'Mu Hadu a Kotun Koli': Gwamnatin Kano Ta Dauki Matakin Tabbatar da Nadin Sanusi II
- Rikicin sarautar Kano tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero ya kai gaban Kotun Koli, yayin da ake jiran hukuncin karshe
- Kotun daukaka kara ta jingine hukuncin da ya tabbatar da nadin Sanusi II, tare da bukatar bangarorin su tsahirta kafin daukar wani mataki
- Gwamnatin jihar Kano ta daukaka kara zuwa Kotun Koli, tana mai cewa akwai kuskure a hukuncin da Mai shari'a Okon Abang ya yanke
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Rikicin sarautar Kano, tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero ya ɗauki sabon salo, inda yanzu batun ke gaban Kotun Koli.
Ana jiran Kotun Koli ta kawo karshen sa-in-sar da ake tafkawa kan wanene sahihin sarkin Kano, tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado.

Asali: Twitter
Rahoton jaridar Punch, ya nuna cewa, gwamnatin Kano ta nemi Kotun daukaka kara da ta jinkirta hukuncinta, saboda ta shigar da kara a Kotun Koli.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alkali ya tura shari'ar Sanusi, Bayero Kotun Koli
A ranar Talata ne kotun daukaka kara da ke Abuja ta jingine hukuncin da aka yanke a baya kan sake nadin Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano na 16.
Hakazalika, kotun, bayan ta tabbatar da mika shari'ar zuwa Kotun Koli, ta gargadi bangarorin da abin ya shafa kan daukar kowane irin mataki, har Kotun Koli ta yi hukunci.
A hukuncin da kotun, mai alkalai uku, bisa jagorancin Mai shari'a Biobele Abraham George ta yanke, ta amince da janye wata bukata da gwamnatin Kano ta gabatar.
Gwamnatin Kano ta mika takardu Kotun Koli
Yayin da aka dawo ci gaba da zama kan aiwatar da umarninta na baya, lauyan gwamnatin Kano, Ibrahim Wangida, ya shaidawa kotun cewa sun daukaka karar wannan umarni a ranar 14 ga Maris.
Wangina ya ce sun bi duk wasu matakai na shari'a, ciki har da mika takardun shari'ar da ake a kotun daukaka kara zuwa Kotun Koli don dakatar da umarnin kotun.

Kara karanta wannan
Bayan ganawar Aminu da Wike, ana fargabar kotu na iya hana Sanusi II hawan Sallah
Mika bayanan shari'ar zuwa Kotun Koli, karkashin dokokin shari'a, na nufin cewa, ba za a aiwatar da hukuncin kotun daukaka karar na ranar 14 ga Maris ba.
A ranar 14 ga Maris, Mai shari'a Okon Abang ya yi sabon hukunci kan jingine hukuncin da aka yi a baya da ya tabbatar da nadin Sanusi II a matsayin sarkin Kano na 16.
Gwamnatin Kano ta kalubalanci hukuncin Alkali

Asali: Facebook
Mai shari'ar ya kuma bukaci dukkanin bangarorin su mayar da wukaken fadansu kan rikicin sauratar, inda ya waiwayi hukuncin kotu na ranar 13 ga Yunin 2024, mai lamba: FHC/KN/CS/182/2024.
Sai dai, rashin gamsuwa da hukuncin Mai shari'a Abang ya sa lauyan gwamnatin Kano, Wangida, ya kalubalanci hukuncin kotu na ranar 13 ga Maris din, yana mai cewa an tafka kuskure fassara kundin tsarin mulki.
Jaridar The Guardian ta rahoto Wangida ya kuma jaddada cewa tuni gwamnatin Kano ta daukaka wannan kara zuwa Kotun Koli.

Kara karanta wannan
2027: Ta fara tsami tsakanin ƴan adawa, burin Atiku da maganar yanki na son ta da kura
Da yake martani kan mika shari'ar zuwa Kotun Koli, lauya bangaren Aminu Bayero, Abdul Fagge (SAN), bai yi jayayya ba, ya ce matakin Wangida na kan doka.
'Sarki 1 ne a Kano' - Gwamnatin Abba
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Kano ta jaddada cewa Muhammadu Sanusi II ne kadai Sarkin Kano, kuma har yanzu kotu ba ta rushe hakan ba.
Da yake magana bayan hukuncin kotun daukaka kara, kwamishinan watsa labaran Kano, Ibrahim Waiya, ya ce wasu na amfani da rikicin sarautar don tayar da fitina.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng