Rikicin Rivers: Shugaban Riƙo da Tinubu Ya Naɗa na Fuskantar Barazanar Ma'aikata

Rikicin Rivers: Shugaban Riƙo da Tinubu Ya Naɗa na Fuskantar Barazanar Ma'aikata

  • Kungiyoyin kwadago sun yi barazanar tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani saboda dokar ta-baci da shugaban kasa ya ayyana a jihar Rivers
  • Sun bayyana cewa ayyana dokar ta jawo cikas ga biyan albashi, wanda ya jefa ma’aikata cikin mawuyacin hali da korar masu zuba hannun jari
  • Shugabannin kwadago sun bukaci Shugaba Bola Tinubu ya janye dokar ta-bacin, ko su dauki matakin da zai iya shafar tattalin arzikin kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Rivers - Kungiyoyin kwadago a jihar Ribas sun yi barazanar tsunduma yajin aiki na sai-baba-ta-gani da ka iya dakile harkokin tattalin arzikin kasa.

'Yan kwadagon sun ce lallai babu makawa za su shiga yajin aikin idan har Shugaba Bola Tinubu bai janye dokar ta-baci da ya ayyana a Rivers ba.

NLC, TUC sun magantu kan ayyana dokar ta baci da Tinubu ya yi a Rivers
Ma'aikata na barazanar tsunduma yajin aiki a jihar Rivers. Hoto: @NLCHeadquarters, @officialABAT
Asali: Twitter

'Yan kwadago su fadi illar dokar ta baci a Rivers

Kara karanta wannan

Dawowar Fubara: Ana rade radin yin sulhu a Rivers, Wike ya yi magana

A cikin wata sanarwa da shugabannin NLC da TUC suka sanya wa hannu, sun ce dokar ta-baci ta hana biyan albashin ma’aikata a jihar, inji rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyoyin kwadagon sun bayyana cewa ma’aikatan kananan hukumomi da ba su karbi albashinsu ba na fuskantar matsananciyar wahala ta tattalin arziki.

Sanarwar ta ce dokar ta-bacin ta sanya jihar cikin mawuyacin hali, inda masu zuba jari suka janye kudurinsu na saka hannun jari a Ribas.

Kungiyoyin sun ce ‘yan kasuwa da suka nuna sha’awa ga shirin ‘New Rivers Vision’ sun janye jikinsu saboda rashin kwanciyar hankali na siyasa a jihar.

Dokar ta baci ta hana a biya ma'aikatan Rivers

Kungiyoyin kwadago na Ribas sun ce suna goyon bayan doka da oda, amma dole ne duk matakan da za a dauka su yi daidai da kundin tsarin mulki.

Sun jaddada cewa dakatar da zababbun shugabanni da ayyana dokar ta-baci bai kamata ya hana biyan albashi ko kuma ya bar ma’aikata cikin mawuyacin hali ba.

Kara karanta wannan

An nemi kama sakataren APC kan yunkurin dakatar da gwamnan PDP a Osun

Vanguard ta rahoto cewa sanarwar ta bukaci gwamnati da ta fi mayar da hankali kan tsaro da walwalar ‘yan kasa maimakon fifita bukatun siyasa.

Shugabannin kwadago sun yi kira ga shugaban kasa, majalisar tarayya da bangaren shari’a da su janye dokar ta-bacin da aka ayyana a Rivers nan take.

'Yan kwadago na barazanar shiga yajin aiki

Kungiyoyin kwadago sun yi barazanar shiga yajin aiki a Rivers
Kungiyoyin kwadago sun fadi abin da zai faru idan suka shiga yajin aiki a Rivers. Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Twitter

Kungiyoyin sun bukaci gwamnatin tarayya da ta zauna da bangarorin da abin ya shafa domin dakile ci gaban rikice-rikice a jihar.

An bukaci ma’aikata da su kara hakuri, kuma su kwantar da hankalinsu, tare da ci gaba da aikinsu yayin da suke jiran matakin da gwamnati za ta ɗauka.

Kungiyoyin sun gargadi gwamnati da cewa idan ba a magance matsalolin cikin kankanin lokaci ba, za su shiga yajin aikin da zai iya shafar tattalin arziki.

Sanarwar hadin gwiwar da aka fitar a ranar 24 ga Maris, 2025, na dauke da sa hannun Alex Agwanwor (NLC Rivers), Ikechukwu Onyefuru (TUC Rivers), da Chuku Emecheta (JNC Rivers).

Kara karanta wannan

'Ayi hankali': Abin da shugaban rikon kwarya ya fada bayan shiga ofis a Rivers

Rikicin Rivers: Lauya ya yi karar Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani babban lauya, Johnmary Jideobi ya shigar da kara da ke kalubalantar nadin Vice Admiral Ibokette Ibas a matsayin shugaban riko na jihar Rivers.

Johnmary Jideobi, ya nemi babban kotun tarayya ta Abuja da ta ayyana nadin a matsayin haramun tare da hana shugaban ƙasa yin hakan a kowace jiha.

Lauyan, mai zaman kansa, ya jaddada cewa kundin tsarin mulki bai ba Shugaba Bola Tinubu damar dakatar da zababben gwamna ko naɗa shugaban riko ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng