Rikicin Sarauta: Dalung Ya Yi Gargadi kan 'Shirin' Saka Dokar Ta Baci a Kano
- Tsohon Ministan Wasanni, Barrister Solomon Dalung, ya nuna damuwa kan yiyuwar ayyana dokar ta-baci a jihar Kano
- Dalung ya yi wannan rubutu ne bayan rahoton batun gudanar da hawan Sallah daga bangaren sarakunan Kano guda biyu
- Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu kan wannan batu, inda wasu suka bukaci a yi taka-tsantsan don kauce wa rikici
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Tsohon Ministan Wasanni, Barrister Solomon Dalung, ya nuna damuwa kan halin da ake ciki a Kano, yana mai cewa ana shirin maimaita irin abin da ya faru a Jihar Rivers.
Dalung ya yi maganar ne bayan wani rahoton da ke nuna cewa Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero, na shirin gudanar da hawan sallah a Kano.

Asali: Facebook
Tsohon ministan ya yi gargadi kan magance rikicin sarautar Kano a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci sarakunan su shirya hawan sallah kafin daga bisani Aminu Ado Bayero ya ce shi ma zai fita hawan sallah.
Shirin gudanar da hawan Sallah a Kano
Bayan umarnin Gwamnan Kano, mai martaba Aminu Ado Bayero, ya aika wasiƙa ga rundunar ‘yan sanda ta jihar, ya na sanar da shirinsa na gudanar da bukukuwan Sallah.
A cikin wasiƙar da Sakataren Aminu Ado, Abdullahi Haruna Kwaru, ya sanyawa hannu, an bayyana cewa za a fara shagulgulan Sallah tun daga ƙarshen watan Maris 2025.
A cewar wasiƙar, za a gudanar da Hawan Sallah, Hawan Daushe da Hawan Nassarawa daga ranar 1 zuwa 3 ga watan Shawwal 1446AH.
Dalung ya yi gargaɗi kan dokar ta-baci
Solomon Dalung ya bayyana damuwarsa kan halin da ake ciki a Kano, ya ce idan ba a yi taka-tsantsan ba, lamarin na iya kai wa ga ayyana dokar ta-baci kamar yadda aka yi a Jihar Rivers.
Dalung ya ce:
"Wannan lamari, idan ba a kula da shi sosai ba, yana da hatsarin iya fuskantar irin haramtacciyar mugunyar makarkashiya da aka yi wa mutanen Jihar Rivers."
A shekarar 2020 Abdullahi Ganduje ya tube rawanin Muhammadu Sanusi II, ya nada Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano.
Sai dai a 2024, gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta yi gyaran doka tare da mayar da Sanusi II kan karagar mulki.

Asali: Twitter
Ra’ayoyin jama’a kan hawan sallar Kano
Bayan kalaman Dalung, mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu kan rikicin Kano da yiyuwar ayyana dokar ta-baci.
Ibrahim Muhammad ya ce:
"Son zuciya ba cin nasara ba ne. Idan mutum bai samu abin da yake so ba, ya kamata ya yi hakuri don zaman lafiya."
Fatima Abdullahi Haruna ta ce:
"In sha Allah, Kano ta fi ƙarfin duk wani azzalumi."
Hassan So Salisu ya ce:
"Allah ya kawo mana zaman lafiya da shugabanni nagari. Wannan lamarin na bukatar a yi duba sosai domin guje wa rikici."
Pantami ya magantu kan sarautar Kano
A wani rahoton, kun ji cewa malamin musulunci, Sheikh Isa Ali Pantami ya yi magana kan rikicin sarautar Kano.
Sheikh Pantami ya bukaci a rika kai zuciya nesa da kuma fifita bukatun al'umma domin samar da zaman lafiya a Kano da Arewa baki daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng