An Shiga Jimami a Kano: Babban Mai Taimaka wa Gwamna Abba Ya Rasu Ana Azumi
- An shiga jimami a Kano yayin da aka sanar da rasuwar Abdullahi Tanka Galadanci, babban mai taimakawa Abba Kabir Yusuf kan Rediyo
- Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana cewa Galadanci ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya a asibiti
- Gwamnan Kano ya bayyana marigayin a matsayin ginshiki a gwamnatinsa, ya na mai addu’ar Allah ya gafarta masa, ya kuma ba iyalansa hakuri
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - An shiga jimami a jihar Kano da kewaye, yayin da aka samu labarin rasuwar Abdullahi Tanka Galadanci, babban mai taimakawa gwamnan Kano kan rediyo.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya sanar da rasuwar Abdullahi Tanka Galadanci, cike da alhini da mika lamura ga Allah Subhanahu Wata'Ala.

Asali: Facebook
An sanar da rasuwar hadimin gwamnan Kano
Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar da sanarwar a shafinsa na Facebook a yammacin ranar Laraba, 26 ga Maris.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar, Sanusi Dawakin Tofa ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna jimami da kaduwarsa matuƙa bisa wannan rashi da aka yi.
Sanarwar ta bayyana cewa marigayi Galadanci ya rasu ne a ranar 26 ga Maris, 2025, bayan gajeruwar rashin lafiya a asibitin koyarwa na Aminu Kano.
Sanarwar Dawakin Tofa, ta rahoto cewa Gwamna Abba ya bayyana marigayi Abdullahi Galadanci a matsayin mutum mai jajircewa kuma ginshiki a gwamnatinsa.
Gwamnan Kano ya yi alhinin rasuwar hadiminsa
Gwamnan na Kano ya ce marigayin ya ba da muhimmiyar gudunmawa wajen ci gaban harkokin watsa labarai da sadarwa a jihar.
Abba Yusuf ya ce:
“Rasuwar Abdullahi Tanka Galadanci babban rashi ne ga wannan gwamnati da kuma daukacin al’ummar jihar Kano.
"Za mu yi matuƙar kewarsa saboda sadaukarwa da ƙwazon da ya nuna wajen inganta hanyoyin sadarwarmu.
“Muna miƙa ta’aziyyarmu ga iyalansa, abokansa da kuma abokan aikinsa a wannan lokaci da mu ke cikin juyayi na rashinsa."
Ana sa ran gudanar da jana’izar marigayi Abdullahi Tanka Galadanci da misalin karfe 5:30 na yamma a Masallacin Filin Galadanchi, kusa da gidan Galadiman Kano.
Karanta sanarwar a nan kasa:
Kanawa sun yi alhinin rasuwar Galadanchi

Asali: Facebook
Legit Hausa ta tattaro sakonnin ta'aziyya da al'ummar Kano suka aika, bayan rasuwar Abdullahi Galadanchi:
Mu'azu Saleh:
"Hakika gwamnatin Kano da mai girma gwamna sun yi babban rashin zakakurai masu amana har mutum biyu; Dan-Zago ya tafi ga Galadanchi shi ma an koma ga Allah.
"Ubangiji Allah ya jaddada masu Rahama da sauran magabata. Idan tamu tazo Ubangiji Allah yasa mucika da imani."
Abban Saiham"
"Allah ya jikan shi da rahama ya kyautata namu zuwan."
Aisha Abubakar:
"Allah ya gafarta masa."
Salihu Adam Salihu:
"InnalliLahi waiina iLahi Raji'un. Allah Ta'ala ya sa Aljana makomarsa, tare da saura al'ummar Musulmai baki daya, Amin."
Aliyu Wada Tudunkaya:
"Allah ya gafarta wa Abdullahi Galadanci."
Hadimin Gwamna Abba ya rasu awanni da nadinsa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna alhini kan rasuwar daya daga cikin sababbin hadiman da ya nada kwanan nan.
A ranar Talata, 7 ga Janairu, 2025, Gwamna Abba ya naɗa Ahmad Ishaq Bunkure a matsayin mashawarcinsa na musamman kan harkokin ayyuka, kuma ya rasu a ranar Laraba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng