Ramadan Ya Zo Karshe, Gwamnatin Tinubu Ta Bayyana Ranakun Hutun Ƙaramar Sallah a Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta ayyana Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata 1 ga watan Afrilun 2025 a matsayin ranakun hutun karamar sallah
- Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 26 ga watan Maris a Abuja
- A madadin gwamnatin Bola Tinubu, ministan ya taya ɗaukacin al'ummar nusulmi murnar karkare azumin Ramadan da barka da sallah da ke tafe
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwamnatin Tarayya karƙashin jagorancin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ta sanar da ranakun hutun karamar sallah na bana 2025.
Gwamnatin ta ayyana Litinin, 31 ga Maris, da Talata, 1 ga Afrilu, 2025, a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan Eid-el-Fitr watau ƙaramar sallah.

Asali: Facebook
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Kaduna: Sarki ya samu shirgegen muƙamin gwamnati, Gwamna Uba Sani ya taya shi murna
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Babbar Sakatariya ta Ma’aikatar cikin gida, Magdalene Ajani, ta fitar.
Gwamnatin Tinubu ta taya musulmi murna
A cikin sanarwar, ministan ya taya al’ummar Musulmi murna yayin da suke shirye-shiryen kammala azumin watan Ramadan cikin nasara.
Ya kuma yi kira ga Musulmi da su rungumi halaye na gari da suka haɗa da hakuri, tausayi, kyautatawa da zaman lafiya, domin gina al’umma mai hadin kai.
Har ila yau, Dr. Tunji-Ojo ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi bukukuwan sallah cikin lumana da farin ciki ba tare da tayar da zaune tsaye ba
Sannan kuma Tunji-Ojo ya buƙaci musulmi su riƙa tunawa da marasa galihu ta hanyar ayyukan alheri da taimako, wanda hakan ke nuna hakikanin manufar Ramadan da Eid-el-Fitr.
A madadin Gwamnatin Tarayya, ministan ya mika sakon barka da sallah ga daukacin al’ummar Musulmi tare da yi musu fatan wannan lokaci mai albarka zai kawo farin ciki, nasara da cikar buri a rayuwarsu.

Kara karanta wannan
Ramadan: Dan Majalisa Kirista ya yi wa Musulmi bazata bayan bukatar babban limami
Yaushe za a yi sallah a Najeriya?
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da musulmi suka fara bankwana da watan Ramadan na wannan shekara watau 1446AH/2025.
Za a fara duban watan karamar sallah a ranar Asabar mai zuwa, 29 ga watan Ramadan wanda ya zo daidai da 29 ga watan Maris, 2025.
Idan Allah ya sa an ga watan ranar Asabar, mai alfarma sarkin musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III zai sanar da cewa za a yi sallah ranar Lahadi.
Idan kuma watan ya ɓuya, Ramadan zai cika 30 cif sannan musulmi za su yi sallah ranar Litinin, 31 ga watan Maris, 2025.
Sakamakon haka ne Gwamnatin Najeriya ta ba da hutun kwanaki biyu, Litini da Talata domin ma'aikata su samu damar yin sallah tare da iyalansu, in ji Punch.
An yi hasashen ranar ƙaramar sallah
A wani labarin, kun ji cewa an bayyana ranar da ake hasashen musulmi za su yi ƙaramar sallah a Saudiyya da wasu ƙasashen duniya.
Masana ilimin sararin samaniya sun bayyana cewa akwai damar ganin watan ƙaramar sallah ranar Asabar, amma kuma sun ce za ta iya yiwuwa a ƙi ganinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng