Miyagu Sun Farmaki Malamin Musulunci Yana Tsaka da Tafsiri, Ya Zargi Malamai

Miyagu Sun Farmaki Malamin Musulunci Yana Tsaka da Tafsiri, Ya Zargi Malamai

  • Wani malamin Islama, Khalifah Mojeed Alawaye, ya ce an kai masa hari yayin tafsirin Ramadan saboda ya na sukar giya da amfani da sassan jikin mutum
  • Malamin ya ce wasu malamai da masu mulki a Oyo sun fusata saboda ya na kira da a hana abubuwan da ba su dace da addini ba
  • Wasu ‘yan bindiga sun kutsa wurin tafsirin da adduna da bindigogi, inda suka far wa tsofaffi da mata, har suka kwashe wayoyi da dukiyoyin jama’a

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ibadan, Oyo - Wani malamin addinin Islama, Khalifah Mojeed Alawaye ya bayyana yadda aka kai masa hari yayin tafsirin Ramadan a jihar Oyo.

Malamin ya ce an kai masa hari a ranar Litinin, 24 ga Maris, 2025, a Imam Compound, kasuwar Akesan a Oyo.

Kara karanta wannan

Ali Nuhu ya sanar da rasuwar fitaccen jarumin Kannywood, Baba Karkuzu

An farmaki malamin Musulunci yana tsaka da tafsirin Ramadan
Wasu yan bindiga sun farmaki malamin Musulunci ya na cikin tafsirin Ramadan. Hoto: Legit.
Asali: Original

Yadda miyagu suka farmaki malami ya na tafsiri

Shehin ya bayyana cewa wa’azinsa ne ya haddasa hakan, saboda ya saba da wasu malamai a garin, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alawaye ya shaida cewa harin ya faru da misalin karfe 1:20 na rana, inda ‘yan bindiga suka shigo da makamai suna far wa mata da tsofaffi da ke wurin tafsirin.

Malamin ya bayyana cewa wasu malamai da musulmai su na jin haushin wa’azinsa da ke sukar shan giya da amfani da sassan jikin mutum don tsafi.

Ya ce:

“Muna faɗin gaskiya daga Al-Qur’ani da Hadisi don gargadi, ina wa’azi kan malamai da ke shan giya, yin sadaka da jini da kuma amfani da sassan jikin mutum, domin za mu tsaya gaban Allah don amsa tambaya.
“Ba na hana kowa yin nasu, amma na ke faɗa domin in wanke kaina a ranar kiyama."
An kai wa malamin Musulunci hari yana cikin tafsiri
Wasu yan bindiga sun kai hari yayin da malamin Musulunci ke cikin tafisin Ramadan. Hoto: Khalifah Mojeed Alawaye.
Asali: Facebook

Malami ya zargi yan siyasa da malamai

Malamin ya ce wasu ‘yan siyasa ma sun fusata da shi saboda ya na kira ga ‘yan siyasar Oyo da su nemi kujerar gwamna a jiha.

Kara karanta wannan

Rundunar ƴan sanda ta yi magana kan shirin hawan sarakuna 2 a Kano

Ya kara da cewa:

“Na dade ina cewa ‘yan siyasar Oyo su nemi kujerar gwamna, domin muna da masu ilimi da za su iya shugabanci, ina fadin gaskiya kamar yadda Al-Qur’ani ya koyar.
“Sun harbi dan uwana da bindiga lokacin da ba su gan ni ba, sun yi barazanar kashe shi, amma ya kalubalanci su, ban san abin da ya sa fadin gaskiya ya zama laifi ba.”

Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun zo da niyyar kashe shi, amma ya tsira da taimakon yaransa, sai dai tsofaffi sun sha wahala wajen tserewa daga wurin.

Malamin ya ce an kwashe wayoyi da kayan jama’a yayin harin, amma daga baya matasa sun taru suka kalubalanci ‘yan bindigar har suka tsere.

Ya ce an kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na Ojongbodu a karamar hukumar Oyo ta Yamma.

Malamin Musulunci ya rasu a Yobe

Kun ji cewa an yi rashi bayan Allah ya yi wa shugaban Majalisar Malamai na ƙungiyar JIBWIS watau Izala reshen jihar Yobe, Imam Muhammad Khuludu Geidam rasuwa.

Kungiyar Izala ta bayyana cewa fitaccen malamin ya riga mu gidan gaskiya a yau Laraba, 26 ga watan Ramadan, 1446AH wanda ya yi daidai da 26 ga watan Maris, 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng