"Sun Haƙura?" An Saki Bidiyon Sanusi II bayan Aminu Ado Ya Janye Hawan Sallah a Kano
- Rikicin hawan sallah a Kano ya zo ƙarshe da sarki na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya sanar da janye shirinsa saboda masalahar zaman lafiya
- Jim kaɗan bayan haka ne aka saki wani bidiyo da Muhammadu Sanusi II ke tambayar shin 'sun haƙura?' cikin zolaya da barkwanci
- Manyan malamai irinsu Sheikh Lawan Abubakar Triumph sun sa baki kan batun hawan sallah, suka roki Aminu Ado Bayero ya yi haƙuri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Ga dukkan alamu rikicin hawan sallah tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero ya zo ƙarshe a jihar Kano da ke Arewa maso Yamma.
An samu masalaha a wannan lamari ne bayan sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya sanar da janye shirinsa na yin hawan sallah a ƙaramar sallar da ke tafe.

Asali: Twitter
Sarki Aminu Ado ya sanar da janye hawan sallah ne a wani faifan bidiyo da shafin Masarautar Kano ya wallafa a Facebook ranar Laraba da daddare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malaman Kano sun sa baki a lamarin
Wannan mataki na zuwa ne bayan malaman Kano sun roke shi da ya duba girman Allah ya janye hawan sallah domin ceto jihar daga faɗawa hargitsi.
Sheikh Lawan Abubakar Shu'aib Triumph na ɗaya daga cikin malaman da suka fito suka roƙi mai martaba Aminu Ado ya janye hawan sallah.
Malamin ya ce duk wani mai hankali da tunani ya san cewa wannan lamari ne mai girma, wanda ka iya haifar da tashin hankalin da ba a yi tsammani ba.
Bisa haka Sheikh Triumph ya roki Aminu Ado Bayero ya duba girman Allah da kasancewarsa mutum mai son zaman lafiya, ya janye shirinsa na yin hawan sallah.
Sa'o'i ƙalilan bayan wannan, sai Sarki Aminu ya bayyana cewa ya janye shirinsa domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano.
An saki bidiyon Muhammadu Sanusi II
Bayan janyewar sarki na 15, Aminu Ado Bayero, wani mai suna Red Pen ya saki bidiyon Muhammadu Sanusi II a shafin X, inda aka ji yana tambaya cikin zolaya cewa "sun haƙura?"
Mutumin da ke ɗaukar bidiyon ya ba Mai Martaba sarki Sanusi II amsa da cewa "sun haƙura, Allah ya taimake ka."

Asali: Twitter
Faifan bidiyon ya nuna Sarki Sanusi II ya na fitowa daga fadarsa sanye da tufafin sarauta da sandar mulki a hannunsa.
Alamu sun nuna cewa an ɗauki wannan bidiyo da bai wuce daƙiƙa 18 ba a dare bayan Aminu Ado Bayero ya sanar da cewa ya janye hawan sallah.
Bayan sanar da janye gangamin sallah
Bayan sanarwar janyewar Aminu Ado Bayero daga hawan sallah, wasu manyan dattawa da ‘yan siyasa sun jinjinawa wannan mataki, suna masu cewa hakan zai taimaka wajen dakile duk wata barazana ga zaman lafiya a Kano.

Kara karanta wannan
Abin da Shehu Sani ya ce bayan Aminu Ado ya janye hawan sallah, ya shawarci Sanusi II
Daga cikin waɗanda suka tofa albarkacin bakinsu har da tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya bayyana cewa sulhu da lumana su ne manyan ginshiƙan ci gaban kowace al’umma.
Haka nan, an rawaito cewa gwamnati ta taka muhimmiyar rawa wajen sasanta rikicin. Wani jigo a majalisar dokokin jihar ya bayyana cewa an yi tarurruka masu yawa tsakanin bangarorin biyu kafin a kai ga wannan matsaya.
Bugu da ƙari, wasu daga cikin magoya bayan Aminu Ado Bayero sun nuna rashin jin daɗinsu, suna masu cewa janyewar hawan sallah wata alama ce ta matsin lamba daga wasu bangarori.
Sai dai, wasu masana tarihi sun yi bayanin cewa tun a zamanin da, masarauta tana fuskantar irin waɗannan ƙalubale, kuma mafita tana zuwa ne ta hanyar fahimta da hakuri.
Ana sa ran nan gaba za a samu karin bayani daga masarautu kan yadda za a tafiyar da al’amuran sarauta domin kauce wa sake samun irin wannan matsala a nan gaba.

Kara karanta wannan
Sheikh Lawan Triumph ya sa baki kan rikicin hawan sallah a Kano, ya aika sako ga Aminu Ado
Sallah: Ƴan sanda sun shirya bada tsaro
A wani labarin, kun ji cewa rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta gargaɗi jama'a su guji duk wani abu da ka haifar da tashin hankali a lokacin bukukuwan sallah ƙarama.
Kwamishinan ƴan sandan Kano, CP Ibrahim Bakori ya tabbatarwa al'umma cewa jami'an ƴan sanda da sauran dakarun tsaro sun shirya tsare jama'a a lokacin sallah.
Salisu Ibrahim ya fadada labarin nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng