Sheikh Lawan Triumph Ya Sa Baki kan Rikicin Hawan Sallah a Kano, Ya Aika Sako ga Aminu Ado

Sheikh Lawan Triumph Ya Sa Baki kan Rikicin Hawan Sallah a Kano, Ya Aika Sako ga Aminu Ado

  • Sheikh Lawan Abubakar Triumph ya roki sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya haƙura ya janye hawan sallah da yake shirin yi
  • A wurin tafsirin Ramadan, fitaccen malamin ya bayyana cewa duk mai hankali ya san ba ƙaramar barazana ke tunkaro Kano ba
  • Sheikh Triump ya roki ɓangaren Aminu da su haƙura sun janye domin tseratar da jinin al'umma da ceto Kano daga shiga hargitsi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Malamin addinin musulunci, Sheikh Lawan Abubakar Triumph ya sa baki kan rikicin da ke faruwa a masarautar Kano game da shirin hawan sallah.

Babban malamin ya bayyana cewa ya samu labarin ɓangaren Muhammadu Sanusi II da ɓangaren Aminu Ado Bayero sun shirya yin hawan sallah a idi mai zuwa.

Sanusi da Aminu.
Sheikh Lawan Triumph ya roki Sarki Aminu Ado Bayero ya hakura da hawan sallah Hoto: @masarautarkano, @hrhbayero, Sheikh Lawan Abubakar Shu'aib Triumph
Asali: Twitter

A wani faifan bidiyo da Kwamared Ibrahim Fada ya wallafa a shafin X, Sheikh Lawan Triumph ya buƙaci Aminu Ado Bayero ya yi haƙuri ya janye hawan sallar da yake shirin yi.

Kara karanta wannan

Ana tsakar rikicin sarauta da hawan Sallah, Kwankwaso ya dura Kano da tawagarsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Triumph ya aa baki kan hawan sallah

Ya ce gwamnatin Kano karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ba Sanusi II umarnin ya shirya hawan sallah, yayin da Aminu Ado ya sanar da hukumomi cewa zai fito hawan sallah.

Fitaccen malamin ya ce wannan matsala ce babban da ke tunkaro jihar Kano kuma duk mai hankali da tunani zai gane haka.

"Mai girma gwamnan Kano ya ba da sanarwa, mun gani a soshiyal midiya kan cewa ɓangaren sarki Sanusi II su fito su yi hawan sallah tare da hakimai da sauransu.
"Sannan kuma ɓangaren Sarki Aminu sun nemi izini a wurin jami'an tsaro duka kuma sun ba su izini, sun fito da takardu sun nuna ma jama'a a soshiyal midiya.
"Abin da wannan ke nunawa akwai matsala, idan an tafi a haka tabbas akwai matsala domin mu mutanen Kano Lahadinmu za ta ƙare a Laraba. Akwai tashin hankali, duk mai tunani ba zai so haka ba."

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta: Dalung ya yi gargadi kan 'shirin' saka dokar ta baci a Kano

- In ji Sheikh Triumph.

Malamin ya roki Aminu Ado Bayero

Da yake ba da shawarin mafita, babban malamin ya roki Sarki Aminu ya duba girman Allah ya janye saboda an san shi da ƙaunar zaman lafiya.

Sheikh Lawan Abubakar ya ƙara da cewa:

"Da wannan muke kira musamman ga ɓangaren mai martaba Sarki Aminu, su dubi girman Allah su yi haƙuri, shaidar da ake masa ta mutum ne mai son zaman lafiya, ba shi da abokin faɗa, shaida ce da har maƙiya suna faɗa.
"Har mawaƙa suna cewa Aminu ba ya faɗa kuma ba ya son mai faɗa, to muna rokon alfarma da wannan ɓangare su dubi Allah su tsare jinin al'umma, su haƙura su janye don a samu zaman lafiya.
"Allah maɗaukakin sarki ka zaunar mana da jiharmu lafiya."

Hakimin Bichi da malamai sun gana da Sanusi

A wani labarin, kun ji cewa Wamban Kano kuma hakimim Bichi ya jagoranci wakilan ƙaramar hukumar Bichi zuwa wurin mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II.

Tawagar ta kai ziyara ga sarkin ne domin yi masa barka da shan ruwa a daidai lokacin da ake surutu kan batun hawan sallah a ƙaramar sallah mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262