Sarautar Kano: Bayan Rangadin Aminu Ado, Sanusi II Ya Shiga Gari Ziyarce Ziyarce

Sarautar Kano: Bayan Rangadin Aminu Ado, Sanusi II Ya Shiga Gari Ziyarce Ziyarce

  • Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammad Sanusi II, ya kai ziyarar jaje ga ‘yan kasuwa da gobara ta shafa a kasuwar Dakata
  • Haka zalika mai martaba Sanusi II ya halarci karatun Hadisi na Sheikh Abdullahi Uwais Limanci a masallacin Limanci, Koki
  • Ya kuma ziyarci gidan gajiyayyu na Shahuci da asibitin yara na Hasiya Bayero, inda ya ba da kayan azumi da kayan Sallah

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammad Sanusi II, ya gudanar da jerin ziyarce-ziyarce a cikin watan Ramadan domin jajanta wa al’umma da halartar wuraren ibada.

Daga cikin wuraren da ya ziyarta akwai kasuwar Dakata, inda gobara ta tashi, da masallacin Limanci a Koki, da zawiyyar Shehu Tijjani Usman a ‘Yan Mota da kabarin mahaifinsa.

Kara karanta wannan

Kaduna: Sarki ya samu shirgegen muƙamin gwamnati, Gwamna Uba Sani ya taya shi murna

Sanusi Ii
Khalifa Sanusi II ya je jaje kasuwar Dakata bayan gobara. Hoto: Sanusi II Dynasty
Asali: Facebook

A cikin sakon da aka wallafa a shafinsa na X, Sanusi II ya ziyarci gidan gajiyayyu na Shahuci da asibitin yara na Hasiya Bayero, inda ya raba kayan azumi da kayan Sallah ga marasa galihu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarki Sanusi II ya je jaje kasuwar Dakata a Kano

A ranar Litinin, 24 ga Maris, 2025 (24 ga Ramadan, 1446 AH), Mai Martaba Sarkin Kano na 16 ya kai ziyarar jaje ga ‘yan kasuwa da gobara ta shafa a kasuwar Dakata.

Sarki Sanusi II ya jajanta wa al’ummar kasuwar bisa hasarar da suka yi, tare da yin addu’a Allah Ya maye musu da alheri.

‘Yan kasuwar sun nuna matuƙar farin ciki da wannan ziyarar, suna mai gode wa mai martaban bisa kulawarsa.

Sanusi II ya halarci karatun hadisi a Koki

A wata ziyara daban, Mai Martaba ya halarci karatun Hadith na Sheikh Abdullahi Uwais Limanci a masallacin Limanci da ke unguwar Koki.

Kara karanta wannan

2027: 'Yar takarar gwamnan APC, Aishatu Binani ta gana da shugaban SDP

Karatun, wanda ke gudana a cikin watan Ramadan, yana ɗaya daga cikin manyan tarurrukan addini da ake gudanarwa a Kano.

Jama’a sun yi farin ciki da halartar mai martaba Muhammadu Sanusi II, inda suka yi addu’o’i na alheri a gare shi.

Limanci
Sheikh Uwais Limanci na mika littafi wa mai martaba Sanusi II. Hoto: Sanusi II Dynasty
Asali: Facebook

Ziyarar zawiyya da kabarin mahaifinsa

A ranar Asabar, 22 ga Ramadan, 1446 AH, Sarkin Kano ya halarci karatun addini a zawiyyar Shehu Tijjani Usman da ke ‘Yan Mota.

Bayan nan, ya kai ziyara kabarin mahaifinsa, Chiroman Kano Aminu Sanusi, ya yi addu’a tare da roƙon Allah Ya gafarta masa da sauran magabata.

Tallafa wa marasa galihu a Shahuci da asibiti

A ranar Jumu’a, 21 ga Ramadan, 1446 AH, Mai Martaba ya kai ziyara gidan gajiyayyu na Shahuci da ke bayan kasuwar Rimi, tare da Asibitin Yara na Hasiya Bayero.

A yayin ziyarar, ya raba kayan azumi da kayan Sallah ga marasa galihu, domin sauƙaƙa musu rayuwa a cikin watan Ramadan.

Kara karanta wannan

'Muna bayan Wazirin Adamawa': Matasa sun dauko tafiyar kifar da Tinubu a 2027

Jama’a sun yaba da wannan ƙoƙari na Mai Martaba, suna mai bayyana godiyarsu da addu’ar Allah Ya ƙara masa lafiya da nasara a shugabancinsa.

Pantami ya yi magana kan sarautar Kano

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon minista, Sheikh Isa Ali Pantami ya yi magana kan rikicin sarautar Kano da ya ki karewa.

Malamin ya ce abin takaici ne yadda aka zuba ido a Arewa har aka samu iyayen kasa biya a jihar Kano mai dogon tarihi a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel