Kwamishinan Abba Ya Yi Murabus ana tsaka da Takaddamar Sarautar Kano

Kwamishinan Abba Ya Yi Murabus ana tsaka da Takaddamar Sarautar Kano

  • Kwamishinan Tsaron Gida da Ayyuka na Musamman na Kano, Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris (mai ritaya), ya yi murabus daga mukaminsa
  • Gwamnatin Kano ta tabbatar da hakan tare da bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus din kuma ya yi masa fatan alheri
  • Janar Idris shi ne kwamishina na biyu da ya ajiye aiki a 2025, bayan Mohammed Diggol, Kwamishinan Kula da Ayyuka da ya sauka tun farkon shekara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Ayyuka Musamman na Jihar Kano, Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris (mai ritaya), ya ajiye mukaminsa bayan watanni bakwai da naɗa shi.

An naɗa shi a watan Agustan 2024 a matsayin kwamishina na farko na sabuwar ma’aikatar da aka ƙirƙira domin kula da tsaron cikin gida a Kano.

Kara karanta wannan

Rundunar ƴan sanda ta yi magana kan shirin hawan sarakuna 2 a Kano

Abba Kabir
Gwamna ya amince kwamishina ya yi murabus a Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Mai Magana da yawun gwamna Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana haka a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Leadership ya rawaito cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya gode masa bisa gudunmawar da ya bayar, tare da fatan alheri a rayuwars da zai yi bayan ajiye aikin.

Gwamna ya amince da murabus din Kwamishina

A cikin sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, an tabbatar da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus din kwamishinan.

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnan ya yaba wa Manjo Janar Idris bisa ƙoƙarinsa tun daga lokacin da yake aikin soja har zuwa lokacin da ya yi aiki a Kano.

Hanar Idris ya kafa tubalin ma’aikatar tsaron Kano

Bayan naɗa shi a matsayin kwamishinan tsaro a Kano, Manjo Janar Idris ya taka rawa wajen kafa tubalin yadda ma’aikatar za ta gudanar da aikinta.

Kara karanta wannan

Dambarwar masarauta: Gwamnatin Abba ta aika sako ga 'makiya Kano'

A cikin sanarwar gwamnan, an bayyana cewa:

"Muna gode wa Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris (mai ritaya) bisa sadaukarwarsa da gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban Kano.
"Muna fatan Allah Ya albarkace shi da samun hutun da ya dace da shi bayan ya bar aikin gwamnati."

Ba a bayyana dalilin murabus din kwamishina ba

Duk da cewa babu cikakken bayani kan dalilin murabus din Idris, gwamnan ya nuna kwarin gwiwa cewa wanda zai gaje shi zai ci gaba da inganta ayyukan ma’aikatar.

Har yanzu dai ba a bayyana wanda zai maye gurbin Manjo Janar Idris ba, amma ana sa ran gwamnan zai naɗa sabon kwamishina a makonni masu zuwa.

Abba Kabir
Abba Kabir yayin kaddamar da aikin titi a Kano. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Jihar Kano ta yi suna wajen fama da matsalar 'yan daba a unguwanni wanda ake ganin hakan zai sanya Abba Kabir Yusuf nada sabon kwamishinan tsaro cikin kankanin lokaci.

Sanusi II ya yi ziyarce ziyarce a Kano

Kara karanta wannan

Kaduna: Sarki ya samu shirgegen muƙamin gwamnati, Gwamna Uba Sani ya taya shi murna

A wani rahoton, kun ji cewa sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya kai ziyarce ziyarce wurare da dama a cikin Kano a watan Ramadan.

Daga cikin wuraren da Muhammadu Sanusi II ya ziyarta akwai majalisin Sheikh Uwais Limanci da kasuwar Dakata da aka tafka asara bayan gobara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng