Atiku Ya Debo Ruwan Dafa Kansa kan Zargin Akpabio da Cin Hanci, APC Ta Yi Martani
- Jam'iyyar APC reshen Akwa Ibom ba ta ji daɗin zargin da Atiku Abubakar ya yi wa Godswill Akpabio ba kan cin hanci da rashawa
- APC mai-ci ta bayyana tsohon mataimakin shugaban ƙasan a matsayin mutumin da bai da ƙimar da zai zargi wasu da rashin gaskiya
- Jam'iyyar ta ce har ta tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya gayawa duniya yadda Atiku ya yi ƙaurin suna wajen cin hanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Akwa Ibom - Jam'iyyar APC reshen jihar Akwa Ibom ta yi wa Atiku Abubakar martani kan zargin Godswill Akpabio da cin hanci.
Jam'iyyar ta APC ta caccaki tsohon mataimakin shugaban ƙasan kan zargin da ya yi wa shugaban majalisar dattawa na cin hanci da kuma yawan cin zarafin mata.

Asali: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran jam'iyyar, Otuekong Iniobong John, ya fitar a ranar Laraba, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akpabio: Wane martani APC ta yi wa Atiku?
Jam'iyyar APC ta bayyana cewa Atiku Abubakar ba shi da ƙimar da zai iya zargin wasu da cin hanci.
“Maganganun Atiku Abubakar kan Sanata Godswill Akpabio sun nuna wata irin manufa ta nuna ƙiyayya da neman amfani da siyasa don cimma burinsa."
“A tarihi, Atiku Abubakar ana kallonsa a matsayin wanda ya fi kowa cin hanci a cikin ƴan siyasar Najeriya. A lokacin da yake matsayin mataimakin shugaban ƙasa, ya yi amfani da ofishinsa wajen siyan kadarorin ƙasa ta hanyar damfara."
“Waɗannan zarge-zarge sun samu tabbaci daga tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, wanda ya bayyana a fili cewa Atiku ya yi fice wajen cin hanci ta yadda bai kamata a damƙa masa amanar wani muƙamin gwamnati ba."
“Tsohon shugaban ƙasa Obasanjo ya sha bayyana cewa ya yi nadamar zaɓen Atiku a matsayin mataimakinsa a lokacin mulkinsa, ya na mai cewa mutum ne maras kunya kuma maƙaryaci wanda bai dace a amince da shi ba."
“A fili yake cewa mutumin da ke da irin wannan mummunan sunan ba shi da hurumin zargin wasu game da cin hanci."
- Otuekong Iniobong John

Asali: Facebook
Jam’iyyar APC ta jaddada cewa Sanata Akpabio ya kasance mai gaskiya da kishin aiki a harkokin gwamnati.
Ta ƙara da cewa lokacin da ya yi gwamna a jihar Akwa Ibom, ya nuna jagoranci nagari tare da aiwatar da shirye-shirye da ayyukan raya ƙasa da har yanzu jama'a ke amfana da su.
Atiku ya magantu kan yin takara a 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana matsayarsa kan sake yin takara a zaɓen 2027.
Atiku ya bayyana cewa har yanzu bai da masaniya kan cewa ko zai sake jaraba sa'arsa wajen neman shugabancin ƙasar nan.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya bayyana cewa ƙasar nan na buƙatar jam'iyya mai ƙarfi domin kawo shugabanci na gari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng