Ta Faru ta Kare: Majalisa Ta Yi Hukuncin Karshe a Korafin Natasha kan Akpabio
- Majalisar Dattawa ta yi watsi da ƙorafin da aka shigar kan zargin cin zarafin da aka yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
- Sanata Onyekachi Nwebonyi da tsohuwar Ministar Ilimi, Dr Oby Ezekwesili, sun yi musayar yawu kan yadda ake tafiyar da batun
- Wani lauyan mai kare Sanata Natasha ya zargi majalisar da rashin bin doka da amfani da ƙa’idojin da suka fi dacewa da son rai
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kwamitin ladabtarwa na Majalisar Dattawa ya yi watsi da ƙorafin da aka shigar kan zargin cin zarafin da aka yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Wani mutumi daga mazabar sanatar, Zubairu Yakubu, ne ya shigar da ƙorafin, amma kwamitin ya ce ba zai saurare shi ba saboda maganar na gaban kotu.

Kara karanta wannan
Kano ta ɗauki zafi da kwamishinan Abba ya sa ƴan sanda suka tsare wasu ƴan jarida

Asali: Facebook
Rahoton The Nation ya nuna cewa wani rikici ya barke tsakanin Sanata Onyekachi Nwebonyi da tsohuwar Ministar Ilimi, Dr. Oby Ezekwesili, kan yadda ake tafiyar da batun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin watsi da zargin Natasha a majalisa
Kwamitin ya ce ba zai saurari ƙorafin ba, kasancewar an riga an shigar da kara a gaban kotu, kamar yadda dokokin Majalisar Dattawa suka tanada.
Sanata Imasuen da ke shugabantar zaman, ya bayyana cewa dokar majalisa ba ta yarda a saurari ƙorafi da ke gaban kotu ba.
Sai dai Dr Ezekwesili ta nuna rashin amincewa da matakin, tana mai cewa dokar majalisa ba za ta iya fin karfin kundin tsarin mulki ba.
Yadda rikici ya kaure a Majalisar dattawa
A lokacin zaman, Sanata Nwebonyi ya fusata bayan da Dr Ezekwesili da wasu ba su amince su rantse ba kafin su bada shaida.
Punch ta wallafa cewa Sanatan ya ce wa Dr Ezekwesili:

Kara karanta wannan
Natasha: Fada ya barke a majalisa, an yi kaca kaca tsakanin sanata da tsohuwar minista
"Kin ba mata kunya! Kina da hali irin na ‘yan daba. Mutane irinki ba su da darajar zuwa wannan waje."
Dr Ezekwesili ta mayar da martani, ta na mai cewa majalisar na kokarin fakewa da wasu ƙa’idoji don kauce wa tantance gaskiya.

Asali: Facebook
Mai ƙorafi ya ce ba ayi masa adalci ba
Zubairu Yakubu, wanda ya shigar da ƙorafin, ya bayyana cewa an hana babbar shaidarsa, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, halartan zaman.
Zubairu Yakubu ya ce:
"Tun da farko na bayyana cewa Sanata Akpoti-Uduaghan ce za ta gabatar da hujjojinta, amma an hana ta shiga majalisa.
"Ta yaya zan gabatar da ƙorafina ba tare da babbar shaida ta ba?"
Lauyan mai ƙorafi, Dr Abiola Akinyode, ta soki yadda Majalisar Dattawa ke tafiyar da shari’o’in da aka shigar gabanta.
A yanzu haka dai za a zuba ido a a ga matakin da kotun tarayya za ta dauka kasancewar majalisa ta ki sauraron korafin saboda yana gaban alkali.

Kara karanta wannan
"Ta kai ƙorafi LPDC," Natasha ta sake kinkimo rigima, ta zargi Sanata da 'rashin ɗa'a'
Alkali ya zare hannu a shari'ar Natasha
A wani rahoton, kun ji cewa alkalin da ake sauraron karar da Sanata Natasha Akpoti ta shigar da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya janye hannu a shari'ar.
Alkalin kotun ya bayyana cewa ya zare hannu a lamarin ne bayan korafin da Sanata Godswill Akpabio ya shigar a kansa game da masa adalci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng