Badakalar N33.2bn: EFCC Ta Sake Dauko Shari'ar Sambo Dasuki, an Samu Bayanai
- Ƙarar da EFCC ta shigar da tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki, za ta dawo sabuwa
- Hukumar EFCC za ta sake gurfanar da Kanal Sambo Dasuki mai ritaya a gaban babbar kotun birnin tarayya Abuja a ranar Talata
- Sambo Dasuki dai yana fuskantar tuhume-tuhume da suka shafi zargin karkatar da kuɗin da suka kai N33.2bn da yake ofis
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hukumar EFCC za ta sake gurfanar da tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) Sambo Dasuki a gaban kotu.
EFCC za ta gurfanar da Dasuki ne da tsohon babban manajan kamfanin NNPCL, Aminu Baba-Kusa, tare da kamfanoni biyu, Acacia Holdings Limited da Reliance Referral Hospital Limited.

Asali: Twitter
Jaridar Tribune ta rahoto cewa idan dai ba wani sauyi aka samu, hukumar EFCC za ta gurfanar da su ne a gaban babbar kotun babban birnin tarayya Abuja a yau Talata.

Kara karanta wannan
Shirin fatattakar Tinubu ya samu cikas bayan matsayar sakataren PDP kan haɗakar Atiku
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa za a sake gurfanar da Sambo Dasuki?
Sake gurfanar da su yau na zuwa ne bayan alƙalin alƙalin Abuja, mai shari’a Hussein Baba-Yusuf, wanda ke sauraron shari’ar kafin a naɗa shi muƙamin, ya mayar da shari’ar ga mai shari’a Charles Agbaza.
Wadanda ake tuhuma za su bayyana a gaban kotun domin sake fara shari’ar daga farko a ƙarƙashin jagorancin Charles Agbaza.
Sambo Dasuki tare da sauran waɗanda ake tuhuma da tsohon daraktan kuɗi na ofishin NSA, Shuaibu Salisu, sun fara gurfana a gaban mai shari’a Baba-Yusuf a ranar 14 ga Disamba, 2015, bisa tuhuma 19 da suka shafi karkatar da N13.5bn.
Daga baya, masu gabatar da ƙara sun yi wa tuhume-tuhumen garambawul, inda aka cire sunan Salisu daga cikinsu.
A ranar 11 ga watan Mayu, 2018, Dasuki da sauran waɗanda ake tuhuma sun sake gurfana bisa tuhuma kan badakalar N33.2bn da kuma karkatar da kuɗaɗen da aka tanada don sayen makamai domin yaƙi da Boko Haram.
Tun a lokacin, masu gabatar da ƙara sun kira shaida guda ɗaya kacal, wanda shi ne jami’in bincike da ya gudanar da binciken badaƙalar kuɗin sayen makamai, amma bai kammala bayani a kotu ba lokacin da aka ɗage shari'ar.
EFCC na da tuhume-tuhume kan Dasuki
A shekarar 2015, EFCC ta shigar da wasu ƙararraki biyu daban-daban kan Kanal Sambo Dasuki a gaban mai shari’a Baba-Yusuf a Maitama, Abuja.
A wata shari’ar daban mai lamba FCT/HC/CR/42/2015, Dasuki na matsayin mutum na biyu cikin waɗanda ake tuhuma tare da tsohon ƙaramin ministan kuɗi, Bashir Yuguda.
Sannan akwai tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, ɗansa Sagir da kamfaninsa, Dalhatu Investment Limited.

Asali: Twitter
Ana tuhumar su da laifuka 25 da suka shafi cin amana da karkatar da kuɗaɗen jama’a har N19.4bn.
Wannan shari’ar tuni an mayar da ita gaban mai Shari’a Yusuf Halilu a Maitama bayan mai Shari’a Baba-Yusuf ya zama alƙalin alƙalin Abuja, kuma shari’ar na cigaba da tafiya.
Dukkan shari’o’in sun sha jinkiri sakamakon ƙin ba da belin Sambo Dasuki da hukumar DSS ta yi, duk da cewa kotuna da dama, ciki har da mai shari’a Baba-Yusuf, sun bayar da belinsa.
Rahotanni sun nuna cewa sake gurfanar da su yau na zuwa ne bayan matsin lamba da aka yi kan alƙalin alƙalan don ya mayar da shari’ar ga wani alƙali, kasancewar ayyuka sun yi masa yawa.
EFCC ta ƙwato N365bn a hannun ɓarayi
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar EFCC mai yaki da cin hanci a Najeriya ta bayyana nasarorin da ta samu kan ɓarayi a shekarar 2024.
Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa sun samu nasarar ƙwato N365.4bn a shekarar 2024 da ta wuce.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng