Ana Zancen Hawan Sallah, Sarakuna da Malaman Bichi Sun Gana da Sanusi II a Kano

Ana Zancen Hawan Sallah, Sarakuna da Malaman Bichi Sun Gana da Sanusi II a Kano

  • Hakimin Bichi da shugabannin Karamar Hukumar Bichi sun kai wa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ziyara a fadarsa
  • Rahotanni sun tattabar da cewa sun ziyarci Muhammadu Sanusi II ne domin yi masa barka da shan ruwa a cikin watan Ramadan
  • Lamarin ya jawo martani daga jama’a, wasu na yaba wa ziyarar, yayin da wasu ke ganin ta na da nasaba da rikicin sarautar Kano

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - A yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan batun sarautar Kano, Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya karɓi bakuncin hakimin Bichi.

An ruwaito cewa daga cikin wadanda suka kai ziyarar akwai manyan shugabannin Karamar Hukumar Bichi.

Fadar Kano
Shugabannin Bichi sun ziyarci mai martaba Sanusi II. Hoto: Sanusi II Dynasty
Asali: Facebook

Shugabannin Bichi sun hadu da Sanusi II

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Majalisa ta yi hukuncin karshe a korafin Natasha kan Akpabio

Shafin Sanusi II Dynasty ne ya wallafa labarin ziyarar a Facebook, aka bayyana cewa sun je ne domin gaisuwa da yi wa sarkin barka da shan ruwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ziyarar ta samu halartar Wamban Kano, wanda shi ne Hakimin Bichi, tare da shugaban Karamar Hukumar Bichi, da dagatai, masu unguwanni, da limaman yankin.

Sanarwar ta ce:

"Mai girma Wamban Kano kuma Hakimin Bichi tare da shugaban karamar hukumar Bichi, da dagatai da masu unguwanni...
Limaman karamar hukumar Bichi ne suka zo yi wa mai martaba sarkin Kano Khalifa Muhammad Sanusi ll PhD, CON barka da shan ruwa."

Mutane sun yi martani kan lamarin

Bayan da labarin ziyarar ya karade shafukan sada zumunta, mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da abin da ke faruwa.

Saleh Musaningi ya yi fatan alheri ga Hakimin Bichi da sauran shugabannin da su ka kai ziyarar, inda ya ce:

Kara karanta wannan

Rigimar sarauta: Kalu ya hadu da Aminu Bayero a taro, ya ƙi kiransa da 'sarkin Kano'

"Mai girma Chiroman Kano, Hakimin Bichi tare da shugaban Karamar Hukumar Bichi, Allah ya ja kwananku."

Shi kuwa Jamilu Halliru Yallabai, ya bayyana godiya tare da yin addu’a ga Kano, ya na mai cewa:

"Masha Allah, Allah ya zaunar da Kano lafiya. Duk wanda ke son kawo fitina a Kano, Allah ya isar mana a kansa, musamman a daren Lailatul Qadr."

Sai dai wani mai suna Ahmad Bello ya nuna shakku kan dalilin ziyarar, ya na mai cewa:

"’Yan Kwankwasiyya ne dai, domin naga kusan kowa da jar hula."

Rikicin sarautar Kano ya dauki sabon salo

Tun bayan dawowar Muhammadu Sanusi II kan karagar mulki a shekarar 2024, batun sarautar Kano ya ci gaba da jawo cece-kuce.

A halin yanzu, bangarorin biyu – na Sanusi II da na Aminu Ado Bayero – na ci gaba da gudanar da ayyukan sarauta, lamarin da ke haddasa rarrabuwar kawuna a tsakanin jama’a.

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta: Dalung ya yi gargadi kan 'shirin' saka dokar ta baci a Kano

Yayin da ake shirin gudanar da bukukuwan Sallah, mutane da dama na sa ido kan yadda za a tafiyar da hawan sallah a jihar.

A halin yanzu, jama’a na ci gaba da fatan ganin cewa an samu zaman lafiya da sulhu a Kano, domin a guje wa rikici ko rabuwar kai tsakanin al’ummar masarautar.

Dalung ya yi magana kan sarautar Kano

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung ya yi magana kan sarautar Kano.

Dalung ya bukaci a maganace rikicin da ke tsakanin mutane biyu masu ikirarin zama sarakuna domin kaucewa wata fitina a jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel