da ake zalunta a ko ina a duniya
  • Ya kuma yi wa iyaye da malamai addu'ar samun rahama, lamarin da ake tunanin shi ya fara sa Pantami kuka a wurin rufe tafsirin ranar Talata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Isa Ali Pantami ya rufe tafirin Alƙur'ani na watan Ramadan 1446AH/2025.

Sheikh Isa Pantami, wanda ke tafsiri a masallacin Annoor da ke Wuse II a Abuja, ya rufe tafsirin bana a ranar 25 ga watan Ramadan wanda ya yi daidai da 25 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Miyagu sun farmaki malamin Musulunci yana tsaka da tafsiri, ya zargi malamai

Malam Pantami.
Sheikh Isa Pantami ya yi kuka da hawaye a wurin rufe tafsirin Ramadan Hoto: Prof. Isa Ali Pantami
Asali: Facebook

Shehin malamin wanda ya kai matsayin Farfesa a karatun zamani ya wallafa bidiyon karatun karshe a shafinsa na Facebook ranar Talata da ta gabata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan kammala karatun wannan rana a Suratul Al-Imran, Pantami ya yi doguwar addu'a ta neman yardar Allah da gafara.

Sheikh Isa Pantami ya fashe da kuka

Farfesa Pantami ya fashe da kuka har da hawaye yayin da yake addu'a, yana rokon Allah gafartawa iyaye mata da maza kuma Ya kawo sauƙi a rayuwar jama'a.

Bidiyon kukan da fitaccen malamim addinin musuluncin ya yi a wurin rufe tafsir ya karaɗe shafukan sada zumunta musamman X watau Tuwita da Facebook.

Tsohon ministan ya kwararo addu'o'i masu muhimmanci game da halin da Najeriya ta tsinci kanta a ciki na matsalar tsaro da wahalar rayuwa.

Sheikh Pantami.
Malam Pantami ya yi addu'ar neman sauƙin tsadar rayuwa a wurin tafsir Hoto: Prof. Isa Ali Pantami
Asali: Facebook

Wane addu'o'in Sheikh Pantami ya yi?

Daga cikin addu'o'in da ya yi, Sheikh Pantami ya ce:

"Allah Ka ba mu mai kyau a duniya da lahira, Allah Ka yi rahama ga iyayenmu da malamanmu, Ka yi jin ƙai gare su. Ƴan uwanmu masu rauni Allah Ka kai masu ɗauki, dukan jama'ar da ake zalunta a duniya Allah ka kai masu ɗauki.

Kara karanta wannan

'Ba alfarma ba ce': Ana zargin Pantami na shirin neman mulki, ya yi wa shugabanni nasiha

"Masu laifuffuka a ƙasarmu, akwai ƴan ta'adda, masu garkuwa da mutane da ƴan bindiga, Allah Ka shirye su, Allah ka taɓa zuƙatansu ka sa su shiriya, waɗanda ba za su shiryu ba, Allah Ka sa bala'i ya kare a kansu.
"Ya Allah ƙunci ya tsananta a rayuwa, Allah Ka sauƙaƙewa talakawa, Allah ya suƙaƙe masu rayuwa. Mata suna cikin jarrabawa Allah Ka biya masu bukatunsu na alheri, yara ƙanana Allah Ka kula da tarbiyyarsu, ka ba su ilimi mai amfani."

Pantami ya yi waɗannan addu'o'i a cikin harshen Larabci da Hausa, kuma yana cikin kwarara addu'ar ne ya fashe da kuka.

Pantami ya yi wa shugabanni nasiha

A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Isa Pantami ya ja hankalin shugabanni a Najeriya kan nauyin da Allah SWT ya ɗaura masu na jagorantar al'umma.

Farfesa Pantami ya yi nasihar tun daga kan masu mukaman kansiloli da shugabannin kananan hukumomi da gwamnoni har shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262