Aiki Ya Dawo Sabo: Gwamnoni 7 Sun Hada Kai, Sun Maka Tinubu a Kotu kan Fubara
- Gwamnonin PDP sun shigar da ƙara a Kotun Koli, suna kalubalantar dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da Shugaba Bola Tinubu ya yi
- Sun ce shugaban kasa ba shi da ikon dakatar da gwamna, mataimakiyarsa, ko majalisa, inda suka nemi kotu ta haramta matakin na Tinubu
- Gwamnonin sun bukaci kotu ta soke dokar ta-baci, ta rushe nadin rikon kwarya, tare da hana Tinubu shiga harkokin mulkin jihohi nan gaba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Wasu gwamnonin jam’iyyar PDP ke mulki sun shigar da ƙara a gaban Kotun Koli, suna kalubalantar dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas.
Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Odu, da ‘yan majalisar dokokin jihar na watanni shida bayan ayyana dokar ta-baci.

Asali: Twitter
Gwamnonin PDP sun maka Tinubu a kotu
Shugaban kasar ya ayyana dokar ta-bacin ne a ranar 18 ga Maris, ya nada wani shugaba na rikon kwarya domin tafiyar da jihar Ribas, a cewar rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A gefe guda, ‘yan majalisar dokokin ƙasa sun goyi bayan matakin Shugaba Tinubu na dakatar da gwamnan da mataimakiyarsa tare da 'yan majalisar jihar.
Sai dai gwamnonin Bauchi, Adamawa, Bayelsa, Enugu, Osun, Filato, da Zamfara sun kalubalanci ikon Tinubu na daukar irin wannan mataki.
An jero sunayen Tinubu da majalisar dokoki ta kasa a matsayin waɗanda gwamnonin suka shigar da ƙara a gaban Kotun Koli.
Bukatun da gwamnoni suka gabatar wa kotu
Gwamnonin bakwai sun ce ba a bi tsarin doka wajen dakatar da Fubara ba, tare da neman kotun ta bayyana cewa shugaban kasa ba shi da ikon yin hakan.
Sun yi nuni da sashe na 1(2), 5(2), da 305 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriy na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima), wanda ya hana irin wannan dakatarwa.
Gwamnonin sun kuma bukaci kotu ta bayyana cewa shugaban kasa ba shi da ikon dakatar da majalisar dokokin jiha bisa tanadin kundin tsarin mulki.
Gwamnonin sun bukaci Kotun Koli ta bayyana dakatarwar Fubara da majalisarsa a matsayin haramtacciya, da ta sabawa doka da kuma take kundin tsarin mulki.
Sun jaddada wa kotun cewa Shugaba Tinubu ba shi da ikon dakatar da gwamna mai ci sannan ya nada shugaban rikon kwarya a madadinsa.
Ana so kotu ta hana Tinubu taba gwamnoni
Gwamnonin sun bukaci kotun ta rushe nadin Vice Admiral Ibok-Ete Ibas a matsayin shugaban rikon kwarya na jihar Ribas, saboda rashin bin tsarin doka.
Sun kuma kalubalanci sahihancin amfani da tsarin kada kuri'ar baki da majalisar tarayya ta yi wajen amincewa da matakin da Tinubu ya dauka.
Gwamnonin sun jaddada cewa ayyana dokar ta-bacin ba ta cika sharuddan da sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulki ya tanada ba.
Sun bukaci kotu ta soke dokar ta-bacin, ta hana Tinubu shiga harkar gwamnonin jihohi, da tabbatar da ikon Fubara da mataimakiyarsa na ci gaba da aikinsu.
Lauya ya maka Tinubu a kotu kan Fubara
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani lauya ya yi karar Shugaba Bola Tinubu a kotu kan ayyana dokar ta baci a Rivers da dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara.
Lauyan mai suna Johnmary Jideobi, ya nemi kotu ta ayyana dakatarwar da Tinubu ya yi wa Fubara da nadin shugaban riko na Rivers a matsayin haramun.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng