KADIRS: "Yadda El Rufa'i Ya Yi Rugu Rugu da Hukumar Haraji a Zamaninsa"
- Hukumar tattara kuɗin haraji ta Kaduna ta musanta kalaman tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufa’i a game da KADIRS
- Shugaban hukumar, Kwamared Jerry Adams, ya ce babu ƙamshin gaskiya a adadin kuɗin da El-Rufa’i ya ce ana tattarawa
- Ya bayyana bambancin tsarin tattara haraji a zamanin gwamnatin Nasir El-Rufa’i da na yanzu karkashin Uba Sani da ke mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Shugaban hukumar tattara haraji ta jihar Kaduna (KADIRS), Jerry Adams, ya bayyana cewa an bar hukumar a cikin mawuyacin hali a zamanin tsohon gwamna Nasir El-Rufa’i.
Da yake magana da ‘yan jarida a ranar Talata, Kwamred Adams ya karyata ikirarin El-Rufa’i cewa gwamnatinsa na tara har Naira biliyan 7 a kowane wata a lokacinsa.

Asali: Facebook
A sakon da KADIRS ta wallafa a shafinta na Facebook, hukumar ta jaddada cewa mafi yawan kudin da aka tattara sun fito ne daga biyan basussuka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban hukumar ya kara da cewa an kuma samu sauran kuɗin daga sayar da kadarori, wanda jimillarsu ta kai N45b, amma ba wai an same su a wata wata ba ne.
KADIRS ta soki gwamnatin El-Rufa'i a Kaduna
Kwamred Jerry Adams ya bayyana cewa duk da wannan tarin kudade da aka tattara, an bar KADIRS cikin rashin kulawa, inda sama da 80% na ofisoshinta ke cikin mawuyacin hali.
Ya ƙara da bayyana cewa haka kuma hukumar ba ta da isassun motocin aiki, kuma an bar ma’aikata ba a cikin yanayin ko-in-kula a zamanin mulkin Nasir El-Rufa'i.

Asali: Facebook
Ya ce wannan lamarin ya haifar da tambayoyi masu muhimmanci kan yadda aka gudanar da kudaden haraji a zamanin tsohuwar gwamnati, duk da ikirarin El Rufa'i na cewa sun yi aiki.
KADIRS: Gwamnatin Uba ta saɓa da ta El-Rufa'i
Shugaban hukumar tattara kuɗin shiga a Kaduna ya bayyana yadda gwamnati mai ci a ƙarƙashin Uba Sani ta saɓa da wacce Nasir El-Rufa'i ya jagoranta a bangaren haraji.
Kwamred Jerry Adams ya ce:
"A cikin shekaru biyu da suka gabata, karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani, an mayar da hankali kan gyara sashen tattara haraji, ta hanyar kaddamar da tsarin biyan haraji ta hanyar fasahar zamani don inganta ayyukan hukumar."
"Sakamakon haka, Jihar Kaduna ta tara N62.48bn a 2023 da kuma N71bn a 2024, wanda ya dara na shekarun El-Rufa’i. A watanni biyu na farkon 2025 kadai, an riga an tara N14.16bn."
KADIRS ta wanke Uba daga zargin El-Rufa’i
Kwamred Adams ya kuma yi watsi da zargin cewa gwamnatin Uba Sani ta rika satar N100m daga asusun kudaden shiga na jihar a asirce.
Ya bayyana cewa tsarin tattara haraji na Kaduna yana sarrafa kansa gaba ɗaya, inda dukkan biyan kuɗi ke tafiya kai tsaye zuwa asusu guda na gwamnati (TSA).
Shugaban hukumar ya kara da cewa wannan tsari ya yi tasiri wajen dakile duk wani yunkuri na almundahana ko satar kuɗin gwamnati.
Hukumar KADIRS ta yabi jihar Kaduna
Kwamred Jerry Adams ya ce a halin yanzu, jihar Kaduna ce ke kan gaba a yankin Arewacin Najeriya a fannin samun kuɗin shiga daga haraji.
Ya wannan ya jawo muhimman tambayoyi a kan yadda gwamnatin Nasir El-Rufa'i ta gaza ciyar da hukumar gaba,bayan ta yi ikirarin samun manyan kuɗi.
El-Rufa'i: "Ana wawashe kuɗin Kaduna"
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa'i, ya zargi gwamnatin Uba Sani, da cewa ta na sama da faɗi da kudaden jihar.
A cewarsa, gwamnatin Uba Sani tana ruf da ciki da kudaden ƙananan hukumomi, tare da karkatar da su zuwa sayen gidaje a ƙasashen waje domin azurta gwamna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng