Rikicin Rivers: Jerin Gwamnonin da Suka Goyi Bayan Tinubu a Dakatar da Fubara

Rikicin Rivers: Jerin Gwamnonin da Suka Goyi Bayan Tinubu a Dakatar da Fubara

Jihar Rivers - Rikicin siyasa da ke addabar jihar Rivers ya tsananta, inda har ƴan majalisar dokokin jihar suka yi barazanar tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Bayan rikicin ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar mai arziƙin mai.

Wasu gwamnoni sun goyi bayan dakatar da Fubara
Gwamna Hope Uzodimma na cikin masu goyon dakatar da Fubara Hoto: @OfficialABAT, @Hope_Uzodimma1, @SimFubaraKSC
Asali: Twitter

Shugaban ƙasa ya dakatar da gwamnatin jiha

Shugaban ƙasan ya sanar da sanya dokar ta ɓacin ne a wani jawabi da ya yi wa ƴan Najeriya, wanda hadiminsa Dada Olusegun ya sanya a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai girma Bola Tinubu ya kuma dakatar da Gwamna Fubara, mataimakiyarsa da ƴan majalisar dokokin jihar har na tsawon watanni shida.

Shugaban ƙasan ya kuma naɗa Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas (mai ritaya) a matsayin shugaban riƙo wanda zai ci gaba da jan ragamar harkokin mulki a jihar har na tsawon watanni shida.

Kara karanta wannan

Sanatan Bauchi ya ba mutane kunya da azumi, bidiyosa yana rabon kuɗi ya shiga intanet

Wannan mataki na Tinubu ya jawo cece-kuce a tsakanin ƴan Najeriya daga fannoni daban-daban, inda aka samu masu nuna goyon baya da masu akasin haka.

Rikicin Rivers ya ƙi ci ya ƙi cinyewa

Rikicin siyasar Rivers ya fara ne kimanin wata shida bayan Simi Fubara ya kama aiki a matsayin gwamna, inda ake zarginsa da yunƙurin tsige kakakin majalisar dokokin jihar, cewar rahoton Businessday.

Wannan yunƙurin da Gwamna Fubara ya yi bai yi wa tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Ezenwo Wike, daɗi ba.

Wike, wanda a halin yanzu ke matsayin ministan babban birnin tarayya Abuja, ya zargi Fubara da ƙoƙarin ƙwace tsarin siyasar jihar daga hannunsa.

Fubara a na sa ɓangaren ya yi zargin cewa tsohon gwamnan ya ƙi sakar masa mara wajen gudanar da harkokin mulkin jihar.

Duk da ƙoƙarin shiga tsakani da aka yi, rikicin ya ƙi warwaruwa cikin lalama, lamarin da har sai da ya kai zuwa ga kotuna.

Kara karanta wannan

"Tinubu ya saba da tsarin jari hujja," NNPP ta haramta dokar ta ɓacin Ribas

Gwamnonin da suka goyi bayan matakin Tinubu

Duk da sukar da wasu ke yi, akalla wasu gwamnoni guda uku sun goyi bayan matakin da shugaban ƙasan ya ɗauka kan rikicin siyasar jihar Rivers.

Dukkanin gwamnonin dai na jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ne kuma sun fito ne daga yankin Kudancin ƙasar nan.

Ga jerinsu a nan ƙasa:

1. Hope Uzodimma na Imo

Uzodimma ya goyi bayan dakatar da Fubara
Hope Uzodimma ya goyi bayan Tinubu kan dakatar da Fubara Hoto: Hope Uzodimma
Asali: Facebook

Gwamnan jihar Imo, wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar APC, Hope Uzodimma, ya bayyana goyon bayansa kan sanya dokar ta ɓaci da Shugaba Tinubu ya yi a jihar Rivers.

A wani taron manema labarai, Uzodimma ya ce matakin da Tinubu ya ɗauka ya yi daidai domin kawo ƙarshen rikicin siyasar da ke ƙara ta'azzara a jihar mai arziƙin mai.

Ya ƙara da cewa, rikicin siyasar Rivers na iya dagula jihar da ma tattalin arziƙin Najeriya baki ɗaya.

Kalli bidiyon jawabinsa a nan:

Kara karanta wannan

Dokar ta baci: Ministan Tinubu ya caccaki Kwankwaso, ya fadi gazawarsa

2. Monday Okpebholo na Edo

Monday Okpebholo
Monday Okpebholo ya goyi bayan dakatar da Gwamna Fubara Hoto: Senator Monday Okpebholo
Asali: Twitter

Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya yabawa Shugaba Tinubu bisa ayyana dokar ta-ɓaci a Rivers, inda ya bayyana cewa matakin ya ceto tattalin arziƙin ƙasar nan.

A cewar jaridar The Nation, Okpebholo, yayin da yake wakiltar Tinubu a bikin ƙaddamar da aikin titin tarayya a Edo, ya soki tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, wanda ya ce matakin zai zubar da mutuncin Najeriya a idon duniya.

Okpebholo ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasan bai iya ɗaukar matakan da suka dace ba lokacin da yake mulki, shiyasa yake sukar Shugaba Tinubu.

Ya ce matakin da shugaban ƙasan ya ɗauka ya yi daidai domin dawo da zaman lafiya a yankin Neja Delta.

3. Gwamnan rikon kwarya a Cross River

Gwamnatin Jihar Cross River ta nesanta kanta daga matsayar Kungiyar gwamnonin Kudu maso Kudu, wadda ta nuna rashin amincewa da ayyana dokar ta ɓaci a Rivers.

Kara karanta wannan

Jonathan ya tsoma baki kan dakatar da Fubara, ya fadi illar hakan ga Najeriya

A cewar jaridar Leadership, muƙaddashin gwamnan jihar Cross River, Peter Odey, ya bayyana cewa jiharsa na goyon bayan matakin Tinubu, domin dawo da doka da oda da kuma dakile rikicin da ke ƙara dagulewa a jihar Rivers.

SERAP ta kai Tinuubu ƙara kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar SERAP ta ɗauki matakin shari'a kan ayyana dokar ta ɓaci da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a jihar Rivers.

SERAP ta ƙalubalanci matakin dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da sauran zaɓaɓɓun jami'an gwamnati da Shugaba Tinubu ya yi.

A ƙarar da ƙungiyar ta shigar a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta buƙaci kotun da ta ba da umarnin soke dakatarwar da aka yi wa Gwamna Fubara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng