Gwamna Ya Ɗauki Zafi da Aka Nemi Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta Ɓaci a Jihar Benuwai

Gwamna Ya Ɗauki Zafi da Aka Nemi Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta Ɓaci a Jihar Benuwai

  • Gwamna Hyacinth Alia ya yi fatali da masu kiran gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta ɓaci a jihar Benuwai ganin irin halin da ake ciki a yau
  • Alia ya ce babu wani dalili da ya kai a ayyana dokar ta ɓaci, ya na mai cewa wasu ƴan siyasa ne ke kokarin fakewa da hakan don cimma burinsu
  • Wannan dai na zuwa ke bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ya ɓaci a jihar Ribas, lamarim da ya tada ƙura a kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Benue - Gwamnatin jihar Benue karkashin jagorancin Gwamna Hyacinth Alia ta bayyana cewa babu wani dalili da zai sa a yi tunanin ayyana dokar ta-baci a jihar.

Gwamna Alia ya bayyana cewa shi ke da cikakken iko na jan ragamar harkokin jihar Benuwai, don haka ba buƙatar dokar ta ɓaci.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya yi buda biki da marayu, ya ɗauki alkawarin ba su aikin yi

Gwamna Abia.
Gwamna Alia ya ce babu buƙatar ayyana dokar ta ɓaci a jihar Benuwai Hoto: Fr. Hyacinth Lormem Alia
Asali: Facebook

Sakataren yaɗa labaran gwamnan, Mr. Tersoo Kula, ne ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar a ranar Litinin a Makurdi, kamar yadda Vanguard ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka nemi sa dokar ta-ɓaci a Benuwai

Sanarwar ta biyo bayan wani taron manema labarai da cibiyar CJI, mai fafutukar tabbatar da adalci, ta yi, inda ta yi ƙorafi kan halin da jihar Benuwai ke ciki.

Mr. Kula ya caccaki masu kira da a ayyana dokar ta-baci a jihar, ya ke cewa ba su da masaniya game da abin da ke wakana a Benuwai.

Ya gargadi waɗanda ke ƙoƙarin tayar da husuma da fitina a jihar da su tattara su bar Benuwai, domin mutanen jihar ba za su amince da ƙirƙirarrun zarge-zarge da ha'inci na siyasa ba.

Gwamna Alia ke da cikakken iko

"Kiran a sa dokar ta-baci a Benue ba shi da tushe, wani yunkuri ne na wasu gurɓatattun ‘yan siyasar da ke neman tayar zaune tsaye don cimma burinsu.

Kara karanta wannan

Tankar mai ta sake fashewa a Neja, hukumomi sun tashi tsaye

"Duk wanda ke da shakku yana iya zuwa jihar domin ya gani da idonsa, babu wani rashin kwanciyar hankali. Gwamna Alia ke da cikakken iko a jihar."

- Mr. Tersoo Kula.

Mr. Kula ya ƙaryata zargin da ake yi cewa Gwamna Alia ya saye alkalai da sauran masu ruwa da tsaki a ɓangaren shari’a domin cimma wata manufa ta siyasa.

Ya buƙaci cibiyar CJI da ta gabatar da hujjoji a bainar jama’a ko kuma su fuskanci sakamakon wannan karya da suka ƙirƙiro mara tushe balle makama.

Gwamna Alia.
Gwamna Alia ya tabbatar da cewa babu bukatar sa dokar ta ɓaci a Benue Hoto: Hyacinth Lormem Alia
Asali: Twitter

Gwamnatin Benuwai tana da tsare-tsare

Sakataren watsa labaran gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatin Alia na tafiya a kan tsari na gyara, inda take fifita jin daɗin jama’a da walwalarsu.

Kula ya jaddada cewa mutanen Benue suna goyon bayan gwamnansu, tare da yi masa addu’ar domin Allah ya ci gaba da ba shi nasara.

A ƙarshe, ya yi kira ga waɗanda ke ƙoƙarin ɓata siyasar jihar da su daina tunzura jama’a tare da ba da girmamawa ga tsarin dimokuradiyya, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Fubara: Gwamnonin PDP sun nufi kotun koli kan dokar ta baci a jihar Ribas

Alia ya kaddamar sabon taken Benuwai

Ku na da labarin Gwamna Hyacinth Alia ya kaddamar da sabon taken jihar Benuwai da ke Arewa ta Tsakiya don bunkasa al’adu, asali, da gadon tarihi.

Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da cigaban jihar ta hanyar yakar koma-baya da gina ingantattun cibiyoyin lafiya da ilimi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng