Kariya Za Ta Kare: Majalisa Ta Amince da Kudirin da Zai Tubewa Ƴan Siyasa Zani a Kasuwa
- Majalisar wakilai ta amince da kudirin da ke neman cire kariya daga shari’a ga Mataimakin Shugaban Kasa, Gwamnoni da mataimakansu
- 'Dan majalisa, Solomon Bob ne ya dauki nauyin kudirin domin hana rashawa, kawar da rashin hukunci da karfafa gaskiya a shugabanci
- Kudirin ya na neman gyara sashe na 308 na kundin tsarin mulki, wanda ke kare shugabannin daga tuhuma ta shari’a a lokacin da suke kan mulki
- Majalisar ta kuma amince da kudiri na ba sarakuna matsayi a kundin mulki, tare da gyara tsarin mulkin kan kananan hukumomi da kirkirar sababbin jihohi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta yi zama a kan kudirin da ke neman tube wa masu mukamai zani a kasuwa.
Majalisar ta amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulki a karon farko wanda ke neman cire kariyar shari’a ga Mataimakin Shugaban Kasa, Gwamnoni da mataimakansu.

Kara karanta wannan
Za a share hawayen ƴan Najeriya, Majalisa ta ɗauki mataki kan tsadar datar MTN da Airtel

Asali: Facebook
An gabatar da kudirin ƙirƙirar jihohi a majalisa
'Dan majalisar, Solomon Bob daga jihar Rivers ne ya dauki nauyin kudirin, kamar yadda TheCable ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan kudirin ƙirƙirar sababbin jihohi ya tsallake karatu na biyu a yau Laraba 26 ga watan Maris, 2025.
Majalisar ta amince da karatu na biyu na kudirori hudu da ke neman kirkirar sababbin jihohi a Najeriya.
Har ila yau, an amince da wasu karin kudirori 38 da ke neman sauya kundin tsarin mulki na shekarar 1999.
Sababbin jihohin da ake so a kirkira su ne Oke-Ogun, Ijebu, Ife-Ijesa, Tiga a jihar Kano da Orlu da Etiti domin hadewa da jihohi 36.

Asali: Facebook
Kudirin cire kariya ga wasu 'yan siyasa
'Dan majalisar ya ce kudirin zai taimaka wajen hana rashawa, kawar da rashin hukunci da karfafa gaskiya a shugabanci.
Sashe na 308 na kundin tsarin mulki ya na ba Shugaban Kasa, Mataimakinsa, Gwamnoni da mataimakansu kariya daga shari’a yayin da suke kan mulki.

Kara karanta wannan
Maganar kirkirar sababbin jihohi ta dawo, kudirin ya tsallake karatu na 2 a majalisa
Kudirin yana neman gyara hakan domin rage yawan cin hanci da rashawa a cikin gwamnati, cewar rahoton The Nation.
Majalisar ta kuma amince da kudirin baiwa sarakuna matsayi a kundin mulkin Najeriya domin kara musu daukaka fiye da yanzu.
Haka kuma, an gabatar da kudiri na kirkirar jihar Etiti daga yankin Kudu maso Gabas domin tabbatar da daidaito tsakanin yankin da kuma sauran yankunan Najeriya.
Misali, yankin Arewa maso Yamma yana da jihohi bakwai, Arewa maso Gabas kuma shida sai kuma Arewa ta Tsakiya guda shida da Kudu maso Kudu da kuma Yamma suna da shida kowane.
Ana ƙoƙarin kwaskware zaben shugaban kasa
Kun ji cewa majiyoyi sun nuna cewa majalisar wakilai ta yi karatu na biyu ga kudirin dokar da ke neman gudanar da dukkan zaɓuka a rana guda.
Kudirin ya tanadi cewa zaɓen shugaban ƙasa, gwamna, ‘yan majalisar dokoki da kananan hukumomi su kasance a rana ɗaya.
Majalisar ta kuma karanta wani kudiri da ke neman kotun ɗaukaka ƙara ta zama matakin ƙarshe wajen sauraron ƙarar zaɓen gwamna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng