"Ba Ni da Hannu," Sheikh Sulaimon Ya Fashe da Kuka a Tafsirin Ramadan, Ya Rantse da Alƙur'ani

"Ba Ni da Hannu," Sheikh Sulaimon Ya Fashe da Kuka a Tafsirin Ramadan, Ya Rantse da Alƙur'ani

  • Sheikh Sulaimon Farooq ya rantse da Alkur'ani cewa ba shi da wani hannu a rashin lafiyar Sheikh Habeeb Adam
  • Malamin ya yi wannan rantsuwa ne a wurin tafsirin Ramadan yayin da rikici a tsakanin malaman biyu ya ƙara ƙamari
  • Manyan malaman sun fara zaman doya da manja ne bayan Sarkin Ilorin ya naɗa Sheikh Sulaimon a matsayin Muftin kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ilorin, Kwara - Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Sulaimon Farooq Onikijipa, ya rantse da Al-Qur’ani Mai Girma a bainar jama’a a wurin tafsir na Ramadan.

Malamin ya yu rantsuwar ne domin karyata zargin cewa ya yi sihiri don sa wa Sheikh Habeeb Adam (El-Ilory), jagoran Markaz Centre for Arabic and Islamic Studies da ke Agege, Lagos, wata cuta mai ban mamaki.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace babban malamin addini a Imo, 'yan sanda sun dauki mataki

Sheikh Sulaimon Farooq Onikijipa.
Sheikh Sulaimon Farooq Onikijipa ya rantse da Alkur'ani a bainar Jama'a Hoto: Sheikh Sulaimon Farooq Onikijipa
Asali: Facebook

A tafsirin watan Ramadan, Sheikh Sulaimon, wanda shi ne Muftin Ilorin, ya karyata zargin cikin kuka da zubar da hawaye da karayar zuciya, Leadership ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban malami ya rantse da Alƙur'ani

Malamin ya ce:

“Wannan Al-Qur’ani ne a hannu na kuma muna cikin ɗakin Allah. Tun farkon rayuwata ban taba rantsuwa da littafi mai tsarki ba, amma yau zan rantse.”
"Ya Allah, Ina cikin gidanka. Idan ni, Sulaimon Farooq, ɗan Aminat, na san wani abu game da rashin lafiyar Mudir Markaz, to dukan la’anar da ke cikin wannan littafi mai tsarki ta kasance a kaina.
"Idan kuwa ana ƙulla min sharri ne to la’anar ta tabbata a kansu.”

Sheikh Sulaimon Onikijipa ya maimaita rantsuwar sau huɗu don tabbatar da gaskiyarsa.

Sheikh Habeeb ya zargi wani kan cutarsa

A gefe guda, Sheikh Habeeb Adam El-Ilory, ya bayyana a wani Tafsiri na watan Ramadan cewa rashin lafiyar da ya kamu da ita tun 2022 ba ta Allah da Annabi ba ce.

Kara karanta wannan

Kaduna: Sarki ya samu shirgegen muƙamin gwamnati, Gwamna Uba Sani ya taya shi murna

Duk da cewa bai ambaci suna ba, ya bayyana cewa akwai wani babban malami da yake zargi da hannu a cikin lamarin.

Ya yi alkawarin bayyana cikakken labarin rigimar da ke tsakaninsu da kuma musabbabin rashin lafiyarsa a nan gaba.

Ya ce:

"Ni dawa nake faɗa? Taya zai ce mahaifina ya yi masa laifi? Abin da mahaifina ya yi kawai shi ne ya ambaci sunayen manyan malumma amma bai sa mahaifinsa ba.
Sheikh Sulaimon.
Sheikh Sulaimon ya musanta duk wani zargi da ake masa Hoto: Sheikh Sulaimon Farooq Onikijipa
Asali: Facebook

Yadda rikici ya kaure tsakanin malaman

Sheikh Habeeb Adam ya bayyana cewa akwai wasu abubuwa guda biyu da suka faru kafin fara rashin lafiyarsa.

"Na farko, wani daga cikin mabiya Onikijipa ya shafa masa kyalle a wuyansa, sannan ya mikawa Muftin Ilorin. Bayan wannan taro, cikin kankanin lokaci, sai ya fara rashin lafiya.
"Na biyu, na je wurin ɗaura aure, to ya riga ni zuwa, ina ƙarisowa sai ya taso kamar zai tarbe ni, kawai ya saka mani wani abu a aljihu, daga nan na kasa magana."

Kara karanta wannan

Sanata Kalu ya watsa wa matasan Arewa ƙasa a ido, ya yi maganar karawa da Tinubu a 2027

Tun lokacin da Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Kolapo Sulu-Gambari, ya naɗa Sheikh Onikijipa a matsayin Muftin Ilorin, dangantaka tsakanin su ta fara tsami.

Halin da ake ciki

A yayin da rikicin ke ci gaba da daukar sabon salo, masu lura da al’amuran addini a Ilorin da Lagos sun bayyana damuwa kan yadda rashin jituwa tsakanin wadannan manyan malaman ke kara kamari.

Wasu mabiya sun fara nuna goyon baya ga daya daga cikin bangarorin biyu, abin da ya janyo rarrabuwar kai a tsakanin mabiyan addinin.

Masu sharhi sun ce wannan sabani ya fi karfi fiye da yadda ake tunani, kasancewar yana da nasaba da dadaddiyar rikicin shugabanci a tsakanin malaman ilimi a yankin.

Wasu sun danganta lamarin da nadin da Sarkin Ilorin ya yi wa Sheikh Sulaimon a matsayin Muftin kasar, matakin da wasu ke ganin ya haddasa jin haushin bangaren Sheikh Habeeb Adam.

A gefe guda, wasu malaman addini sun bukaci manyan malaman biyu da su kwantar da hankalinsu tare da neman hanyar sasanci don kare martabar addinin Musulunci da hadin kan al’ummar yankin.

Kara karanta wannan

Ramadan: Dan Majalisa Kirista ya yi wa Musulmi bazata bayan bukatar babban limami

Sun yi kira da a daina furta kalaman da ka iya kara ruruta wutar rikici, musamman a wata mai alfarma kamar Ramadan.

Sarkin Musulmi ya shawarci al'umma

A wani labarin, kun ji cewa Mai alfarma sarkin Musulmi ya bukaci jama'a su ci gaɓa da kauracewa ayyukan sabon Allah har bayan watan Ramadan.

Sultan ya kuma roƙi su dage da addu'ar neman Allah ya kawo sauƙin rayuwa da waraka a goman ƙarshe mai cike da rahama a wajen musulmai.

Salisu Ibrahim ya fadada wannan labarin ta hanyar yin bayanin malamai a yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng