Za a Share Hawayen Ƴan Najeriya, Majalisa Ta Ɗauki Mataki kan Tsadar Datar MTN da Airtel

Za a Share Hawayen Ƴan Najeriya, Majalisa Ta Ɗauki Mataki kan Tsadar Datar MTN da Airtel

  • Majalisar Dattawa za ta gudanar da bincike kan tsadar kudin sayen datar kamfanonin sadarwa irinsu MTN da Airtel a Najeriya
  • Hakan na ɗaya daga cikin matakan da Majalisar ta ɗauka a wani kudiri da Sanatan Kuros Riba ta Kudu ya gabatar a zaman ranar Laraba
  • Majalisar ta umarci ministan sadarwa ya kira kamfanonin su tattauna domin rage farashin data daidai da yadda ƴan Najeriya za su iya saye

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Koken ƴan Najeriya kan masifar tsadar datar kamfanonin sadarwa musamman waɗanda aka fi amfani da su watau MTN da Airtel ya fara shiga kunnuwan shugabanni.

Majalisar Dattawan Najeriya a ranar Laraba ta umarci Kwamitin Sadarwa da ya binciki karin farashin data da aka yi kwanan nan da mutane ke ta kuka da shi.

Kara karanta wannan

2027: 'Yan majalisa na kwaskware tsarin zaben shugaban kasa da gwamnoni

Majalisar Dattawa.
Majalisa za ta gudanar da binckike kan tsadar data a MTN da Airtel Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Majalisa ta sa baki ka tsadar data

Kamar yadda Channels tv ta kawo, majalisar ta kuma buƙaci kwamitin ya bada shawarwari don samar da mafita mai dorewa da dacewa ga bangaren sadarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan mataki wani bangare ne na kudurin da Sanata Asuquo Ekpenyong (Kuros Riba ta Kudu) ya gabatar a zaman Majalisar Dattawa yau Laraba.

Sanatan ya shaida wa majalisar cewa karin kudin ya jefa miliyoyin ‘yan Najeriya, musamman matasa da ke dogaro da intanet wajen samun kudin shiga, cikin matsi.

Matakan da Majalisar dattawa ta ɗauka

Kudurin ya bayyana cewa karin farashin data da ya kai sama da kashi 200% ya yi matukar shafar ‘yan kasa, musamman matasa da ke amfani da intanet a sana’o’insu.

Daga cikin kudurorin da majalisar ta amince da su, akwai bukatar Ministan Sadarwa, Kirkire-kirkire da Tattalin Arzikin Zamani ya zauna da kamfanonin sadarwa domin duba karin farashin data.

Sannan Majalisar ta umarci ministan da ya tabbatar da cewa farashin data ya dawo mai sauki ga kowa da kowa.

Kara karanta wannan

Yadda Akpabio ya jawo alkali ya cire hannu a shari'arsa da Natasha a kotu

Matsalolin da ke kawo cikas a sadarwa

Kudurin ya lissafo wasu matsaloli da ke haddasa tsadar sadarwa a Najeriya, kamar:

  • Rashin wadatacciyar hanyar sadarwa da matsalolin wutar lantarki
  • Ƙaruwar kudaden shigo da kayayyakin fasahar sadarwa
  • Haraji da caji iri-iri daga hukumomin gwamnati daban-daban
  • Matsalar tsaro da ke kara kawo haɗari da kudin inshora
  • Tsare-tsaren gwamnati da ke hana saurin bunkasar harkokin kasuwanci da kirkire-kirkire
  • Tsadar man dizal da makamashi sakamakon rashin ingantacciyar wutar lantarki daga gwamnati

Domin shawo kan wadannan matsaloli, majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta tattauna da kamfanonin sadarwa don duba karin farashin data da tabbatar an rage tsadar domin amfanin ‘yan kasa.

Haka kuma, majalisar ta amince da kudirin dokar da ke wajabta rajistar ‘yan kasa, wanda zai taimaka wajen tantance ‘yan Najeriya ta hanyar rusa tsohuwar dokar Hukumar Kula da Shaidar Dan Kasa (NIMC) tare da kafa sabuwa.

Majalisa ta yi watsi da ƙorafin Natasha

Kara karanta wannan

Awanni da nada sababbin hadimai, Abba ya ba su umarnin bayyana yawan kadarorinsu

A wani labarin, kun ji cewa an yi fatali da ƙorafin da dakatacciyar sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti ta shigar kan zargin Godswill Akpabio.

Kwamitin ladabtarwa na Majalisar Dattawa ya ce ba zai saurari ƙorafin da ɗan mazaɓar Natasha ya shigar ba saboda lamarin na gaban kotu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng